← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 72 OF 101

Sashe 72

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

***
Mami kuwa ta cika ta yi fam, abu biyu ne suka haɗe mata, ga hotunan gidan da Futuha ta aikomata da kuma wayar da suka yi tana rusa uban ihun kuka tana cewa gida za ta taho yanzun a daren, ga kuma labarin auren Humaira da Fadeel da take ji a wurin Abba sai aka yi katari a ranar kuma Humaira ta fita hira wajensa. Wannan ranar ta fi kowacce baƙin ciki a wajenta. Suna falo zaune har Anna da ta fito saboda tashin hankalin akurkin gidan da ta ga Futuha ta koma da kuma batun yajin da ta dako har ana batun tana hanyar dawowa gida, sai yare suke bugawa a falon Jannat tana yi itama Annar na yi, Raihana da su Mubarak dai sai tausarsu suke yi inda Mubarak ya dage akan lallai idan Futuha ta tako yau sai ta juya ta koma gidanta acewarsa ba za ta tayarwa Abba hankali ba ga shi yana fama da hawan jini. Anna kuwa ta dage lallai sai Futuha ta dawo gidan tunda ba haka aka yi da Yakubun ba, a wannan yanayin Humaira ta shigo falon fuskarta dauke da murmushi sai baza uban ƙamshi take yi mai sanyi. Ganin yanayin mutan gida sai da ta ji dam saboda ta yi zaton ko wani abun ne ya kuma faruwa. Idanunsu a kanta, ga Anna da Jannat harara ne, Mami kuwa ba za ka tantance ba sai dai fa fuskar a haɗe take tamau. Humaira ta dake ta ƙarasa ta gaida Anna. Ba ta ko kalle ta ba balle ta amsa, ganin haka ta mike za ta nufi ɗaki Mami ta yi mata tsawar da kowa a falon sai da ya dube ta.

"Ke! Da iznin uban wa ki ka fita wajen Fadeel?!!!"Kamar an É—inke mata baki sai ta kasa cewa uffan yayinda Raihana ta yi caraf ta amsa.

"Mami na fadamaki fa kuma Abba yace Yaya Fadeel ya zama É—an gida tunda zai auri Æ´ar gida. Kiyi hakuri please ki daina jin haushinsa yanzu tunda har Sis Tasleem ma ta yi aurenta ta manta da shi."

Wani kallon banza Mamin ta watsamata, Anna da Jannat dai idaunsu kawai suka zuba ga Mamin saboda sun kasa yarda ita ce, a zuƙatansu basu taɓa jin sanyi cikinsa ba kamar yanzun musamman Anna da take ganin fuskar tsohuwar Mamin da ta sani a Agadez a na wannan. Mami kuwa kamar ta yi shiru sai ta yi tunanin watakila shirun nata ya tona ainahin abin da ke ranta musamman ma ga su Jannat ga Mubarak da suka zubamata idanu cikin hankalta. Don haka ta sauke ajiyar zuciya.

"Shikenan wuce ki shiga ciki ki sauya kaya. Anjima zamu yi magana."

Humaira wacce idanunta suka cicciko da hawaye ta gyaɗa kai gami da miƙewa ta bar falon tana ji kamar an muzanta ta. Haka ta koma ɗakinsu cikin mutuwar jiki.

"Ke da Mami ko?"

Ummita ta wurga mata tambayar da ya sanya ta dubanta, tana daga zaune saman darduma bayan ta idar da salatin Annabi s.a.w. Kaf abin da ya faru tana ji daga inda take. Ɗan murmushin yaƙe ta yi mata.

"Ban san kuskuren dake cikin nagartar Fadeel ba, watakila kuma sai yanzu da idanuna suka soma ganinsa da ƙima wata silar za ta raba mu ta nisanta mu da juna idan har hakan zai faranta ran Mami."

Girgiza kai Ummita ta yi.

