← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 93 OF 101

Sashe 93

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Haka Baba Amina ta yi ta yi mata maganganu masu ratsa zuciya har sai da jikinta ya yi sanyi. A karshe ta soma cin kazar su na zolayarta. Hajjo ta mike ta fice zuwa wurin yan uwansu da suke ɗakin baƙi. Itama Baba Amina ta fita wannan ya ba Raihana damar dawowa ta zauna gefen Humaira tana yamutsa fuska.

"Wai kun ji labarin an yiwa Sis Futuha kishiya kuwa?"

Dagaske ba su da wannan labarin, Humaira dai ta ganta tana kuka ranar da Fadeel ya zo amma ba ta samu damar cewa uffan ba saboda umarnin da Mami ta ba ta a lokacin.

"Kai Raihana, dagaske kike?" Fadin Ummita.

Taɓe baki ta yi.

"Allah ko dagaske, Ƴar Snow mijinta ya aura."

"Ƴar Snow fa kike ce?!"

Fadin Ummita idanunta waje. Humaira ko sai da ta ɗan yi jim don ta na tunani kamar ta san sunan kamar kuma ba ta sani ba. Can ta tuna wace ce, wacce dai ta yiwa Futuhar mummunan ƙazafin da ya yi sanadin aurenta da Yakubu ba Ibb da take mutuwar so ba.

"Ita dai, yau ma za ta tare kuma a gidan da Futuha ta fito. An mata gyara sosai. Hum, ta tashi hankalinta ita kuma, dazu har rotse ta yi mishi a goshi dakyar ya kwaci kansa ya bar gidanta. Abba ma ya je ya yi mata kaca-kaca da barazanar saɓa mata muddin ta ƙara gangancin kashe rai. Ba don Abban da abokin Yakubun ba ai da tuni itama ta dawo gida zawarci."

Raihana ta karashe zuciyarta a karye har kwalla sai da ta cika idanunta. Rashin sa'ar ƴan uwa mata da ma rashin sa'ar uwa ta gari yana mata zafi a ranta. Me suka ɗauki duniya ne haka? Kowanne cikinsu dogon buri ya ke ci mata kai ka ce shi ke da alhakin ƙayyadewa kansa lokacin da zai mutu. Futuha a zahiri ta nuna kwadayin abin hannun Yakubu, yau gashinan ya nuna mata halin maza ire-irensa. Tasleem ko ba ta ma san a layin da za ta jera ta ba.

"Allah ya kyauta. Ya tsare. Amma ta bani tausayi gaskiya. Ai ko ni duk hakurin ba na jin zan iya zama da wacce ta yimin ƙazafi ba a rayuwa."

Fadin Ummita kenan da ya katse tunanin Raihana.

"Amma a ganinki tun farko laifin waye? Laifinta ne da ta zaɓi duniyar Tiktok akan zahirinta, Allah dai ya tsare."

Suka amsa da amin.

***
Misalin karfe biyar na yamma aka shirya Humaira cikin wani arnen leshi mai daukar idanu kalar yellow ochre, ta yi wani irin kyau da ta fito tamkar a matar wani hamshaƙin. Ummita kanta ta ci ado sosai cikin wani leshi golden da suka yi ankonsa da Raihana. Su biyu kacal suka yi shi, Ahmad kuwa Hajjo ta karɓe ta ce wajenta zai zauna ita ce mai rainonsa. Duk kuwa ta yi hakan ne don kar ya hana Ummita sakewa a wurin biki, tana fatan itama Allah ya fiddo mata da miji ta yi aure.

