Sashe 100
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Maryama baki da hankali! Ke mahaukaciya ce ashe ina maki kallon mutum mai hankali? Ta ya ya za ki samu saɓani da mutum ki yi mishi zagin uwaka ubaka kuma ki tura ɗiyarki wajensa?! Shikenan! Yanzu dai ta tabbata ɗan Bokanki ne a cikin Ɗiyarki."
Wannan kalma ta ƙarshe na Anna ya mugun jijjiga zuciyar Mami. Ai sai ta fashe da wani irin kuka, Jannat masoyiya ga Tasleem itama kukan ta sanya gami da zuwa ta ɗago Tasleem tana rantsuwar ita dai wallahi sai ta kai ta an zubar da cikin. Nan da nan Tasleem ta ture ta.
"Aa wallahi! Ba wanda ya isa ya zubarmin da ciki, Babandi ya ce idan na tabbatar ciki ne da ni toh yana son abinsa idan na haihu na kai masa!"
Tana maganar kamar ba Tasleem ba cike da faɗa idanunta tsaye kai ka ce ba ita ta gama kuka yanzu ba. Gaba daya suka bi ta da kallon mamaki. Kiran da Dawud ke kwalawa Mami iyakar ƙarfinsa ya yi sanadin da suka ɗunguma cikin tashin hankali zuwa waje. A falo suka yi kiciɓus da shi, lokacin su Hajjo sun dawo ba su kai ga shigewa masaukinsu ba. Wasu kuwa sun fice zuwa kasuwa ƙarasa siyayya.
"Meyafaru Dawud?" Ta tambaya jikinta a mugun mace. Kan ya kai ga cewa komai sai ga Ridwan cikin kayan aikinsa da abokan aikinnasa su uku, biyu mata sai É—aya namiji. Fuskarnan tamkar ba shi ne mai fara'a ranar bikin Fadeel ba. Ya É—aure ta tamau, ya fito a jami'in aikin na gaske marar son wasa. Arrest warrant ya buÉ—e ya nunawa Mami.
"Hajiya mun zo tafiya dake bisa zargin da ake yi maki na garkuwa da yaran maigidanki. Hukuma ta bamu damar shigar da ƙara kotu."
Wani razanannen ihu Futuha ta saki tana ƙunduma uban ashar wai ƙarya ne. Shi kuwa Dawud hawaye kawai yake fitarwa don dama labarin da ya zo kawo wa Mamin kenan. Su Hajjo suka yi cirko-cirko suna kallon ikon Allah har matan nan suka nufi Mami da zummar tisa ƙeyarta a tafi.
"Me kuke nufi? Ina ku ke zaton za ku kai ni?! Yanzu a ganinku zan cutar da yaran da nake yiwa so fiye da yara a da na haifa?"
"Hajiya wannan duka shari'a ce za ta bayyana. Yanzu dai ki bamu haÉ—in kai mu yi aikin da ke gabanmu."
Wannan ranar ta zo musu da tashin hankula iri-iri. Futuha ta É—auki waya ta yi kiran Abba, koda ta sanar masa ban da Allah ya kyauta gami da kashe wayar babu abin da ya ce. Nan Futuha ta hau fadin wai dama Abba ba sonsu yake ba, ya fi so ya ga sun watse sun bi duniya! Mami kadai ke son su tsawon shekarun nan komai da take yi don su take yi.
Ganin Futuha na kokarin yin suɓul da baka ne ya sanya Mami dakamata wata tsawar.
"Ke! Ya isa hakanan! Nace ki bari haka! Ai ƙarya fure take ba ta ƴaƴa. Idan ma an yi hakan don a ɓatawa uwarku suna ki kwantar da hankalinki babu inda ƙarya za ta je. Duk inda za su kai ni zan fito."
Abin da Mamin ta ce kenan sannan ta yi gaba ma'aikatan suka mara mata baya. Ridwan sai da ya tsaya ya É—an waiga, rashin ganin Ummita a wurin sai ya ji hakan bai masa dadi ba. Kawai sai ya sa kai ya fice.
Nan fa yaran Mami kamar su yi hauka. Suka kira Mubarak suka labarta masa, hankalinsa ya tashi. Ya kira Abba, Abba ya kwantar da hankalinsa ya ce ya yi hakuri ya nutsu tunda satika ya rage ya kammala ya dawo, ya bari zai kula da komai.
***
Kamar da wasa sai ga Mami har tsawon sati a hannu hukuma, babu duka balle zagi, ta kafe akan ita ba ta san Wizzy ba kuma ba ta san ma a inda ya santa ba. Wizzy ma an tambaye shi yace shi bai taɓa ganin wacce suke waya ba, amma ya riƙe muryar. Ya kuma sani matar uban su Humairar ce.
Sai da Mami ta cika sati aka shiga kotu, duka wannan Abba yana asibiti adalilin ciwonsa da ya tashi. Raihana ko ta dawo gida amma Abba ya bata umarnin tattarawa ta koma gidan Baba Amina don ta ƙarasa jarrabawarta. Ummita kuwa tana Bichi amma sanadin shari'ar sai da ta dawo.
Ita da Humaira aka nemi su bada bayanin komai da ya faru da su, haka kowaccensu ta yi magana zuciyoyin cike da rauni babu kamar Ummita dake ƙara jin tsanar Sadik Wizzy da su Baaba wadanda duk aka titso ƙeyarsu ta hanyar Wizzy din, kowannensu ya amsa eh ya aikata laifin idan ka cire Mami da ta dage akan ita sharri da ƙage akai mata. Lauyar da Hajiya Lubna ta ɗaukar mata ta tsaya tsayin daka wurin yi mata wannan yaƙin. Aka yankewa su Wizzy hukunci daidai da laifukansu yayin da kotu ta wanke Mami daga zargi bisa duba da rashin hujja koda ƙwaya ɗaya da za'a kama ta dominsa.