"Ban ce ki bijirewa dukkan wani umarni na Mami ba, amma ki sani, ba Mami ce kaɗai me iko a kanmu ba. Abba shi ne mafi ƙarfin ikon zartarwa. Idan har Allah ya ƙaddara aure tsakaninku babu wani mahaluƙi da zai iya dakatar da faruwar hakan. Mami hujjarta ba karɓaɓɓiya ba ce, akan wane dalili don bai auri wata ba wacce dama tun farkon fari ba dominta ya ƙulla zumunta da gidannan ba, ace za a haramtawa wacce ba ta ji ba kuma ba ta gani ba abin da Allah bai haranta ma ta ba? Anan dai na raba fahimta da Mami."

Humaira ta sauke nannauyan ajiyar zuciya har a lokacin ba ta dauke idanu cikin na Ummita ba ta ce.

"Bana son saƙe-saƙen da zuciyata ta soma yimin akan Mami, iyakar ƙarfina nake ƙoƙarin ƙaryata tunanina Ummita sai dai hakan na nema ya faskara."

ÆŠan murmushi mai ciwo Ummita ta yi mata.

"Na fahimceki, ba kuma na son saka Mami a jerin masu son zuciya idan nayi haka kamar ban mata adalci ba duba da yanayin riƙon da ta yi mana na nuna fifiko akan yaranta na ciki. Sai dai a wannan gaɓar bana goyon bayan hakan, ki toshe kunnuwanki Humaira. Fadeel mutumin kirki ne, a duniya ban da soyayyar iyayenki, zan iya rantse maki Fadeel ne masoyinki na gaske bayansu don ko mu ba lallai mu nuna mishi sonki ba. Ya sadaukar da lokacinsa duk a kanki, shekara da kusan watanni ya jure dukkan wulakanci da baƙaƙen maganganun da sauran mazan da suke sonki da aure suka kasa jura suka kama hanyar gabansu, Fadeel ya cancanci ki aureshi. Ba fata nake maki ba amma muddin kika zama mai juya baya a gareshi da ƙin yarda da shi, wallahi Humaira haƙƙinsa ba zai bar ki ba."

Daidai wannan gaɓar hawaye suka wanke fuskar Humaira, ta sani gaskiya ɗaya ita ce Ummita ta faɗamata. Har haushin kanta take ji idan ta tuna yanda ya dinga ya bibiyarta a bainar jama'a tana yanƙwana shi. Ya jure dukkan wannan ya kuma sadaukar da lokacinsa don kawai ya ga ta sauko don kanta ta aminta da shi, ita kuwa me zai sa ta butulce masa?

Daga haka Ummita ba ta ƙara ce mata uffan ba, ai ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali, don haka ta bar ta da tunani iri-iri a ƙasan ranta.

***
A falon kuwa da fitar Humaira sai Jannat ta kwashe da dariya.

"Mamin yara kenan, yau kuma marainiyar Allahn Æ´ar gaban goshinki da ba ta laifi ita kike yiwa wannan É—ibar albarkar?"

Mami ba ta ce uffan ba don har lokacin zuciyarta a zafafe take musamman da Jannat ta alaƙanta Humaira da sunan ƴar gaban goshinta. Wannan ko a mafarki ba ta hangen haka.

"Mami, don Allah ki bar Humaira da Fadeel haka, idan har yanda Raihana ta ce sanadiyyar Tasleem ne. Yanzu Tasleem igiyoyi uku ne a kanta har da ƙaruwar Baby da ta samu. Ni ban san dalilinki na hana ta kula matashi mai kirkinsa ba."