Gidan gaba daya aka fice har Mami wacce Hajiya Lubna ta yi ta yiwa famfon kar ta bari a kwace mata ragamar gida. Wato ta zuba idanu Baba Amina ta yi mulki a gidan mijinta alhalin ita ya dace komai ya ɓulla ta hannunta. Anti Laila kuwa ƙanwa ga Hajiya Lubna, wato matar da ta koyawa Humaira girke-girke. Takanas ta zo har da ƙatuwar ledarta na taya murnar aure da ta tahowa da Humairar. Ita kam da zuciya ɗaya ta ke sonta. Ta kuma iso da ƙaramin akwati mai dauke da agogo mai dankaren kyau daga Kabir dan Hajiya Lubna ya ce a ba Humaira. Humaira duka ta amsa ta damƙawa Raihana. Ita ko ta je ga Baba Amina dake zaune ta nunamata. Mami na kallon wannan diramar, haushin Raihana tamkar ya kashe ta, wato ba ta ma dauketa komai ba don tun zuwansu wurin yinin komai aka bada na Humairar wajen Baba Amina take kai shi. Ko inda Mamin take ba ta kalla, Mamin dai ta haɗe itama cikin wata shaddarta sabuwa da ta sa aka yi aikinta daga can Mali amma ba ta taɓa sanya ta ba sai a yau ta yi mata rana.

"Hajiya Maryam wallahi sai mun tashi tsaye, nikam ina tsoron kar wannan abu ya tabbata. Kiga yarinya duk ta fi yaranki more aure? Duba kiga yan uwan mijinta babu na raini a cikinsu. Suturarsu masu tsada ne na ƙarshe ina faɗamaki."

Hajiya Lubna ke wannan bayanin tana karewa su Anti Amarya da su Hannatu ƙanwar Fadeel kallo. Mami ta cika ta yi fam, ta ji kwallar baƙin ciki sun cika idanunta.

"Bar ni haka Hajiya Lubna, wallahi kuka nake son fashewa da shi. Wannan ranar baƙa ce a gareni kuma ba don kin matsa akan zuwan ba da babu inda zan tako don ban ga wani abu cikinsa bayan baƙin ciki ba. Yarana su na can cike da tashin hankali, amma wadannan hotihon banzan ba su kishin yan uwansu sam, ji yanda ita waccan ke zirga-zirga ke kya ce bikin kanin ubanta ake yi, ji don Allah yanda wancan soloɓiyon ya wage baki yana zubawa Humaira kudi."

Ta karashe tana duban Yassar da ya ke tiƙar rawa yana yi wa Humaira karin kudi da take tsaye a fili.

"Sai hakuri, farin cikinnan zamu san yanda zamu yi daga baya ya koma baƙin ciki."

Kallo bai tashi komawa sama ba, sai da aka yi kiran uwar Amarya ta fito, Mami da Baba Amina suka fita a lokaci guda. Wannan abu ya yiwa Mamin ciwo amma hakanan ta danne ta dinga zuba murmushin da bai je zuci ba. Humaira kuwa har hawaye ne suka zubomata, babu wanda ya fado a ranta sai Dada da mahaifiyarta. Baba Amina ta dan ja ta a jiki ta a goge mata fuskar da handkerchief sai hoto da liƙin ya koma kansu wannan ne dalilin barin Mami hall din gaba daya don hatta da MC din idan ya ambaci sunanta sai ya ambaci na Baba Amina.

Raihana ta fito don kai wa wasu ƙawayensu na makaranta kati dake waje, ta ji wayar Ummita dake jakarta na ƙara. Kafin ta ciro ya zama missedcall, ta ga ba ma kira daya ba ne, kira ne wurin goma sha wani abu daga Mubarak, Ridwan da kuma wata lambar da ta dauki hankalinta matuƙa kuma ta girgizata. Tana nan tsaye bayan ta ba da katin sun shige ta rasa abin yi sai kakkarwar hannu da jiki, wayar ta ƙara ringing. Lambar ce dai dagaske, lambar da ta gani a wayar Mamin har ta tura wa Abba. Ta yi saurin ɗagawa kirjinta na harbawa. Kafin ta yi magana ya riga ta.

"Blackbeauty, ina fatan kin dauki muryata? I am the Wizzy the father of Ahmad."

