← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 8 OF 101

Sashe 8

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Da ace kun san mene so da duk baku ɓata bakunanku ba. Sannan Ibb Gusau lafiyayyan mutum ne kar ki kara aibata shi. Tunda kuma ba ku da shawarar da za ku ban, ni nasan me zan yi."

Tana kai wa nan ta miƙe ta yaye mayafin ta faɗa banɗaki ba tare da ta amsawa Raihana da ke jefomata tambaya akan abin da za ta aikata ba.

***
  Mami ce tsaye a farfajiyar gidan ta haɗa cikin atamfa ruwan ƙasa mai adon fari, ta sha mayafi ruwan ƙasa hakanan takalminta. Ta dai yi kyau ƙarshe, idan ka kalle ta ba za ka ce ita ta haifi yaran ba saboda daidai gwargwado ta iya ɗaukar wanka. A gefenta Yassar ne su na magana yana ƙorafin shi dai mota yake so tasan yadda zata yi Abba ya siya mishi. Mami jinsa kawai ta ke yi tana yi kuma tana duban gate, da ta gaji ta ja guntun tsaki.

"Wai ina Yakubu ya je ne? Daga jeka ka sha mai shikenan har yanzu bai dawo ba?"

Yassar ya taɓe baki yana zura hannu a aljihun wandonsa.

"Mami ina magana ba ki amsamin ba, koda dai nasan wannan halin na Abba zai wahala ma ya siyamin. Amma fisabilillah ina ɗan jami'a ina kallon abokaina har ma da matan da na raina su a makaranta su na da motocin kansu ni kuwa ko keke Abba ya kasa siyamin saboda mammaƙo."

Ran Mami a ɓace ta dube shi.

"Yassar ka shiga taitayinka, mahaifin naka kake yiwa waɗannan kalaman marasa daɗi? Toh ya yi maku mammaƙon, kai ai namiji ne, namiji kuma da nema aka san shi. Guminsa ne ya gina wannan gidan, ya kuma mallaka mishi motocinsa, kai ma ka yi zuciya ka mayar da hankali a karatunka watarana ba Abbanku ba, da kanka sai ka siyawa kanka motar, ba na son shirme. Ni kiramin Yakubu a waya ka ce ya yi sauri ya ƙaraso, ina Humairar take ne..."

Ba ta ƙarasa zancen ba ta waiga, Humaira na tsaye a gefensu kasancewar su na magana ba su ko lura da ita ba. Itama ta yi shirinta tsaf cikin atamfarta koriya wacce tana ɗaya daga cikin ɗinkunan da aka yi mata. Ta yi kyau sosai, murmushi ta ɗan yiwa Mamin.

"Mami na fito ai."

Yassar ya ja tsaki ya bar wajen don takaicin Mamin da kuma na ganin Humairar da yake jin haushi da kishin tattalinta da iyayen nasu suke yi sai ka ce su ba ƴaƴa ba ne, Mami na kwala mishi kira amma bai ko waigo ba sai amsawar da ya yi da ƙarfi.

"Zan je na É—au wayar ne na kiramaki Yakubun."

Daga haka ya ci gaba da tafiyarsa, Mami ta girgiza kai fuskarta ɗauke da matsanancin damuwa. Sai jikin Humaira ya yi sanyi, wannan kalar zamantakewar mutanen gidan na ba ta mamaki, ace ƴaƴa ba sa ganin iyayensu da gashi, kowace magana ta fito a bakinsu hakanan za su watsa musu ba tare da taunawa ba, toh wace riba ake samu a hakan? Ita tunda ta zo ma ban da Ummita da Raihana sai Muhsin masu ƙokarin zuwa islamiyya, ba ta ga wani cikin su Tasleem na zuwa ba. Bar su dai da yawon gidan ƙawaye a ɓoye Abban bai sani ba. Itama dai Raihanan ba zama take sosai ba amma takan tsaya har a biya karatu da ita,  wasu lokutan sai dai ta ji tana amsa wayar zasu haɗu da wani saurayin idan ta fita makaranta.
    A yanzu kuwa daga maganganun Mamin ta fahimci watakila Yassar kuɗi ya nema ko wani abin da bai samu ba ya faɗi abu game da Abban shi ne take goranta mishi.

"Muje Humaira, ya zo."

Ta amsa da toh ta bi bayan Mamin cike da jin tausayinta, kowace uwa na son ta ga nata na bin ta sau da ƙafa, amma Mami ba ta samu wannan biyayyar ba na yara. Daga manyan har ƙananan, koda dai ta ji Ummita na cewa shi dai babban ɗan nasu ya bambanta da sauran, kuma su na masifar shakkarsa, akwai abubuwa da dama wanda idan yana nan ba sa aikatawa. Ta ce daidai da hantarar da suke yi mata idan har yana nan ba sa yi.

Har dai suka soma tafiya a titi tunane-tunane take yi, hankalinta jiya bai kwanta ba sai da ta tsinkayi Tasleem na hira da Raihana su na tsokanar Futuha akan marin da ta sha har su na faɗin gobe ma ta ƙara. Daga baya dai ko don tana ɗakin ne sai suka juye harshe zuwa turanci, ta lura ba su fiye yin buzanci ba su kam, a yadda Ummita ta ce ma, ba komai suka iya faɗi a yaren ba, sun dai fi ganewa idan an musu magana ba su iya mayarwa yadda ya kamata ba. Wannan sai babban yayansu. Shi dai yana ji sosai.

Daidai wani babban gida motar ta tsaya, suka fito suka nufi ciki. Kyau da tsaruwar gidan har ya so ya kere na su. Da murmushi Mami ta dubi Humaira lokacin da suka shiga farfajiyar gidan.

