← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 79 OF 101

Sashe 79

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Habawa! Ai wannan bidiyo ba karamin kaɗa ƴan hanjin Tasleem ya yi ba. Kuka da sheshsheka haka ta dinga yi tana kururuwar wallahi Humaira ba ta isa ta auri Fadeel ba. Cikin wannan yanayin Hamza ya risƙeta a ɗaki.

"Tasleem lafiyarki kuwa? Anyi wani abu?" Gaba daya yana tambayar ne kirjinsa na dukan tara-tara, tsoronsa kada dai har wani ya yi masa shigar sauri ya fesa mata labarin aurensa. Dama da niyyar da ya shigo dakin da ita kenan, Hajiyarsa ta ce lallai ya sanarmata kafin wani magulmacin ya fesa mata. Ta fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta miƙe tsaye idanunta gaba daya sun rufe ta hau bambamin faɗa.

"Kai Hamza! Kai ne silar rushewar mafarkaina, ka yi sanadin da na kasa samun cikar burina don haka na rantse maka ba za ka ƙara ɗanɗanar farin ciki daga gareni ba muddin ba ka sauwaƙemin igiyar aurenka ba!"

Hantar cikin Hamza ta kaɗa , ya rasa meyasa yake ɗan shakkar Tasleem a wasu lokutan, ya dai aminta cewa duk inda masifaffen mutum yake ana ɗan shayinsa. Daga kalamanta ya ƙara tabbatar da zarginsa, wato wani munafukin ya kawo mata tsegumi. Zufa ta karyo mishi, ya mike a rude ya hau zuba kamar famfo.

"Kiyi hakuri Tasleem, wallahi auren da zan yi ba don na ci amanarki zan yi shi ba. Ramlat ta jima tana zaman jiran..."

"Dakata Hamza! Dakata! Wai wane yare kake yi? Na kasa gane komai! Yi yaren da zan ji na fahimta sosai! Uban waye zai yi aure sannan wace Ramlat ka ke magana akai?!"

Ta yi maganar cikin fita hayyaci, ko kaɗan ta kasa fahimtar komai. A farko sai da razana ta sanya ta dauke wutar dole, ta ji wani dumm a kunnenta, ta dinga kallon Hamzan tamkar wani sabon halitta a gabanta. Kai tamkar a ranar ne ta soma ganinsa a duniya. Shi kuwa ya rasa me zai ce, ya aminta da cewar dai ya yi katoɓara, wato dai ba batun auren take yi ba. Sai ya sauke ajiyar zuciya.

"Shikenan, abar zancen, meke faruwa ne kika..."

"Anƙi a bar zancen! Wallahi sai an yi shi!!! Waye zai yi aure! Ka fadamin nace!!"

Yanda take maganar cikin ihu da ƙarfi ya sa ɗiyarsu farkawa daga bacci a razane tana kuka, ko kallon inda take Tasleem ba ta yi ba balle ta kai mata agaji, shi ko Hamza da ya yunƙura da nufin zuwa ya ɗauke ta, ta yi sauri ta shiga gabansa ta cakumi wuyan rigarsa har necktie dinsa na zugewa ya fadi a ƙas don shigowarsa kenan ba jimawa daga asibiti, wurin Hajiyarsa kawai ya shiga kafin ya yo nan. Ya sa hannu ya fisge ta ya wancakalar.

"Kina hauka ne Tasleem? Don nace aure shi ne kike yimin wannan borin? Ki tsaya fa ki ji, umarnin Hajiya ne wannan auren kin fi kowa sanin dai ni ba ni da  ra'ayin mata biyu."

