← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 84 OF 101

Sashe 84

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Maganganunta sun sa Mami ta yi ɗif na wucin gadi, ta kuma kalli Anna wacce ke kallonta itama cikin rashin fahimtar komai sannan ta maida duba ga Futuha da alamar tambaya. Futuha kuwa ta kauda kanta tana ɗan taka yatsun ƙafar Tasleem, tana bin ta da kallon ya za ta yi mata haka? Ita kuwa Tasleem kafaɗunta kawai ta ɗaga kaɗan gami da kauda idanunta don ta rantse ta shirya yaƙi da duk wanda ya ce sai ta koma gidan Hamza. Yanzu dai Mami ce za ta yi mata yaƙin da za ta wanku a idanun Abba ko kuma ta yi barazanar tonamata asiri a wajensa. Wannan shi ne ƙudurinta.*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

"Ke! Ni sa'arki ce? Ni kike yiwa wannan maganganun?"

Mamin ta fadi cikin zafi da kuma son sanin ainahin manufar Tasleem din.

"Nasan komai Mami, na san wace ce ke da abubuwan da kika aikata. Wallahi samun da za ki yi na rufamaki sirrikanki nayi shiru da bakina guda daya ne, ki wanke ni a wurin Abba ya amince na zauna a gidan ba tare da kwaɓa ko wata tuhuma ba. Wannan kaɗai za ki yimin ni kuma na maki alƙawarin zan ɓoye komai."

Gumi ne ya tsirfowa Mami a goshi, kirjinta har wani tagwayen lugude ya shiga yi. Wane irin suɓul da baka ta yi har ta zayyanewa Futuha komai da komai ba tare da tunanin hakan kan iya haifar mata matsaloli a gaba ba? Yanzu gashinan wa gari ya waya? Kai! Wai Tasleem dai ɗiyar cikinta ke yi mata barazana ko kuma ta tona mata asiri? Ta kara ɗaga idanu ta kalli Tasleem din wacce Anna ta damu da tambayar mene ne shi din da Mamin ta aikata amma ba ta ce uffan ba itama idanunta a kan Mamin tarr babu shakkar komai. Wannan ya ƙara firgitar da Mamin, sai kawai ta sanya kai ta bar ɗakin ta fice ba ya ko tsaya amsa kiran da Anna ke kwala mata ba.

"Kai bana son iskanci kun ji ko? Ku faÉ—amin abin da Maryam ta aikata na san matakin dauka kafin itama wannan mugun uban naku ya sa a ficemin da ita."

"Haba Anna, duk fa lalacewar uba uba ne."

Futuha ce ta fadi don har ga Allah ta ji sosuwar rai bisa kiran Ubansu mugu da aka yi. Tsaki Tasleem ta ja.

"Sai ki yi ai, uban da bai damu da namu farin cikin ba za ki shigarwa don an fadi aibu a kansa? Anna bari kiji abubuwan ban mamakin da É—iyarki ta aikata."

Tana fadin haka ta kwashe dukkan wasu labaran da Futuha ta ba ta ta fesarwa Tasleem, inda ta yi kuskue Futuha ta gyara, idan ma mantuwa ce ta yi sai ta tuna mata. Anna wani irin murmushi take yi sosai. Sai da suka kai aya sannan ta girgiza kai.

"Ban yi mamaki ba. Maryama dai da na baku labari akan zafin kishi za ta iya aikata komai, ban yi mamaki ba. Sai dai na cika da al'ajabin yanda har ni ta ɓoyewa wadannan labaran. Kai an gaida Maryama. Muna mata kallon biri tana mana kallon ayaba."

"Uhum, ai ni kaina Anna na sha mamaki. Farko na yi zaton duk don soyayyarmu ce ta sanya amma kuma zuwa yanzu na fahimci son zuciyar Mami ne. Kanta kaÉ—ai ta sani ba ta damu da mu ba."

Tasleem ta furta a zafafe. Futuha ta girgiza kai ta bude baki za ta yi magana Anna ta tari numfashinta.

"Shashasha kawai, ke ba ki san Maryama ba. Son kanta ai ku din ne kan nata. Ni na sani tabbas dagaske domin ku samu jin dadi da walwalar ta aikata hakan, amma shi ne don ranki a ɓace yake kike neman kwaye mata zani a kasuwa ko?"

Tasleem dai turo baki tayi kawai tana kokarin fiddo nono ta ba bebinta. Sai kuma aka koma jimamin Anti Jannat, Futuha ta kira Yakubu ta sanar masa komai saboda sanin da ta yi yana da manyan mutane watakila su shiga rigar alfarma a saki Jannat.

***
NIJAR

Humaira cikin Æ´an uwanta da abokan arziki a garin na Maine. Gaba daya a kwanaki uku da ta yi ba ta da wata damuwa sai farin ciki da annashuwa. Kawunta sosai yake hidimar kawo mata dukkan wani abu da take so. Matarsa Tanti Hafsatu da suke kira da Hajjo kuwa ita da wasu cikin yan uwan Mamanta tun zuwanta aka soma yi mata gyare-gyaren aure. Ci wancan sha wannan, wasu kuwa tana ji sai dai su ce ba yanzu ba sai a ranar da za a kai ta. Wannan gatan da take samu ya sanya har hawaye takan yi, ta sani ba don Mami ta dauki fushi da ita kan lamarin Fadeel ba, babu abu daya da ba za ta samu daga gareta ba. Amma fushin ya kore komai. Sun gaisa da Abba a wayar Kawu amma koda wasa bai yi mata wani bayanin game da abubuwan da ke faruwa ba. Hakanan Fadeel da su Ummita, su din ma babu wanda ya ce komai. Shi Fadeel batu ne na Jannat, koda wasa bai bari ta ji ba don ba ya son abin da zai É—aga hankalinta.

