← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 80 OF 101

Sashe 80

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Kana buƙatar ɗanka, ni kuma ina buƙatar ka cikamin wannan aiki da na sanyaka ya kasance na ƙarshe."

Ya yi wata muguwar dariya yana hangen motar Abba da aka buɗewa ƙyaure ta fito.

"Ai ki sha kuruminki Hajjaju, a yau babu su babu kwanan duniya."

Ta jinjina kai tana murmushin mugunta.

"Dakyau! Sai na samu kyakkyawan labari."

Daga haka ta katse kiran, Raihana dake yunƙurin shigowa ta ja baya tana mai riƙe kirjinta da ya tsananta bugu, kalmar innalillahi shi ta shiga ambato domin kunnuwanta sun kasa gasƙata abin da ta ji na fita a bakin Mami. A cikin sakanni kadan ta dawo hayyacinta, da wani irin azama da gudu ta bar wurin zuwa dakinsu hannunta har kakkarwa yake yi wajen danna waya. Ummita na tambayarta ko lafiya sai dai ina! Babu baka sai kunni. Wayar Abba ta kira, ringing biyu ya ɗaga da sallama. Yana tafe tana tuƙi lokacin har ya fita zuwa babban titi.

"Ab..ba..ba.."

"Lafiya Raihana? Meyafaru?"

"Abba za a kashemin ku, ka tsaya ka juyo gida."

Madadin ta ji razani a muryar Abban sai ta ji kamar ko a jikinsa.

"Kar ki damu Raihana, babu mai tsallakewa kaddararsa. Amma ki sani, ina da labarin da kika tsinta ko kuma kika ji a yanzu tun a daren jiya ya risƙi kunnuwana. Na sanar da D.P.O tun a daren jiya ya kuma bani shawarar da ta dace. Ina tare da rakiyarsu. Kin ji ko?"

Humaira dake gefe ta kasa gane zantukan da Abba ke yi, kirjinta sai duka yake. Abba kuwa bai jira cewar Raihana ba ya katse kiran. Tun daren jiya ya tsinci wayarbda Mami ke yi da wani inda take ba shi umarnin kashe shi da Humaira gaba daya. Har gari ya waye ya kasa tufka da warwara, ga mamaki mai tsanani da ya kewaye zuciyarsa. Ya ka sa gasƙata cewa Maryam ce da wannan yunƙurin.

***
Can ɓangaren Wizzy kuwa, yana tafe a bayan su Abba sannu da sannu don ya cimma su a inda ya gama dukkan wani tanadi da shiri, har a lokacin duhun asubahi bai gama washewa ba. Kallon da zai yi ta mirrow ya hangi motar dake biye da shi a baya, ganin da ya yi duk inda su Abba suka kurɗa a mota shima ya kurɗa ana biye da su ya sanya shi buga sitiyari, ya tabbata ko wace motar ce ba zai wuce na masu tsaro ba, zarginsa bai gama tabbata ba sai da ya ga yana shan wata wawuyar U turn an bude gilashi an bishi da harbi sai da aka fasa gilashin motarsa ta baya.

***
Mami ta fito afujajan daga bandaki daure da zani jiki duk kumfa da azama ta nufi wayarta dake faman ƙara, ganin Wizzy ya sanya ta murmusa don ta san haƙanta ya cimma ruwa. Sai dai me? Wani wawan ashariya ya jefa mata.

"Kin janyo an kusa kashe ni a madadin na kashe?! A gidan uban wa Æ´an sanda suka sami labarin nan?"

"Me kake nufi? Ban fahimta ba?" Ta jefa masa tambayar a rikice, ya yi mata bayani yanda za ta gane. Ya kara da fadin.

"Ke Madam, na baki nan da gobe ki gaggauta kawomin ajiyata idan kuwa ki ka yi wasa da hankalina zan zo har cikin gidan na ga uban da zai hana ni É—aukarsa! Useless kawai!!"

