Sashe 86
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Tana fadin haka ta miƙe, an zo daidai wajen da Nusy take so, tana ganin shigar Ummita kicin ta yi saurin miƙewa ta bude net din Ahmad ta daukeshi. Ta ɗago suka yi ido hudu da Waleed da ya shigo daga bangaren Anna rike da ball a hannunsa. Ya gaida ta don bai mance sadda Ummita ta yi baƙuwa ba ya ƙi gaishe ta Antinsa Humaira ta yi mishi tsawa. Ta amsa tana dan wayancewa da jijjiga Ahmad kai kace kuka ne yake yi. Waleed kuwa dama ruwa ya fito sha sai kawai a guje ya yi kicin yana wasanninsa na yara. Ta sauke ajiyar zuciya da sauri ta ɗaga zumɓulelan hijabinta ta sanya Ahmad a ciki ta rufe, ta kama hanya ta fice bayan ta sauke nikaf din ya rufe fuskarta.
Har ta fice daga farfajiyar gidan, Allah ya taimaka Maigadi ya ɗan mike wannan ya sa ta ƙara ɗaga kafafunta ta fice a gate din.
Daidai lokacin motar su Humaira ta tsaya suka fito, idanunta akan matar dake ta baza sauri ga kukan jariri na tashi cikin hijabinta. Kafin ta yi wani tunanin sai ga Ummita a haukace ta banko kyauren gate din ta fito.
"Ahmad! Wayyo jama'a ku taimakamin É—ana!!"
Jin haka ai sai wasu samari da ma ita kanta Humaira dake tsaye suka nufi matar a guje, daidai sadda Wizzy ya yo gaba da zummar kawai ta bude motar ta shiga daga ta iso, sai dai ina, wata irin raruma da wani ya kai mata sai ga ta nan yiff a ƙasa, yaro kuwa ya ji buguwa ya fasa ihun da ya fi kukan da yake yi a baya. Da rawar jiki kuma a haukace Ummita ta hau ɗage hijabinta sai ga Ahmad, Wizzy kuwa tuni ya yi wata muguwar ribas ya bar wurin a miliyan, duk iyaka kokarinsu na ganin sun damƙeshi abin ya ci tura. Nusy dai ta zo hannu tana kuma ji da gani wanda ta aikata dominsa ya juya ya bar wurin.
Nan da nan Ummita ta damƙe Ahmad tana kuka har lokacin jikinta na kakkarwa. Samarin nan kuwa suka shiga kokarin bugun Nusy wani dattijo ya hana ya bada umarnin a damƙa ta a hannun ƴan sanda.
Ana nan ba a kai ga tafiya da ita ba sai ga motar su Abba ta sanyo kai. Mami tun daga nesa ta hangi cincirindo ai sai da ta ji wani mugun jiri daga zaune yana son kwantar da ita.
"Meke faruwa haka kuma? Waccan ba Mamana ba ce?"
Fadin Abba yana ɗan ƙara ƙurawa wurin idanunsa. Mami dai ta kasa ce masa uffan sai Raihana daga baya ta amsa da su ne har da Ummita. Sai kawai ya ja burki ya tsaya ya fito, Mami dai ta kasa motsi balle ta fito daga motar. Suna fita wayarta ta hau ƙara. Ganin sunan Wizzy sai da ta ji wani guntun fitsari ya kufce mata ya zubo, ta ɗaga ba tare da cewa uffan ba.
"Ke tsohuwar kilaki! Ki saurare ni dakyau! Na rantse maki tunda har aka kama min farin cikin rayuwata sai na salwantar da rayuwarki! Sai na kasheki da hannuna muddin asiri ya tonu! Kuma yanzu na gaji da bibiyar ɗana ta hanyarki! Zan tunkari ita banzar gyatumarsa ta ba ni ɗana ko ta halin ƙaƙa ne! Ke kuma ki saurari abin da zai biyo baya! Ba ki san waye ni ba! Labarina kawai kike ji!"
Yana kai wa nan ya datse kiran, wasu hawaye masu É—umi na bakin ciki ya zubo saman fuskar Mami, ta yi saurin kauda su ta bude murfin mitar ta fito. Duk wannn abu da take yi akan idanun Hajjo wacce tun fitowar su Abba ta lura da Mamin da kuma yanayinta, tana ganin wayar da ta amsa. Mamin na fitowa itama idanunta ya sauka cikin na Hajjon, ta gane fuskarta sarai, matar Kawun Humaira sai ta kauda fuska ta daure ta tamau.
Abba ya dubi Ummita da neman ba'asin yanda lamarin ya faru. Cikin kuka ta labartamasa komai, Futuha tunda ta ji an ambace ta da ma sunan unguwar da take sai ta zaro manyan idanunta waje gami da dafe kirji a mugun firgice. Kafin ma Ummita ta kai aya ta hau rantse rantse.
"Na rantse da Allah karya take yi, ke a ina kika san ni? Wallahi Abba karya ne ni tunda naje wannan unguwar ma ban taba shiga kowane gida ba don ba class dina ba ne su. Wallahi sharri take yimin."
Nusy kuwa dai ba ta tanka ba sai jin ciwon gudun da masoyinta ya yi ya kyale ta a nan, idan wani ya ce mata zai aikata hakan gareta za ta ƙaryata. Mami kuwa tana gefe ta yi gum ba ta ce uffan ba.
Hajjo dai ba ta bar kallonta ba har sai da Abba ya ba su umarnin duk su shige ciki shi zai juya a miƙa Nusy hannun hukuma. Da wannan gaba daya suka yi cikin gidan, Raihana ta rungume Humaira ta fashe da kukan da Humairar ta ba kanta ko don abinda ya kusan faruwa ne. Tun tana rarrashinta har dai kukan ya soma karyar da nata zuciyar. Dama ta lura da irin muguwar ramar da Raihana ta yi. Tasleem ta tsallake su gami da jan tsaki ta shige ciki don yanzu ta koma ainahin dakinsu kuma tsohon gadonta.