***
Ta dawo gidanta hankali kwance, yaranta gaba daya su na cike da farin cikin kuɓutar mahaifiyarsu da kuma wanke ta da kotu ta yi idan ka cire Raihana da ba ta gidan kuma ko labarin ma ba ta kaunar ta ji. Ummita da Humaira kuwa har abada ba su jin za su ƙara aminta da Mami. Ballantana kuma Abba da yake ji a jikinsa lallai da saka hannunta. Ya kuma kara yarda da kalar zalunci na matar da yake aure.
Ta iske Abban a falonsa zaune yana kallon labarai, ga dukkan alamu hankalinsa ma ba ya kan talabijin din, ya zurfafa cikin tunani. Gaba daya ya rame kamar wanda ya yi cutar watanni. Ita kanta Mami ta rame saboda tashin hankulan da ta gani a wannan ƴan watannin. Zama ta yi gefensa. Ya ji zuwannata amma bai ko kalle ta ba. Kafin ta kai ga magana ya riga ta cikin shaƙaƙƙiyar murya.
"Maryam, zaman me Jannat take yi a gidana?"
Ta yi turus, ta yi zaton zai ce wani abu a kanta amma sai ta ji ba ma ta itan yake ba. Cikin Æ´ar borin kunya ta ce.
"Ina za ta iya tafiya gidanta alhalin yar uwarta na garƙame a wajen jami'an tsaro? Adalilina ne ya sanya ta ke zaune."
Ya miƙe zaune sosai daga kishingiɗar da ya yi.
"Ta tattara ta bar min gidana, ba na buƙatar ganinta. Abin nufi, koda wasa kada ta ƙara gangancin takowa cikin gidannan! Gida dai nawa ne, ni ke da iko da shi! Toh daga yau ba na buƙatar ta ƙara zuwa."
Sulhu take nema, tana so ta shawo kansa don ta san meke tafe a ransa a kanta don haka sai ta yi saurin amsawa.
"An gama Abban yara. Zan sanar da ita ba za ta ƙara takowa ba."
Bai ce uffan ba ya na ta tufka da warwara har sai da ya ji ta kwantar da kai saman kafaÉ—arsa.
"Abban yara kana kaunata, naji ance har kwanciya asibiti ka yi sadda aka tafi da ni. Nayi mamakin wannan ƙazafin da wannan baƙin azzalumin ya so ya yimin, ya kusa raba ni da rigar mutuncina."
Abba ya yi wani murmushi mai ciwo.
"Kika ce rigar mutunci Maryama? Ina rigar mutuncin naki yake? Ai a yanzun ma da nake tare da ke, DARAJA ÆŠAYA kawai kike ci. Ban da wannan kusan zan iya cewa babu komai da ya rage a tsakanina da ke."
Yana kai wa nan ya zame kanta daga kafaÉ—arsa, ta yi wani irin zama tana kallonsa satoto.
"Bangane nufinka ba? Daraja É—aya kamar ya? Igiyar auren fa?"
Ta yi tambayar zuciyarta na duka da karfi, kallonsa take yi kawai tana lissafo ire-iren tashin hankulan da ta jefa kanta ciki duk a sanadiyyarsa da yaranta. Toh me Yusuf ke shirin ce mata?Abba ya yi É—an murmushin takaici.
"Aure? Ai ba ki ɗauke ni miji ba. Nima rashin sani ne ya kai ni ga ɗaukar mace irinki a matsayin matar aure, uwa ga yarana. A iyakar zaman da nayi da ke, ki faɗamin abu guda da na tauye maki na haƙƙoƙinki dake rataye a wuyana Maryama. Abin da ban taɓa zato ba, ashe wayona da hankalina bai min rana ba tunda har na rayu da mace irinki mai fuska biyu har na tsawon shekarunnan ba tare da na ankara ba. Kura da fatar akuya, kin cutar da ni kin cutar da ahalina. Na riƙe ki da zuciya daya, na kula da ke da kuma naki. Wannan wane kalar sakayya kika yimin? Ni dai Yusuf kika so a kashe? Kika gurɓata rayuwar yarana? Da me na rage ki? Wace buƙatar ce da ta zame min wajibi ba na kokari wajen sauke shi?"
Mami sauraronsa take yi amma fa gaba ɗaya ya gama kashe mata dukkan wani kuzari. Kirjinta ya hau bugu fat! fat! Wato ta tabbata dai Abba da kansa ya sani ta yi yunƙurin kashe shi da Humaira? Ashe dama kurum ya yi yake bin ta da kallon shashasha? Dama rigar mutuncinta ya jima da kecewa a idanunsa? Wani gumi ya shiga tsirfo mata, tana sauraronsa amma ba ta iya fadin ko harafin A ba har ya kammala ya mike ya fice zuwa ɗaki ya bar ta da nanata zantukan ƙarshe da ya yi.
"Ki nesanta kanki daga zuwa ɗakina Maryama. Ki zauna a naki ɗakin har zuwa sadda mai yiwuwa ko zaman ya ƙare ko wani abun daban saɓanin tunaninmu ni da ke."
Mikewa tsaye ta yi gwuiwoyinta a sake, ashe dai har yanzu akwai sauran rina a kaba, a tunaninta ta gama rufe bakin tsanyar tunda har shari'a ta wanke ta ba tare da kawo hujja ko daya zai nuna akwai sa hannunta ba. Lallai kafin Abba ya ankare da abubuwan da ta shuka na baya, ya kamata ta san mafitarta. Da wannan ta miƙe ta koma ɗakinta.