Sashe 14
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Humaira ta karasa, ita ban da haushin Raihana da ta ji, har da wani irin bakin ciki da tsanar saurayin da Raihanan ta yi waya da shi ta ji. Ta yarda ba su ga maciji da yan uwanta, amma fa tana kaunarsu kuma tana ji a jikinta sai inda karfinta ya kare matukar ta ga É—ayansu zai cutu. Don haka tana zuwa saitin Raihana ta fizgo hannunta suka kalli juna, Raihana har sai da ta yi taga-taga za ta fadi kafin ta warce hannunta a tsorace, da karfi ta ce.
"Ke kuma Malama wai mene haka? Me na yi maki za ki nunamin hauka?"
Ta fadi ne cike da karfin hali domin a tsorace take, tana gudun ace aljanun Humairar ce suka tashi. Humaira wacce idanunta har sun rine tsabar bacin rai ta kalleta sosai.
"Raihana kina da hankali kuwa? Kin san me kike shirin aikatawa kanki? Æangare masu muhimmanci da girma a jikinki wani jakin banza ya ke so ki tura masa? Kina hauka ne? Wannan saurayi ne da za ki kula? Toh wallahi muddin kika yarda kika aikamasa kin gama cutar da kanki har abada, balle kuma akai ga ya nemi ku hadu da shi a waje. Ina iliminki ya tafi? So ba hauka ba ne ki bude idanuwanki ki fidda baragurbi cikin rayuwarki."
Raihana da tun da ta fahimci dagasken Humaira ta ji dukkan hirarsu sai ta hau borin kunya ga zufa na yankowa saman goshinta har yana jiƙa sumar dake kwance a wurin.
"Me kike nufi? Ni ba ni da hankali ne da zan tura masa? Ko kin dauka shashasha ce ni? Toh ni nasan yanda nake tafiyar da ire-irensu don haka ki rabu da ni. Wannan rayuwata ce. Zan gudanar da ita ne yanda na so. Bai shafeki ba."
Humaira ta yi shiru, can ta nisa za ta kara magana wayar Raihanan ya hau kara, aikuwa da azama ta nufi wayar har tana ture Raihana. ÆŠagawa ta yi ta sa a kunne, Raihana na son dakatar da ita amma tana tsoron kar ta sha duka a hannunta.
"Sweetheart na ji shiru, muna waya..."
"Ba ita ba ce, wannan yayarta ce. Zan kuma yi maka gargadi da babbar murya. Wallahi wallahi ka kara gangancin neman yar uwata da tura maka wani hoto na sassan jikinta sai na nunamaka ba kowace mace ake taɓawa ba a sha ba. Sai ka raina kanka. Banza dan akuya kawai! Tirr da matasa irinku wadanda ba su ajiye komai a cikinsu ba sai tsabar iskanci da baɗala. Mu zuba ni da kai mafashi ya fasa!"
Ba ta saurari me zai ce ba ta datse kiran ta wurgawa Raihana wayar tana jifanta da muguwar harara, Raihana dai kasancewar ta yi amannar wannan jinnun Humairar ne ke magana ba ita ba, ta kasa kataɓus sai rawar jiki tana ji kamar ta saki fitsari a gefe guda tana jin bacin rai da tsanar shiga hanci da kudundunen da take mata amma ba dama ta yi magana, ta kuma sa a rai za ta yi duk yadda za ta iya ta ga ta ba shi hakuri kar ya kai zancen Humaira zuci.
"Idan kin kammala wayar ashararancin sai ki yi sauri ki kammala aikin Mami na jira. Shashasha da ba ta san ciwon kanta ba."
Daga haka Humaira ta ja tsaki ta fice cikin zafin rai. Wayar Raihana na ta ƙara amma ta kasa ɗagawa don gani take yi da zarar ta ɗaga aljanun Humaira za su isar mata da saƙo ta kuma dawowa, wannan karon kam ta sani lugudar ta za ta yi mata. Hawaye na zubomata tana ci gaba da gyaran dakin, hawayen na bakin cikin abin da Humaira ta yi mata ne, tun da take samari a duniya ba ta taɓa yin wanda har a zuciya ta ji tana mishi son aure ba irin Musaddam, yanzu ga shi nan ta ɓata mata shirinta. Tana mishi so da zuciya daya wanda take jin ko mene ne za ta iya yi a kansa. Don haka a gaggauce ta share dakin ta fice zuwa bangaren Anna domin ta samu damar ba shi hakuri sosai.
Ai kuwa duk kalar hakuri da karyar taɓin hankalin da ta dorawa Humaira duk domin ya aminta da ita ya kasa, cewa ya yi shi din son da take mishi bai je ko'ina ba tunda har za ta bari wani ya ji sirrinsu. Raihana kamar ta mutu don bakin ciki, ta tsinewa Humaira ya fi a ƙirga.
Ita kuwa Humaira umarnin Mami ta cika ta sanya turaren wuta a dakin ta fice nasu dakin. Koda Ummita ta nemi sanin abin da ya jefa ta cikin ƙunci, cewa ta yi babu komai. Har ta yi wanka ta shirya ba ta cikin walwala.