Futuha kuwa ɓangaren Anna ta yi don ta kwantar mata da hankali bisa hukuncin da aka yiwa Jannat.
***
A ci da hakuri. Lol.Ta fakaici idanun jama'ar dake falon ta shige ɗakinta ta sanya muƙulli. Waya ta fitar ta dannawa Hajiya Lubna kira. Ƙara uku ana hudu ta ɗaga.
"Lubna ki taimakamin, komai ya lalace."
Tana maganar ne cike da tashin hankali.
"Kwantar da hankali ki sanar da ni a nutse. Meke faruwa ne?"
Nan da nan ta zayyane mata komai ta ƙara da fadin.
"Muddin waccan yarinyar ta buÉ—e baki ta yi wata maganar toh ki sani akwai babbar matsala. Nikam ban san kuma me zan yi ba."
"Wannan ba damuwa ba ce Maryam, yanzu dai abin da nake so ki yi kokarin sanin station din da aka miƙa ta ni kuma zan nemi Alhaji don ya yi magana su sake ta. Ai harka ce ta kuɗi kwantar da hankalinki komai zai tafi daidai."
Ta dan ji sassauci kaÉ—an.
"Shikenan, bari Abban yaran ya shigo. Amma lallai muddin wannan yarinya ta fito zan dauki mummunan mataki akan É—an iskan yaron nan."
"Ko kefa, ki kwantar da hankalinki komai zai tafi yanda muke so. Ai ko ba ko faÉ—a ba dole Wizzy ya ci ubansa. Ya batun can kuma na baya, kin gano wanda ya sanar da Æ´an sanda? Na fadamaki Maryam koda yaranki kar ki sake ki aminta da su."
Wannan ya tunasar da Mami tashin hankalin da ke gabanta.
"Uhm, bari kawai Lubna. Ai yanzu an yanka ta tashi domin babu wani abu cikin sirrina da Æ´ar banzar nan Tasleem ba ta ji daga bakin Futuha ba wai har ni ta ke yiwa barazana akan maganar? Wancan batu kuwa har gobe na kasa fahimtar komai, karshe na zargi Abbansu ko shi ya sanar toh idan haka ne kuma meyasa har yanzu bai dau mataki ba? Nidai na ga y sauyamin, babu hira da ni balle a sakarmin fuska."
"Toh kuwa lallai ki zauna ku yi magana da shi sosai ki fashe da kukan kissa ki nuna sauyin nan da ya yi maki sam bai maki dadi koda dai duka wadannan ba sai na koyamaki ba ke dinma Malamata ce a wannan fannin. Yaranki ko zan yi waya da Babandi mu sanya a ƙulle musu baki ta yanda babu inda maganar za ta ƙara fita."
Sanin da Mami tayi Anna ba matsala ba ce ya sanya ba ta ma kawo ta a rai ba, ita idan ta sani ba wani abun bane. Tun kuma safiyar yau din sai yanzu ta yi wani murmushin da har zuciyarta ta ji daÉ—in wannan zantuka na aminiyarta.
"Ina yinki sosai Aminiya, Allah ya kara doraki kan Alhaji da maƙiyanki."
Suka yi dariya, nan kuma suka koma batun Jannat wanda tuni ya baza gari, Hajiya Lubna ta jajanta mata da tambayar yanda za su yi da batun kudaden. Ta taɓe baki.
"Motarta dai ta ce a siyar sai sarƙoƙinta da mijinta zai taho da su. Ya ce dai babu hannunsa a ciki don haka ko sisin kwabo nasa ba zai yi kuka ba."
"Shegen sama, shiyasani, ko me ake ciki dai sai ta fito. Sai kuma ta kiyayi gaba tunda yanzu idanun duniya duk a kanta suke."
Mami ta numfasa.
"Atoh, kinga bari naje ga waccan kafaffan mijin nawa ko zan iya tankwara zuciyarsa na gano dalilin sauyamin da ya yi."
Suka yi dariya ransu ƙal kafin su yi sallama.
***
Hajjo ta yi wanka ta fito ta dubi Ummita baki buÉ—e.
"Wai har yanzu ba ki bar wannan kukan ba? To maganin me zai maki?"
"Kema dai kya faÉ—a Tanti, ni wallahi ban ga amfanin kukanki ba. Mu godewa Allah ma tunda ya yi mana maganin komai."
Cewar Humaira dake kokarin kauda nata hawayen, Raihana ko tana zaune shiru ba ta ce musu uffan kwakwalwarta cike da tunani iri iri. Tasleem ba ta dakin suna can bangaren Anna ana maida zance.
"Don Allah ki bar tunanin komai ki godewa Allah. Ai babu babban makami a yanzu irin addu'a kuma Alhamdulillah gashinan ta yi maganin komai."
Da wannan Ummita ta hakura da kukan ta share hawayenta, ita babban tashin hankalinta bai wuce kuma abin da zai ƙara faruwa a gaba ba. Ko ba a fada ba ta san azzalumin mahaifinsa ne ke biɗarsa. Ita kuma idan duniyarnan za ta haɗe babu mai raba ta da Ahmad.
"Wayarki tana ta ƙara tun ɗazu, Yaya Mubarak ne ke kira amma kin ƙi ki ɗaga." Fadin Humaira tana mai miƙa mata wayar, ta sa hannu ta karɓa ba ita kuwa ta faɗa bandakin don gyara nata jikin.