"Gidan aminiyata kenan Hajiya Lubna, ita ce za ta kai ki wajen koyon girki. Ƙanwarta ke yi."

Humaira ta gyaɗa kai ranta ya yi fari sol, ta san dai Mamin ta ce ta shirya zasu je unguwa amma ba ta kawo a rai fitar ta shafe ta ba. Daidai za su shiga babban falon suka yi karo da ɗan Hajiya Lubna shi kuma zai fito, matashin saurayi mai jini a jika, ya sha ƙananun kaya abinsa ya yi tsaf. A fuska ba za ka kira shi da kyakkyawa ba sai dai hutu da jin dadi ya sa fatarsa murmurewa. Gaisawa ya ke da Mamin amma hankalinsa kacokam na ga Humaira wacce daga kallo ɗaya da ta yi mishi ta kauda kanta don ita kam a duniya ta tsani kallo. Mami na lura da yanayin kallon da yake jifan Humairar da shi, ita kanta bai mata ba don haka don ta katse shirun ta ce.
 
"Hajiyar dai na ciki ko? Don na san ta yanzu sai ta iya ficewa ta bar ni zaman jira."

Dariya ya ɗan yi yana shafo ƙeyarsa.

"Tana ciki Hajjaju. Ku shiga kafin na shigo."

Ta amsa mishi ta yi gaba Humaira ta bi bayanta da sauri har tana tuntuɓe saboda kallon da yake bin ta da shi. Mami ta kalleta kawai ta kauda kai ba ta ce uffan ba. A falon gidan suka iske ƴan mata da yara ana kallo ana hira, wuta tarr a gidan madadin gidansu wanda idan har ba wutar Nepa aka ci sa'a suka kawo da rana ba, zai yi wahala ka ga hasken fitila a gidan sai Magriba zuwa ƙarfe sha biyun dare.

Gaba É—ayansu suka gaida Mami, ta amsa. Ta dubi Humaira.

"Ki zauna ki jira ni bari na ƙarasa wajenta." Ta amsa da toh ta nemi wuri ta zauna. Ta lura gidan dai ƴan boko ne, ba su ko damu da ita ba sai mai aikin gidan da ta miƙe ta kawo mata ruwa da lemu ganin da ta yi tare suke da aminiyar uwar ɗakinta. Godiya ta yi mata amma ba ta sha ba, hankalinta kacokam na garesu, wani shiri suke kallo na india, sun maida hankalinsu kacokam. Itama sai nata hankalin ya tafi can. Ta shafe mintuna goma a nan tana jiran Mami, can sai ga wani ɗan yaro ya sauko daga benen da Mamin ta hau.

"Ki je ana kiranki a sama."

"Toh" Kawai ta ce ta miƙe ta nufi hanyar da yaron ya fito, kafin ta ƙarasa ta tsinkayi wata muryar babbar mace na faɗin.

"Ke dai ki bi a hankali, kar ki yi garaje kamar yadda ki ka so yi a wancan lokacin."

Sallamarta yasa suka kalli hanyar da sauri, ba ta lura da yanayinsu ba ta karasa ta durkusa gefe ta gaida matar wacce kamanninta sak da wannan matashin da suka gani É—azun. Matar ta amsa mata fuska a sake.

"Ah Maryam, ki ce É—iyar tamu kyakkyawa ce masha Allah. Humaira ko?"

Humaira ta gyaɗa kai tana sunkuyar da kai murmushi a saman leɓbanta.

"Masha Allah, Allah ya yi albarka kin ji? Allah ya gafartawa Hajiya Fatima, idan kika biyo halinta kin more. Mace mai hakuri da kawaici. Allah ya gafarta mata."

Ta ji wani sanyi a ranta, a duniya tana jin daÉ—in a yabi Mahaifiyarta. Ta amsa da amin ita da Mami.

Mamin ta dube ta.

"Toh Humaira, gobe idan Allah ya kaimu koda ba ni ba, sai ku zo da Ummita a kaiki gidan koyon girkin. Na faɗamaki ta gida ce, ƙanwar Hajiya Lubna ce. Sai ki mayar da hankali ga abin da ya kai ki. Nasan kina da fahimta da saurin ɗaukar abu, don Allah kar ki ba mu kunya kin ji ko?"

Ta amsa da toh Mami. Kafin Mami ta É—ora daga inda ta tsaya wannan saurayin na É—azu ya hayo. Suka maida duba gareshi. Wani irin ajiysr zuciya ya sauke yana duban Humaira sannan ya maida kallonsa ga Mami.

"Ai na É—auka har kun tafi."

Mamin ta É—an yi murmushi kaÉ—an ta girgiza kai.

"Ina nan Kabeer, amma yanzun za mu tafi. Abban yara ya kusa komawa gida."

Ya karasa ya zauna. Hajiya Lubna nan da nan fuskarta ta sauya ganin kallon da yake jifan Humaira da shi. Mami ta dubi Humaira ta bata umarnin ta koma ƙasa ta yi jiranta za ta sauko su tafi. Daga fitarta shi ma ya miƙe caraf ya bi bayanta. Hajiya Lubna za ta yi magana, Mami da sauri ta hana ta ta hanyar ɗan dafe kafaɗarta. Dole ta fasa. Amma ta kudurce a ranta lallai za ta yiwa abin tufka don ita kam ɗiyar ubangidan mijinta take so ya aura, ta kuma lura da yadda yake bin Humaira kamar jela to akwai wata a ƙasa. Ƙwafa kawai ta yi ta watsar suka ɗora hirarsu daga inda suka tsaya.
Chapter 8 · 0% Book details