← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 78 OF 101

Sashe 78

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Ya yi wata shegiyar dariyar shaƙiyanci.

"Shikenan amma dai yanzu ki je ki daukarmin sabon hoton yarona ki turo na gani. Kar ki turon kala É—aya."

Ta ja guntun tsakin da take da tabbacin ba zai shiga kunnuwansa ba sannan ta amsa da ta ji. Bayan sun ajiye wayar ta soma jin haushin kanta, ko ta yaya za ta shiga yiwa yaron hoto, wannan yawan hoton da take yi har Ummitan kan iya gano wani abin muddin dai ba ta yi da gaske ba. Yarinyar akwai kaifin tunanin. Ta dai yi shahada ta fito zuwa dakin. Ba ta ko dubi Jannat ba da ma wasu baƙin da suka shigo ta nufi wurin Ummita.
Ummita ta tarar ita ɗaya adalilin fitar da Humaira ta yi bisa rakiyar Raihana zuwa kasuwa siyayyar tsarabar da za ta kai Nijar, motar Abba ta kai su. Ganinta sai Ummita ta ɗan saki fuska. Kuka yake ta yi tana tsaye tana faman jijjiga shi ya ƙi yin shiru.

"Ya aka yi me ya same shi haka yake kuka?"

"Nima ban sani ba Mami, tun ɗazu ya ƙi ya yi shiru."

Mami ta sa hannu ta karɓe shi.

"Ina madararsa?"

Kasancewar Abba ya siyo madarar gwangwani biaa shawarar Baba Amina tun a farko don ta ce nonon ba ya isar sa. Ta ƙarasa wajen feeder da ta haɗa madarar ciki saboda zafi sai ta sanya a kofi mai dauke da ruwan sanyi ta bar shi ta miƙawa Mamin haɗe da bif na sanyawa a wuya gudun ɓata jiki. Mamin ta shiga ba shi tana dan murmushin da bai kai zuci ba, can a ƙasan ranta ban da tsinuwa babu abin da take jifan Wizzy da shi. A cewarta duk shi ne ya cuce ta. Ummita ko ta yi shiru kawai amma jikinta ya yi sanyi, hakanan ta ji ba ta aminta da wannan kulawar daga Mami ba, Mamin da ko kallon arziki ba ta fiye bin Ahmad din da shi ba duka saboda ganin da ta yi tamkar ɗanta na soyayya da ita Ummitan. Wannan sabon sauyi da kuma hoton da ta ke dagewa wurin yiwa yaron sai yake ƙulle mata kai. Na farko dai Mamin ko status ba ta taɓa ɗorawa ba na yaron hakanan ba ta ga wani ko wata da Mamin za ta aikawa hoton ba balle har a kai ga ɗauka.

Haka ta yi ta saƙe-saƙen zuci, can dai ta miƙe zuwa bandaki sanadin fitsarin da ya matso ta, koda ta fito hoton dai ta tarar Mamin na ɗaukar Ahmad, tana ganinta kuma sai ta wayance ta hanyar nunamata hoton.

"Kinga wannan ɗa wato ya san Camera, ya yi ƙuri yana kallo kai kace ya san hoton za'a yi."

Ta dan yi ƴar dariyar yaƙe amma ba ta ce uffan ba. Can kuma kamar an mintsili Mamin ta miƙe tsaye sannan ta miƙawa Ummita yaron.

"Maza sanya shi a kafaɗa ya yi gyatsa. Ni bari naje daki naga wadannan ƴan karɓar lefen sun soma cika gida."

Da sauri Ummita ga magantu.

"Mami don Allah kiyi hakuri hakanan ki sanya hannu a auren Humaira."

Ta tamke fuska.

"Humaira ta nunamin ni ban isa da ita ba, ba ni ce uwarta ba. Me kike so kuma na ce mata? Ai shikenan, ni dai idan a tunaninta baƙin ciki nake yi don ba nawa aka aura ba to tabbas ta cutar da ni ta kuma dauki alhakin riƙon da nayi mata a ɗan shekarun nan. Ta je, aure dai ta yi shi ga tanan ga Fadeel din."

Daga haka ta sa kai ta bar dakin. Ummita ta bi bayanta da kallo, sai take ɗan jin kalaman Mamin na shigarta, kodai dagaske akwai wani aibun na Fadeel wanda ba su da masaniya da shi? Haka ta yi ta saƙe-saƙen zuci akan ƴar uwarta da wanda za ta aura, wannan ya yi sanadin da ko zancen hoto ba ta ƙara tunawa ba balle ta yi.

***
"Nifa ina ji a jikina ba wani abin arziki zai samyo wa yarinyar nan ba, ita da ake zargin ma ba cikakkiyar mace ba ce? Ki kwantar da hankalinki ai sun zo kayan su na can sashin Abbanku yanzu za a yo nan da su. Zamu ganewa kwarkwatar idanunmu."

Jannat ke rarrashin Tasleem a waya da wadannan kalaman. Gaba daya ta hargitse wai ita dai Antin ta san yanda za ta yi Hamza ya rabu da ita ta zo ta auri Fadeel.

"Hum, Anti kenan, bana jin a yadda yake mutuwar so da kaunarta zai iya yin karamin lefe."

"Mtsw, ke kam akwai wauta wallahi. Toh an faÉ—amaki shi son daga lefe ake ganewa? Ke dai ki bari na aiwatar da abin da zan yi, koda ta shiga gidan na rantsemaki sai dai ta gaji ta nemi saki."