Ai kuwa wani tsautsayi za a ce ko suɓutar baki da ya kwashi Tasleem, sai ga ta nan ta narko wata ashariya ta narka ga Hajiyar Hamza, shi kuwa da ya ke yunkurin nufar Bebinsu dake kuka sai ya tsaya cak yana mai jin wani gingirim a kai. Tasleem dai ke zagin uwarsa mahaifiya da ta haifeshi? Da wata wawuyar zuciya ta kwashe shi bai san lokacin da ya nufe ta ba gadan-gadan ya hau jibga, tun tana ihu tana ƙunduma masa ruwan ashar har dai ta rasa bakin magana saboda kumbura mata baki da ya yi har yana fidda jini. Cikin sa'a sai ga wata goggwonsa ta shigo da zummar a gaisa ta ci karo da wannan mummunan abu, dakyar ta samu ya bar jibgar Tasleem. Amma ina da wata zuciyar ta kwashi Hamza sai ga bakinsa na furta kalmar saki ga Tasleem. Ta yi matukar razana don ba ta shiryawa hakan ba bagatatan! Duk irin ban baki da hakurin da Gwaggo ƙanwa ga Hajiyarsa ke bayarwa bai ko saurare ta ba, itama ta ji laifin na Tasleem ya girmama amma ba ta so sam ya kai ga saki ba musamman ma kasancewar a gabanta ne. Sai da ta ji dama ba ta shigo ba.

***
Sai yamma likis Humaira da Raihana suka shigo gidan, wadanda suka yi saura  ba su wuce gida ba su na ganinta aka hau guɗa. Ita kuwa sai ta ɓoye fuskarta a kafadar Raihana suka ƙarasa ɗakin. Kuka sosai take yi, babu abin da ya fado mata a rai irin Ummita, irn hakan ce ta kusa faruwa tsakaninta da Sahabi amma al'amura suka rincaɓe. Koda suka karasa, Ummita ta rungume ta cikin wani irin murna na taya ƴar uwarta farin ciki.

"Toh wai meye abin kuka don Allah?"

Ta furta tana rarrashinta. Raihana ta yi dariya.

"Ke kuwa na murna ne mana."

Ita dai ba ta tanka musu ba, a karshe ma ta shige bandaki bayan ta ajiye ledar dake hannunta don ta kama ruwa.

Wannan daren raba shi ta yi suna hira da Fadeel da ke faman zayyane mata irin kewarta da zai yi ba kadan ba.

"Boddona, ba za ki iya É—aga tafiyar har bayan aurenmu ba sannan muje tare?"

Ta yi murmushi tana dan lumshe idanu domin dagaske ta soma jin bacci, sai hirar da shi ta É—an kawar mata da damuwar maganganun Mami akan matukar ta auri Fadeel toh ta tabbata ta yi asarar ingantacciyar rayuwar farin ciki. Ita kuwa yanda take jin kaunar Fadeel ta amince da duk kalubalen da za ta fuskanta a dalilinsa.

"Kin yi shiru."

Ya furta cikin son jin abin da zai fito daga bakinta.

"Ka yi hakuri, na faÉ—amaka ba jimawa zan yi ba, sati kawai Abba ya É—ibarmin."

Sauke ajiyar zuciya ya yi.

"Shikenan Boddo, amma lallai fa zan yi kewarki."

"Kwana nawa ne zan zama mallakinka?"

"Me kika ce?"

Sai da ya faɗi hakan ne ta ankarar da suɓul da bakan da ta yi. Kawai sai ta rufe ido da tafin hannunta na hagu tana dariya ƙasa-ƙasa, ashe dai za ta iya mayar masa da martanin magana mai dadi? Shi kuwa a bangarensa fasalta irin farin cikin da kalamanta ya jefa shi ciki ba zai yiwu ba, koyaushe shi ne mai amayar da abin da ke ƙasan ransa ita kuwa ko oho sai dai ta bi shi da Hum, um, eh ko aa. Sai hakurin da take yawan ba shi idan ya yi wata ƴar ƙorafin ko ya ya. Haka suka raba dare su na hira a karshe ya dinga magana ya ji shiru sai hucin numfashinta da ke amsa kuwwa ta cikin wayar, anan ne kuma ya fahimci  bacci ya yi awon gaba da ita. Dole hakanan ya hakura shima ya katse kiran.