Ai ba ta san lokacin da ta durƙushe a cikin fararen duwatsun dake wurin ba, Wizzy da ya yiwa Ummita fyaɗe? Shi ne Wizzy da Mami ke waya da shi? Ta kara fiddo wayar a kunne ta duba dakyau, tabbas lambar ce ba ƙarya ba ne. Ta katse kiran ta ciro wayarta tuni hawaye sun gama wanke fuskarta ga wayar har tana faɗuwa a kan duwatsun ta buɗe ta fiddo lambar Wizzy dake wayarta, ta ƙura idanu tabbas ita ce dai lambar.

Mami wacce ke tsaye tare da Hajiya Lubna su na jiran direban Hajiya Lubnan da aka nema aka rasa ya kaÉ—a yawo, ta hango Raihana cikin halin ruÉ—ani. Ta dubi Hajiya Lubna.

"Raihana kuma? Meyafaru da ita?"

Hajiya Lubna ita dinma sai lokacin ta ankara da ita, cikin sauri suka hau tafiya zuwa inda take.Kafin Raihana ta kai ga daukar kowane mataki, wayar Ummita dake hannunta ya ƙara ringing, Mami daidai lokacin suka karaso ita kuma ta ɗaga wayar tana fadin.

"Waye Wizzy? Mene dalilinka na kiran Ummita?"

Kirjin Mami ya bada dam, suka dubi juna da Hajiya Lubna cikin tsananin kiɗima. Wizzy kuma? Kiran Ummita? Ai sai kafafun Mami suka hau rawa, dakyar ta karasa ta zagaya gaban Raihana, ita kuwa Raihana ganin Mami ya sanya ta ƙara nanata tambayar da ta yiwa Wizzy don ta ga yanayin da za ta shiga. Ai kuwa zaro idanu ta yi waje, hannu ta kai ta fisgi wayar.

"Bani mu ji waye?"

Haka kawai ta fadi ta sa wayar a kunne ta dan yi gaba acewarta wai ƙarar sautin da aka sanya a cikin hall ya sa ba ta jin abin da yake fadi. Hajiya Lubna cike da dabara ta riƙe hannun Raihana.

"Ki kwantar da hankalinki, ko waye za mu sani. Me ya ce maki ne naga duk kin shiga ruÉ—ani har da su kuka?"

Raihana ta bi matar da kallon munafuka mai ƙara tunzura uwarta. Ai dama sai hali ya zo ɗaya ake ƙawance. Ta sani sarai don kada ta bi bayan Mamin ne ya sa ta ke siyasance ta. Sai ta kauda kai ba tare da ta ce mata uffan ba. Hankalinta na kan Mamin da ta ba su baya ta kuma yi can nesa da su.

Mami kuwa ta saurari kalaman dake fitowa a bakin Wizzy.

"Ke wace ce? Ki ba wayar ga mai wayar uwa ga yarona ita nake son magana da ita kar ki bari na wulakanta rayuwarki kema."

"Wizzy." Ya ji muryar Mamin cikin kunnuwansa, sai kuma ya kyakyace da dariya.

"Oh, ki ce wayar fasin fasin ake da ita, daga hannun wannan sai na waccan, Hajjaju kenan. Kin yi mamakin jin na kira lambar Uwar yarona ko? Ki. Yi zaton zan zuba idanu na biyewa shirme da shiriritarki? Kin kasa cika umarnina ma fiddo Nusy har jami'ai sun fara farauta ta saboda ta ba da kwatancen inda nake, ta ci amanata. Yanzu haka na yi nesa da Kano da ma duk inda aka san za a gan ni na koma ainahin ƙauyenmu. Toh ki sani, a duk radda na tashi dawowa zan yi zuwan a mutu ko a rayu, ba Ahmad kadai ba har uwar Ahmad zan dauke ke kuma haɗuwarmu dama na faɗamaki ai ba za ta yi kyau ba. Ki shirya tonan asirikanki."

Gumi ya shiga tsirfowa Mami, ta dan juya ta dubi  su Raihana, ta kuwa kuramata idanu babu ko kiftawa. Ta kauda kai ta ce.
Chapter 93 · 0% Book details