A rana ta hudu Kawu ya kawo mata magungunan tsarin jiki sai rubutuka da ya yi mata. Tun soma shan da ta yi ta soma jin sauyi daga gangar jikinta. Ya ba ta addu'o'i masu ƙarfi ya ce ta dinga yi kullum safe da yamma sai kuma tashin dare da ya lura tana yi har ya zame mata jiki, nan ma ya bata wasu addu'o'in. Ya kuma ce ta dinga karanta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin ƙafa arba'in duk sadda ta shiga wata damuwa.
A kwanakin da ta yi ta ga soyayya da kauna matuka, har ta cika sati cif bata da wata damuwa ko na É—igo. Ana gobe za ta wuce su na zaune su na shan hira da Kawu yana mata nasiha akan zaman aure da kuma irin kyawawan halayyar mahaifiyarta sak ta dube shi cikin nutsuwa.

"Kawu, don Allah mene ne maƙasudin rabuwar Mamana da Abba?"

Ya ɗan yi shiru, toh meye amfanin ɓoyon tunda har Fatima a yau babu ita? Shi kansa akwai al'amarin da ya ɗaure masa kai a labarin wanda har yanzu bai fahimta ba sai dai ya yi karfin halin ba Humaira dukkan labari. Daga na irin soyayya da kaunar da Abba suka yi da Fatima, da ma kuma yanda a karshe ta zo ta tsane shi mugun tsana wanda sun sha tambayarta ta ce musu ita dai ba ta sani ba kawai ta tsane shi. Ya ƙara da fadin.

"Wannan tsanar har Fatima ta mutu ba mu gano silarta ba, idan ya taso mata sai ta dinga riƙe kanta tana ji yana mata ciwo tamkar ya fashe, wani lokacin kuma ta yi kuka mai yawa daga bisani bacci ya ɗauke ta. Mun bar shi akan iskokai ne. Sadda za ta rasu kuwa, lafiya lau ta haifeki sai bayan ma har ƙanwar Dada, Inna ta mata wanka ta shirya ta tsaf kawai aka shiga aka ga fuskarta da dukkan jikinta ya yi baƙiƙirin kamar wacce aka ƙona. Aka tattaɓa aka ji babu rai, gaba daya lokaci guda ta komaɗe ta koma tamkar babu jini a jikinta."

Humaira da tun soma labarin take kuka sosai ga wani irin fargaba da ya shigeta da kuma tausayin Mahaifiyarta ta ce.

"Kawu kenan nima idan na haihu zan mutu ne irin yanda Mammana ta rasu?"

"Haba Humaira, wa ya ce maki haihuwa mutuwa ce?"

Ta girgiza kai.

"Kawu nima na yi fama da makamancin wannan halayyar na Mamma akan Fadeel. Ni tsana ce na yiwa kowane É—a namiji da zai ce yana sona."

Ya yi shiru yana kallonta da mamaki, ta cigaba da koramasa bayanin duk yanayin da ta tsinci kanta a ciki da ma hayaƙe-hayaƙen da Mami ke yi mata don taimakonta. Sai wani tunani ya zo masa, tabbas Fatima ta ce itama a lokacin Mami ta taimaka mata da hayaƙi wanda nan da nan ta ke jin kanta na juyawa bacci mai nauyi ya dauketa kuma idan ta farka muddin ba Abban ta gani ba to fa tsanar ba ta ƙara dawowa. Ya tuna har hayaƙin ta ba su akan su cigaba da yi mata.

"Ya aka yi kika daina jin tsanar?"

Ya yi mata tambayar cikin sauri. Nan ta kwararo masa bayani, ita dai tun maida hankali sosai da ta yi ga ibada shikenan kuma sai komai ya sauya. Ta ba shi labarin abin da ke damunta wato tsanar Fadeel din da Mami ta yi. Hatta da farkon zuwan Fadeel din gidan wanda Tasleem ta yi zaton wajenta ya zo ta shirya sai da ta ba shi labari. Kawu ya yi shiru yana sauraronta cikin wata irin fargaba da tunani. Kada dai a baya sun tafka kuskuren yarda da Maryam? Ya tuna tabbas Fatima mai yawan ibada da nafilfilu tun sadda ta dawo gida Nijar suka lura gaba daya ta bar yin ibadunta yanda ya kamata. Hatta da sallah sai Dada ta yi magana take tashi ta yi. Idan ma ta idar babu wata doguwar addu'a take miƙewa.

Ya ambaci kalmar Innalillahi zuwa karshenta a zuciya, bai mance ba akwai sadda wani Malami tun lokacin Fatiman ya ce asiri ne aka yi mata kuma da sanya hannun abokiyar zamanta amma sai suka yi biris suka ji haushi suka ƙaryata shi, a tunaninsu ta ya ya za'ayi matar da take zaune da su da zuciya daya ta aikata wani mummunan abu ga Fatiman?

Jikinsa sai ya yi mugun la'asar.

"Kawu akwai wani abu ne naji ka yi shiru?"

Sai ya yi mata murmushin yaƙe.

"Babu komai Humaira, maza je ki kwanta dare ya yi kinga gobe sammako za ku yi."

Ya fadi hakan ne saboda tare za ta wuce da su Hajjo sai budurwar ɗiyarsa sa'ar Humairar, wato Safina. Sauran masu zuwa ɗiyoyin Inna ƙanwar Dada sai ana bai fi sauran kwana biyu biki ba za su taho da Kawun.
Chapter 84 · 0% Book details