Daga haka ya katse mata wayar, Mami kuwa ai sai ta ji kafafunta sun dauki rawa, toh waye ya san da zancen da har maganar ta isa kunnuwan ƴan sanda? Ta ya ya hakan ta kasance? Duk iyaka tunani da zarginta ta kasa fahimta, a iyaka saninta sadda take waya a falon Abba yana dakinsa yana bacci, koda ta kammala ta shiga yanda ta bar shi hakan ta tarar da shi. Toh waye wannan da ya ji sirrinta? Sai ta zaɓi shigewa banɗakin don ta ƙarasa wanke jiki a gaggauce ta je ta duba mutanen gidan ko za ta samu wata shaidar.

***

Fadeel ya ƙurawa hoton da Ridwan ya aikomasa idanu, hoto ne na wacce ake zargi da yin ɓatanci ga Ummita da Humaira, kamar ya san fuskarnan sai dai ya kasa tuna inda ya santa. Sai ya zaɓi buɗe ɗayan hoton na bayanin da Ridwan ya turo masa. Sunan ya sanya shi miƙewa tsaye babu shiri. JANNAT MOHAMMAD AGADEZ.

Tabbas idan idanunsa ba su gane mishi ƙarya ba, ita ce dai ƙanwar Mami daya taɓa gani a gidan su Humaira har ta ke jajanta masa lamarin ɓatan su Humaira. Kai ya sha ganinta ma ba sau daya ba ba biyu ba. Wannan shi ne ana zaton wuta a maƙera...*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

"Abba lafiya?" Tambayar da Humaira ta yi mishi hankali tashe jin ƙarar bindiga ga kuma juyin da motar dake bayansu tayi babu shiri.
"Kwantar da hankalinki. Babu komai."

Yana fadin hakan ya gangara gefen titi ya tsaya, motar su D.P.O su dinma fakawar suka yi don sun tabbatar ba za su samu damar cafke mutumin ba.

"Ina zuwa." Abin da Abban ya ce kenan kafin ya bude motar ya fita. Humaira dai har wata zufa ke karyowa a goshinta, kirjinta kuwa bugu yake yi ba ƙaƙƙautawa, babu abin da ya faɗo ranta sai waɗancan mugayen masu garkuwar da suka kama su. Waigen Abba kawai take yi tsaye da wanda ta tabbatar ɗan sanda ne don ta gan shi ba sau ɗaya ba kuma ba biyu ba a gidannasu duk da cewar bai sanya kakin aikinsu ba. Hakanan sauran mutane biyar da ke tare da shi babu kayan aiki a jikinsu.

D.P.O Alhussain ya dubi Abba dakyau.

"Kar ka damu Alhaji, in sha Allahu zai zo hannu. Mun kwafi lambar motar zamu tsaurara bincike ta yadda komai za ya bayyana a zahiri. Amma Alhaji a shawarce ina so ka ɓoye batun kawo maku harin nan da aka yi koda kuwa ga iyalinka ne sannan abin da ka fito da niyyar yi kada a fasa shi yin hakan zai bada wata ƙofar da za a ƙara yin wani shirin nan gaba. Zamu yi bincike sosai har mu gano waye."

Abba ya jinjina kai har a sannan cike yake da ɗumbin mamakin Maryam wanda ko a mafarki ya ga za ya aikata makamancin hakan zai ƙaryata a yayin da ya farka. Dakyar ya daurewa zuciyarsa suka yi sallama da D.P.O sannan ya koma ga motarsa ya shiga. Murmushin ƙarfin hali ya sakarwa Humaira wacce wayarta ke ta ƙarar shigowar kira daga Fadeel amma tsabar ruɗani ya sanya ba ta ko fiddo ta a jaka ba ballantana ta kai ga ɗagawa.

"Abba mu koma gida don Allah. Na fasa tafiyar."

Kallonta ya yi, sosai sai ta ba shi tausayi, ko ya za ta yi idan ta ji abin da ke faruwa ko kuma ya yi nufin afkuwa garesu kuma daga wacce suka yi amannar har abada ba za ta taɓa cutar da su ba? Sai ya girgiza mata kai cikin murmushi na ƙarfin hali ya amsa.