Haka suka yi ta tufka da warwara akan baiwar Allahr da ba ta ji kuma ba ta gani ba. Guɗar da Jannat ta ji yo daga can falo ana rangaɗawa ne ya sanya ta fitowa daga dakin Anna da ta shige zuwa falon wanda tuni Annan ke zaune itama tana jiran ta sha kallo. Sai dai kuma nan da nan kallo ya kuma sama ganin yanda aka shiga shigo da akwatina daga daya biyu har sai da aka sauke set uku reras na kaya! Toh fa!! Zo ka ga idanun Mami wacce ba da son ranta ba ta fito sai domin Annan da ta yi mata magana kan ko yaya ta danne abin a ke ranta, ga kuma Jannat wacce tsabar bakin ciki da hassada sai da ta ji kwalla sun cicciko a idanunta. Ga Anna kuwa, jikinta har wani irin tsuma yake yi balle kuma a je kan uwa uba Mami wacce ta mike a mugun razane ta dakawa matar dake guɗa wata irin tsawa wanda sai da wuri ya yi tsit aka zubamata idanu.*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Da sauri kuma cikin yare Anna ta yiwa Mami magana. Nan da nan ta saita kanta. Ta juya zancen.
"Ni na fada, yaron nan mugu ne, wannan kayan bai yi kama da na yaron arziki ba. Duka-duka nawa yake da har zai ci ace ya tara wannan uban dukiyar? Toh idan ku idanunku sun rufe ni Maryam babu tsiyarsa da za ta burgeni!"

Wata mai kaudin bakin ta tare ta.

"Haba Hajiya Maryam, babu kyau shaidar abin da ba ki da tabbacinsa. Ni wallahi ban taɓa jin an kushe wannan yaron ba sai daga wajenki."

Mami ta dubi mai magana, wata abokiyar tsokanar Abban ce ana kiranta da Larai.

"Ke Larai! Ki tsaya iyaka matsayinki. Dama irinki mai kwadayin abin duniya mai jiran ƙiris ai babu ta yadda za'a yi Fadeel ya taɓa laifi a wurinki. Inace har da ke ya kai wa ziyara a satin can ya sauke maki buhun shinkafa da mai? Toh bari ki ji na fadamaki, wallahi matukar ina raye ina wannan gidan babu mai aurawa Humaira ɗan yankan kai! Ashe kenan son da nake mata na banza ne matukar ba zan yi mata yaƙin abin da nake da tabbacin gaskiya ne ba. Yadda zan tsayawa Raihana hakanan zan tsaya tsayin daka akan ganin rayuwarta ta inganta."

Jikin da yawa a wurin ya yi sanyi, wasu na tauna maganganun Mami su na shinshino ƙamshin gaskiya a ciki, idan ba gaskiyar ba ne, akan wane dalili ne zai sa yaron da aka ce bai ko haura arba'in ba zai mallaki maƙudan kudaɗen da zai haɗo gagarumin lefe akwati har saiti biyu. Wasu kuwa suka tafi akan zargin ba komai Mami ke gwadawa ba sai abin da ke ranta ƙarara wato hassada da baƙin ciki. Ai tun da take babu wata ɗiyarta da ta more irin wannan miji ga kyau ga kudi uwa uba kuma ƙuruciya.
Baba Amina ce ta tari numfashin Mami gudun kada ta kawo musu abin da ba shi ba don da alama har zatukanta sun samu matsuguni a zuƙatan wasu.

"Kiji tsoron Allah Maman Mubarak (Kamar yanda take kiranta), tun farkon soma munanan kalamai a kan Fadeel da kike yi, sai da Yaya ya sanya aka yi bincike sosai kuma aka tabbatar da komai nashi daidai da wurin aikinsa sai da ya tura aka kara tabbatar da shi din managarcin mutum ne mai kokarin kyautatawa na ƙasa da shi. Don Allah ko mene ne a ranki kada ki kawo mana shi anan, kar ki sanya a zargi abin da ba shi ba. Yadda aka fara komai lafiya a ƙare lafiya."

Maganganun Baba Amina sai suka shafe zargin da wasu suka fara a zuƙatansu, suka kuma haskaka ko mene manufar Mami, wato dai ba komai ba ne face hassada.

Mami za ta ƙara magana cikin azama Jannat ta rike hannunta gami da yi mata raɗa cikin yare a kunne.

"Kar ki sake ki bada kanki a gabansu, za a tafi ana zunÉ—enki. Ki bar komai za mu samu mafitarsa."

Ita kuwa Anna sai ta hau yiwa Mamin faÉ—an gangan, karshe ta goyawa Baba Amina baya, ita dai Baba Amina jinta kawai ta ke yi don ta san Anna ba kaunar Humaira take yi ba. Ta sha jin yanda yanayin mu'amalarsu take a bakin yaranta da kuma Ummita. Amma a yau matar ke cewa wai Humaira ba ta da miji sai Fadeel.

Idanun Mami ba su raina fata ba sai da aka shiga fiddo tsadaddun lesuka da atamfofi har ma da mayafai, komai da komai da ake so a lefe babu ne kawai babu a ciki. Kayayyaki masu mugun tsada dai gashinan a gabanta tana gani kuma ba na kowa ba sai Humaira, yarinyar da ba ta taɓa jin ɓurɓushin kaunarta a ruhi ba. Guɗar Larai da ta cika wajen kusan ma da gayya take yi tana ambaton Allah ya sanya alheri, Humaira ta yi goshi.

Mami fuu ta mike ta bar wajen, duk dauriya irin ta Jannat kasa daurewar ta yi, tun tana yaƙe har fuskarta ta koma ta ɗauru tamau kamar ƙullin goro. Ba don Anna ta dakatar da ita daga tashi cikin yare ba, da tuni itama ta bi sahun Mami. Sai bidiyon dole da ta dinga yi, koda aka kammala gani sai ta tura wa Tasleem da Futuha domin su sha kallo.

***
Chapter 78 · 0% Book details