***
Bisa shawarar Mami, Tasleem ta ƙi zuwa gidan saboda tsoron haɗuwa da Abba sai kawai ta sauka a gida Futuha. Tun zuwanta babu abin da suke zantawa sai lefen Humaira da ya bi ya tsone musu idanu. Futuha ta yi kwafa.

  "Ki rabu da yar iska, yanzu za ta soma yiwa mutane fiffika tana ganin duka ta fi mu. Ni fa wallahi zan so ace yanda kika fito daga gidankin nan ke kika aure Fadeel din ko ba komai mu ga ta tsiya."

Fadin haka ran Tasleem ya É—an yi sanyi. Ta ji ashe Futuhar na kaunarta da alheri ba kamar ya da ta zata ba a baya.

"Hum, bari ke dai yar uwa. Nima dai zan so hakan ta kasance amma Abba kinsan shi zai toshe dukkan wata kafa da mutum zai yi wancakalarsa a rayuwa. Ni wallahi a baya Mami nake zargin ba ta sonmu amma yanda ta hakikance akan ba ta son auren Fadeel da Humaira yasa na ƙaryata zargi. Abba shi ne mugun."

Futuha cikin yanayi na suɓutar baki da kuma dadin zance ta taso.

"Ke! Inji wa? Wallahi toh kf duniyarnan ba mu da masoyiyar da ta wuce Maminmu. Kinsan irin sadaukarwar da ta yi duk don mu samu rayuwa ingantacciya?"

Ba ta jira jin ta bakin Tasleem ba ta shiga ɓaro zance babu ƙaƙƙautawa. Sai da ta ba Tasleem labari kaf na irin abubuwan da Mami ta yi a rayuwa sannan ta yi shiru. Dama zancen ya jima yana cinta a rai, ita ta tsani ka ba ta sirri don sai da ta yi dagaske ta ke iya riƙeshi. Tasleem ta ji zantukan tamkar a mafarki har dai sai da ta ƙara matsawa kusa da Futuha.

"Idan wasa kike yi kinsan Allah bana son irin wannan."

Tsaki Futuha ta ja kafin ta rantsewa Tasleem cewa dagaske ne kuma Mami da bakinta ta faɗa mata. Wani ihun murna mai cike da al'ajabi Tasleem ta yi, tana mai ji a ranta cewa dole ta fesawa Anna da Jannat ko don su bar ganin laifin Mami sannan Anna ta ƙara samun tabbaci akan babu abin da ya sauya daga Maminta. Jin Futuha kawai take yi tana jaddada mata kada ta sanar da kowa komai ta rike sirrin Mami, ita dai ta bi ta da toh, tana kuma da yaƙini akan ai Jannat da Anna masoya ne ga Mamin, lamarin sosai zai yi musu dadi.

***
Washegari tun da asuba Humaira ta yi wankanta tsaf ta shirya cikin wata atamfar super da Mami ta ɗinka mata. Sai da ta kammala shiri tsaf su Ummita na zaune da Raihana cikin jimamin tafiyarta ta bar su, ta karasa ta dauki inda Ahmad ke shimfide ta ta sumbaci goshinsa sannan ta gyara masa lulluɓi. Suka kara yin sallama da su Ummita, daga bisani suka yo mata rakiya. Mami na sashin Abba, Abban yana falon Mami yana jiran Humaira ta fito ya je ya sanya ta a mota. Sai da suka gaisa sannan ya ba ta umarnin su tafi.

"Abba zan yiwa Mami sallama."

Ya girgiza kai.

"Bacci take yi kwa yi a waya."

Ko kadan ba ta so haka ba, tana da tabbacin akwai abin da ke faruwa. Maganar Abba karo na biyu akam ta kama hanya su tafi ya sanya dole ta bi umarninsa ta yi gaba bayan sun kara yin sallama da su Ummita tamkar kada a rabu.

***
Mami dake kallonsu ta windon Abba ta saki labule cikin huci ta furzar. Wayarta ta fiddo ta dannawa Wizzy kira.
Chapter 79 · 0% Book details