"Aa Mamana, babu inda za mu juya. Muje na sanyaki a mota, kada ki damu nasan direban kamar yanda na faɗamaki ɗa ne ga tsohon Maigadin ɗan uwana. Yana da amana, na kuma sani sai dai abin da Allah ya riga da ƙaddarawa zai afku toh wannan babu wani mahaluƙin da ya isa ya tsallake. Ki kwantar da hankalinki in sha Allahu lafiya kalau za ki je ki dawo kinji ko?"

Da kalaman Abba masu ƙarfafa gwuiwa kuma lokaci guda masu karya zuciya ta ɗan samu sassauci, ko ba komai ya tunasar da ita abin da ruɗani ya so ya mantar, wato ambaton Allah. Abba kuwa tuƙi kawai yake yi amma gaba ɗaya yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa mai ɗumbin yawa. Humaira dai hankalinta ya rabu kaso barkatai, abin da ya faru yanzu da kuma yanayin Abba sai ko kirjinta dake faman bugu tun faruwar al'amarin.

Abba kuwa ya damƙa ta a hannu na amanan, Rabe. Mazaunin gaba ya zaɓar mata ita ɗaya yadda ba za ta takura ba, duk kuma yadda ya so Raben ya karɓi kudin motar ƙi ya yi saboda karamci da kuma albarkacin Marigayin da ma shi kansa Abban wanda zai wahala su kai mishi wani kuka nasu ya ƙi yi ba idan da halin yin.

Sosai Humaira ta yi kuka da suke sallama da Abban domin sai da ta ji tamkar kada su rabu. Sai dakyar Abba ya samu ta nutsu ya yi mata Æ´ar nasiha har da zolaya kafin ta saki ranta.

Bayan tafiyar Abban ta fiddo wayarta don ta kira su Raihana sai ta tarar da missedcalls har goma sha, wasu daga Raihanar wasu kuwa Fadeel ne. Kafin ta kai ga wani yunkurin sai ga Fadeel ya ƙara kira. Tana ɗagawa da sallama ya rufe ta da faɗa.
"Meyasa Boddo! Meyasa za ki tsoratar da ni wai?! Raihana ta kirani a ruÉ—e ko na yi waya da ke nace aa, mun gwada kiran wayoyin Abba a kashe. Ina kike yanzu ganinan a hanya."

Ta tuna dagaske wayar Abban a kashe take tun amsa wayar Raihana da ya yi tana ganin sadda ya kashe ta gaba daya. Ko kusa faÉ—an Fadeel din bai yi mata zafi ba, ta sani damuwa da lamarinta ne ya yi silar hakan.

"Ka yi hakuri, wayar tana cikin jaka, ina tasha har na shiga abin hawa."

"No ki jira, ni zan zo na kaiki."

Cikin sauri ta girgiza kai tamkar yana gabanta.

"Aa wallahi, ka yi hakuri dai tunda har Abba ya san direban kuma sun gama magana."

"Wace tashar ce?" Abin da ya nemi sani kenan kawai, ta faɗamasa sunanta daga nan ya katse kiran sai lokacin ne kuma ta samu damar kiran Raihana. Jin muryar Raihanar a shaƙe ya sanya ta tabbatar da ta san komai.

"Raiha, kiyi hakuri wayar tana jaka."

"Babu komai, Abba ina ta kiran wayarsa a kashe. Lafiya ku ke?"

Ta yi tambayar cikin kokarin kwantar da murya da ɓoye damuwa bisa shawarar Ummita.

"Ba mu jima da rabuwa ba, ya juyo ya taho gida."

"Toh, Allah ya tsare ya kiyaye hanya. Zamu yi kewarki ko ince har mun fara."

Ta dan yi murmushin ƙarfin hali.

"Nima haka Raiha, a gaidamin Ummita da Ahmad. A sanya mu cikin addu'a."
Chapter 80 · 0% Book details