Sashe 85
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Miƙewa ta yi ba don ta gamsu da yanayin fuskar Kawun ba ta yi mishi sai da safe ta bar wurin. Hajjo dake gefe tana damawa Kawun fura tana jinsu ta mike bayan ta gama damawa Kawun fura ta ajiye masa da ludayi, cikin harshen fillanci ta ce.
"Komai da ya faru ya riga ya faru sai dai a kiyaye gaba. Yanzu tunda har ka gano bakin zaren sai a yiwa abin tufka ta hanyar cigaba da kula da yarinyar da dora ta bisa turbar addu'a da kuma nema mata abubuwa tsarin jiki duk da cewa babu tsarin da ya fi addu'ar."
Kawu ya numfasa cike da jimami da taraddadi.
"Mamaki da tsoron halayyar DAN ADAM ya ƙara shiga ta Hafsatu, yanzu ke kya ce wannan baiwar Allahr za ta iya cutar da ko mage ne balle kuma mutum?"
Murmushi Hajjo ta É—an yi.
"Meye abin mamaki anan? An fa yi wanda ya fi haka. Kuma kar k manta zargi ne.."
"Ko kusa bana kokwanto ko zargi a kan haka, wannan gaskiya ce da na jima da ji kuma na ƙi yarda sai yanzu da komai ya bayyana a zahirance. Ba zai yiwu ace hayaƙin da Maryama ta ba Fatima shekarun baya ba irinsa take hayaƙawa Humaira kuma yanayin da Fatima ke shiga dalilin hayaƙe-hayaƙen ace iri guda ne da na ɗiyarta. Wannan ai ko akwai ban mamaki, ban da kuma toshewar basira irin tamu a lokacin, mun kasa tunanin akwai cutarwa a ciki ba? Kowannenmu ya shaida da irin kaunar da Fatima da Isuhu ke yiwa junansu ba amma rana ɗaya ta yi masa tsana wadda da bakinta ta furta mana ba ta san dalilinsa ba? Kai Hafsatu, nikam ba zargi nake yi ba, na riga da na tabbatar da sa hannu wannan makirar."
Hajjo ta jinjina kai yayinda kwalla suka cicciko mata na tuna yanda Adda Fatima (kasancewar yaya take a wurinta koda babu aure tsakaninta Kawu, don yar uwarsu ce ta fannin Baffansu) ta sha fama kafin rasuwarta.
"Amma idan har hakan ne toh wallahi matarnan ta jira sakayyar Ubangiji don ta dauki alhakin wacce ba ta ji ba kuma ba ta gani ba. Matar da ta yarda da ita tsakani da Allah mu ma haka. Ni babu abin da ya ban tsoro sai wannan bori da tada jijiyoyin wuyan da Humaira ta ce tana yi akan ba ta kaunar aurenta da Fadeel. Toh a zatonta yarinyar za ta yi ta zama babu aure? Ai ni tun da naji cewar wai Humaira ba a sanyata a makarantar boko ba sai da na yi maka magana idan ba ka manta ba, nace maka ko Æ´ar gidan Iyagana da ta girmi Humaira da suka koma can Katsina da zama an maida ta boko kuma yanzu gashinan har ta kusa kammala kwalejinsu. Ka hau ni da faÉ—an ai wannan ma gata ne za ta yi mata. Eh gatan ne, amma yanzu wa aka cutar? Za ta shiga rayuwar miji É—an boko fisabilillahi daga shi har danginsa na san sun ci sun tada kai da biro da takarda yarinya babu faransancin babu turanci."
"Hafsatu don Allah abar maganar tunda dai mai afkuwa ya riga da ya afku. Ki yafemin faÉ—an da nayi maki a lokacin, amma ki sani ko Humaira ba ta yi wata aba boko ba, mu godewa Allah tunda ta tsira a hanyar tsirar, wato na islama da ba a hanata ba. Sannan karki manta duk fa yanda Allah ya tsarawa bawa a rayuwa hakan ne zai tabbata. Yanzun ba gashinan ba nan da ta yi mana girki kamar kunnuwanmu za su tsinke don dadi? Ai DUKAN RUWA BA ZAI HANA GWARJE AMO BA! Mu je zuwa muna nan dake wataran yarinyar nan sai ta zama tamkar farin wata mai haska darare a cikin yan uwanta. Babu abin da zai hana zakaran da Allah ya so ya yi cara."
Ta ji karfin gwuiwa bisa maganganunsa har sai da ta murmusa.
"Allahu ya nunamana wannan ranar."
Kawu ya amsa da amin yana jawo ƙwaryar furarsa.
***
©Rufaida Umar.Mami sosai ta cika da mamakin ganin Abba bai ce uffan ba hame da dawowar Tasleem gidansa matsayin bazawara. Koda ta kalallameshi banda Allah ya kyauta babu abin da ya ce. Tunanin shirye-shiryen bikin da ya sa a gaba shi ya dauke hankalinsa ne ya sanya ba ta kawo komai ba amma a kaifin basira irin nata ta sani akwai dai abinda ya sauya Abban, ko fara'arsa ta daina gani.
Æangaren jannat kuwa ranar da ta kama na dawowar Humaira, a ranar ne aka gurfanar da ita gaban alÆ™ali, a Æ´an kwanakin da ta yi gaba daya ta fita hayyacinta duk kuwa da cewar babu duka balle zagi amma fa wahalar zama a inda ba ta sama ba ya sauya ta. Tasleem koda ta ganta fashewa tayi da kuka, sai kuma a lokacin ne suka san Fadeel ne ya Æ™arfafa binciken har mai afkuwa ta afku. Wannan ya Æ™arawa Mamin tsanar Fadeel, itama Tasleem sai da ya yi mugun É“ata ranta.