Waɗannan zantukan su na fitowa kai tsaye daga bakin Mubarak, kafin ta tattaro amsar da za ta ba shi sai ga Futuha ta bankaɗo labulen falon ta shigo a haukace tana wani irin kuka da sheshsheƙa, ta ci uban ado an shafe fuska da Foundation amma sanadin kukan da ta sha duk sai ta koma kamar wata aljana. Ganin Mubarak a zaune bai sa ta bar ihu da kukan da ta fasa ba, gaba daya suka miƙe ita kuwa kai tsaye jikin Antinta Jannat ta faɗa gami da ƙara sautin kuka da ihu. Wannan ya yi sanadin shigowar Abba falon don tun ɗazun yake tsinkayar muryoyi a sama amma na yanzu ya fi duk na baya shiga kunnuwansa don haka ya shigo falon a hargitse. Ganinsa sai Anna ta ɗan ja jiki ta koma ladabin ƙarya kamar yanda ta saba yi a gabansa. Tsawa ya dakawa Futuha ba shiri ta kame bakinta ta yi shiru, Mami sam ba ta so zuwan Abban ba don zai iya lalata shirinta ya sa Futuha komawa dakin mijinta a yau. Ya kuwa jefowa Mamin tambayar abin da ke faruwa idanunsa ma ko kan Anna bai kai ba saboda tsoro da fargabar da ihun Futuha ya haifar masa. Mami ta ɗan gyara murya ta ce.

"Ke Futuha sai kiyi masa bayani, waƙa a bakin mai ita ta fi dadi ai."

Futuha ta dubi Mami sannan ta maida kai ga Abba amma ta kasa cewa komai tsabar fargaba. Jannat ta yi kundunbala ta soma magana muryarta dauke da salon makirci, nan ta labartawa Abban ƙarya da gaskiya akan ginin da Yakubu ya yiwa Futibar ya maida ta. Abba ya tamke fuska tamau, Jannat ba ta taɓa ganin ya dube ta da tsantsar ɓacin rai da rashin walwala ba sai a ranar.

"Shi ne me?"

Tambayar ta sa Jannat kasa cewa uffan, sai Mubarak ne ya yi caraf ya amsawa Abban.

"Shi ne ita kuma ta dawo gida ta ce ba za ta rayu a cikinsa ba."

Abba ya nuna Futuha da yatsa.

"Ke, ki saurare ni dakyau, ni dai ubanki Isuhu ina raye a kan idanuna ba za ki maida ni mutumin banza ba da bai san me yake yi ba. Kai Mubarak ka dauki mota ka maida ta ka kuma tabbatar ta shiga gidan aurenta kafin ka dawo gida. Ba zan É—auki wannan sakarcin wofin ba."

Anna tana so ta yi magana amma tana gudun zubewar girmanta a idanun Abba, girman da ta ɓoye ainahin zuciyarta ta danne komai ta shekara da shekaru wajen gina shi a idanun Abban don haka ta ja bakinta ta yi shiru, Jannat kuwa ta ƙulu iyakar ƙuluwa. Balle kuma Mami da take jira Abban ya koma ɓangarensa ta je su buga wacce za su buga don bai isa ba sai ya ƙwatarwa diyarta ƴanci. Hakanan Futuha tana kuka ta bi bayan Mubarak suka tafi, a mota ganin ta cika shi da ihu ya dakamata tsawar da ta hargitsa ta, ya koma Mubarak ɗinsa sak da suke shakka, dole ta haɗiye sauran kukan ta koma yinsa a ciki ciki yanda ba zai ji ba.

***
Ya kammala shirin baccinsa tsaf zuciyarsa duk a ɓace saboda takaicin Futuha, haka Mami ta shigo tana ɗaure masa fuska, ya dube ta kadan kuma ya ba kansa cewa damuwar ce itama ke cinta wannan ya sa bai ce mata uffan ba. Sai da ta mula don kanta sannan ta magantu.

"Abban yara wane irin hukunci ne ka zartar akan al'amarin da ba ka ganewa idanunka zahiri ba?"

Da ɗan mamaki ya juyo daga barin chajin da yake ƙokarin sanyawa a wayar ya dube ta.

"Kika ce me?"

Ta kauda kai har lokacin fuskarta a daure ta amsa.
Chapter 72 · 0% Book details