Misalin karfe takwas da mintoci Mubarak ya iso gidan. Su Muhsin suka cika gidan da Oyoyo, Tasleem su ma duk yanda su ke ganin yayannasu da shige musu hanci da kudundune sun yi murna da ganinsa. Humaira na gefe tana murmushi ba ta karasa ba tana karemishi kallo. Shi kam kammaninsa da Abba har ta ɓaci, shima dai ba ya kama da Mami, sai ko baƙi da laushin gashi irin na yan uwansa da ya dauko. Kansa cike taf da suma ya tara. Bayan ya zauna ganin Ummita ta karasa ta gaida shi ya amsa cikin sakin fuska ne ya sa itama karasawa su gaisa. Ya nunata da yatsa ya yi shiru alamar dai so yake ya tuno wani abin. Can kuwa ya ce.
"Humaira, right?"
Ta dai fahimci so yake ya tabbatar ko haka sunan ya ke sai ta gyada kai. Su Tasleem suka kwashe da dariya, ya tambayi dalili suka amsa da ba komai. Mami ta fito fuskarta cike da fara'a, ganin mahaifiyarsa ya mike tsam ya karasa ya dan rungumo kafaÉ—arta, ta dan tureshi tana murmushi.
"Ba ka girma ko?"
Ya kuwa kara marairaicewa.
"Girma fa kika ce Mami, yaushe rabonki da ni don Allah?"
Har lokacin murmushin take yi ta amsa.
"Amma ai ana waya da videocall ko?"
Da wasa ya sake ta ya juya.
"Shikenan bari na koma inda na fito tunda kin ƙoshi da ganina."
Da sauri ta riƙo rigarsa har duka falon aka dara. Ya ja hannunta suka nufi bangaren Abba su na hira.
Abba ya yi murna da ganin ɗan nasa, ya kasa rufe baki. Nan suka hau taɓa hira karshe kuma Abban ya ce ya je ya kimtsa ya ci abinci tukunna. Da wannan ya mike ya fita, daga uwa har uban suka zuba mishi ido cike da kauna kowannensu kuma da abin da yake ayyanawa a ƙasan rai.
***
Zaune yake a babban falon dake cikin Airport din Abuja, ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa mai cike da gargasa ya fi a ƙirga, ya maida duba saman wayarsa yana latsawa. Cikin sa'a kuwa ya ji muryar ma'aikaciyar ya karaɗe wurin inda take umartar fasinjojin da za su je Kano akan su nufi ciki. Ya mike kuwa don dama abin da ya zaunar da shi kenan. Hannunsa ɗaya riƙe da trolley ɗinsa yana ja, tafiya yake da sassarfa. Bayan komai ya kammalu jirginsu ya ɗaga. Isar su keda wuya, ya yiwa abokinnasa IBB GUSAU waya. Kafin ya kai ga magana ya ji saukar muryarsa daga gefe.
"Barka da zuwa."
Juyawa ya yi yana dubanshi da idanunsa dake ɓoye cikin wani arnen baƙin gilashi, sai kuma ya ja guntun tsaki yana ɗan murmushi, lokaci guda ya ba shi hannu suka yi musabaha kafin su rungume juna suna cike da farin ciki. Bayan sun saki juna da mamaki ya ga idanun Ibb sun kaɗa, nan da nan ya daure fuska.
"Ok, hakan na nufin ba ka yi murnar ganina ba kenan na koma inda na fito ko?"
Girgiza kai Ibb ya yi ya sa hannu yana karɓar trolley dinsa yana fadin.
"Hakan ba zai taɓa faruwa ba, in sha Allahu ka dawo kenan. Tafiyar kuma daga ni har Alhaji ba za mu ƙara bari ka yi irinta ba. Shekarun da ka yi sun isa hakanan."
Ya shafi sumar kansa bai ce komai ba ban da baki da ya ɗan taɓe ya yi gaba kai kace ya san inda mazaunin motar amininnasa ya ke. Ibb da murmushi ya mara mishi baya. Suka jera su na gifta filin wurin, Ibb ba gajere ba ne, amma fa duk tsawonsa bai kama ƙafar abokinnasa ba, kusan su biyun duka sai ka rantse ba su ne suka gama yiwa juna murmushi da runguma ba, tafe suke su na kallon hanya kai ka ce ba su san juna ba, duk inda suka gifta sai an bi su da kallo, ƴan matan dake wurin kuwa ji suke inama inama, inama za su yi nasarar samun sa'a a cikinsu ɗaya ya yaba, da sun tabbata masu sa'a. Shi yana sanye da ƙananun kaya yayin da Ibb ke sanye cikin manyan kaya dinkin babbar riga har da hula kai kace wani Ango.
"Ina ka nufa?" Ya yi tambayar fuska a haÉ—e a sadda Ibb ya murza sitiyari ya nufi gate din Airport din, shi ma ba tare da ya kalle shi ba ya amsa.
"Ka fi kowa sanin inda ya dace mu soma manufa. Tushiya masomin dawa."
Girgiza kai ya yi.
"No Ibb, i am not ready for it, muje ka kai ni hotel. Hakan na fi buƙata. Please."
Ba musu Ibb Gusau ya amsa da Alright, ba ya so fadi tashin da ya jima su na yi da Alhaji ya tashi a tutar wofi, ai an yi mai wuyar da suka samu ya dawo garin. Don haka kai tsaye Bristol Hotel ya kai shi ya kama mishi masauki, da wani irin walwala da annuri dauke saman fuskarsa ya fito ya rabu da shi ya kama hanya don ya je ya ba Alhaji kyakkyawan albishir. Lallai ya san da zuwan ɗan nasa, amma bai taɓa kawo wa a rana irin ta yau ba da ake shagalin bikin ƙaninsa mafi soyuwa ba a rai.08