Mami tana ganin an shige ciki domin shari'ar ta koma da baya ta fidda waya ta kira Wizzy. Tuni ta shiryamasa cewar ya aika mace gidan ta daukar masa Ahmad tunda babu kowa sai Anna da Ummita.
"Ka gaggauta wanzar da shirin don bana son a samu wata matsala, ka kuma tabbatar da komai ya tafi daidai."
Daga haka ta katse kiran ta shiga dakin shari'ar.
A gabansu alƙali ya yankewa Jannat hukuncin biyan tara na ɓata sunan da ta yiwa su Ummita, miliyan biyar ga kowaccensu. Sai kuma ƙaryata kanta a gidan jaridu da ma rediyo da kuma soshal midiya kan cewar ita ce ta sa aka yi wannan mummunan aikin da kuma ba da hakuri. Hakanan shi ma Joshua. Tun daga lokacin ya hau kuja da roƙon gafara don ya sani ba shi da maƙudan kuɗaɗen da zai biya don wake kansa a gaban alƙali. Ya shiga tsinuwa ga Jannat wacce ita ce ummul-aba'isin na shigarsa wannan hali. Shi da ya yi aikin akan kuɗaɗe ƙalilan sai ga shi ya jawowa kansa, ga mahaifinsa da ya ce babu shi babu hannunsa a ciki.
Daga haka aka ƙara titsa ƙeyarta aka tafi da ita har sai lokacin da aka biya tara sannan.
Haka suka fito bakin kotun su Tasleem da Mami na kuka, ga Anna can a gida ta baza idanu tana jiran ta gansu tare da ita.
Mami kuwa zuciyarta cike take da zullumin ko Wizzy ya aiwatar ko kuwa an samu akasi. Ta duba ta ga dukkan yaranta idan ka cire Mubarak da ke can Sokoto a camp babu wani da ba ya tare da su. A iyakar saninta babu wata matsala da za a samu da shigar mace cikin gidan tunda dai babu kowa.
***
A daidai wannan lokacin motar su Humaira ta tsaya a tasha, suka fito ita da Hajjo a take aka samar musu abin hawa da zai kai su har gida sakamakon lodin kayan da suka taho da su. Suna hanya zuciyarta cike taf da farin ciki, ba ta kira kowa ba da zummar sai dai kawai su ganta.
***
Wizzy ya bude motar gami da duban matarnan, matashiyar budurwarsa da yake ji da ita a lokacin, sai da suka kai ruwa rana kafin ta aminta da buƙatarsa har sai da ya yi nata alƙawarin da ta jima tana son ji, wai aure. Ta sha zabgegen hijabi da niƙaf.
"Nusy, kar ki bari a samu wata matsala. Ki bi komai daki-daki yanda muka tsara."
Ta yi mishi farr da idanu bayan ta É—age nikaf din.
"Wannan ba damuwa ba ne Guy, komai zan yi dominka."
Ya jawo fuskarta ya sumbaci goshin sannan ta sauke nikaf din ta dauki jakarta ta fita. Yana daga can tsallaken ya ga shigarta gidan ba tare da dogon zance da maigadin ba. Sai ya sauke ajiyar zuciyar, ribas ya yi da motar ya koma daga can bayan gidan ya tsaya gudun kada a gan shi duk kuwa da cewa motar tinted ce amma ita ce dai motar da ya kai wa su Abba hari.
***
Ummita dake zaune a falo ga Ahmad a gefenta yana bacci cikin net dinsa. Hankalinta gaba daya ya yi zurfi a tunanin yanda aka kaya a wurin shari'ar amma ta kasa kiran koda Raihana ce don ta ji meke faruwa. Sallamar budurwar ta katse tunaninta, ta dubi ƙofa gami da amsawa. Ganin mace da nikaf ba ka ganin komai sai idanunta ta dan yi jim, ba don ba ta saba ganin mai irin shigar ba sai don kasancewar abu ne mai wahala su yi baƙuwa da irin shigarnan. Kamar Nusy ta san zargin da take yi, sai ta ɗage nikaf din, kyakkyawar fuskarta ta bayyana da murmushi mai bayyana haƙorinta na makkah.
"Sannu, nan ne gidan su Futuha Yusuf?"
Ganinta har da haƙorin makkah da kuma yanayi na kamala sai ta ɗan saki jiki, itama cikin ɗan murmushin ta amsa.
"Yauwa, eh nan ne. Ƙaraso ciki mana."
Nusy cikin tabbacin samun nasara ta ƙarasa ta zauna idanunta ya sauka kan wanda ta zo dominsa, wato Ahmad. Yaron tubarakAllah, da alama goyo mai kyau yake samu don yana da kumari sosai fatarsa kuma ta ƙara gogewa.
"Ba ki sanni ba ko? Ni makwafciyarta ce ta Kuntau ana cemin Maman Suhail, mun yi da ita dama zan yi mata rakiya wata unguwa shi ne ta yimin kwatancen gidan nan ta ce na zo mu hadu anan mu tafi."
Ba wani sanin gidan na su Futuha na yanzu ta yi ba balle ta fahimci gaskiyar lamarin, ta ba da gaskiya sosai akan zancen Nusy.
"Allah Sarki, eh sun dan fita ne amma na tabbatar sun kusa dawowa yanzu. Bari na kawomaki ruwa."