Sashe 97
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Humaira ko tun da wata abokiyar tsoƙanarta ta sanya hannunta cikin na Fadeel ta yi ɗif ta kasa magana, duk iyakar kokarinta na ganin ta zare amma gogan sai ya tamke su tam a cikin nasa. Nan fa aka shiga hotuna bayan kammala gaishe-gaishe. Fadeel ya matsu ko kallonsa ne Humaira ta yi amma ina, kunya ba ta bar ta ba. Zuciyoyinsu sai wani zillo yake yi na farin ciki.
Wizzy na tsaye daga baya yana ƙarewa gidan kallo da mutanen dake ciki, bai san Mami ba a fuska hakanan ita din ma balle ya yi tunanin za ta gan shi ko kuma shi din ya gan ta. Yana kuma da tabbacin zai wahala wani cikin su Humaira da Ummita su iya gane shi, a ganinsa abu har an shekara zai wahala su gane shi.
"Ke Ummita, yaron nan dai ɗuminki yake son ji." Faɗin Hajjo tana mai miƙo mata shi bayan ta je sun kammala hotuna da su Fadeel an gaisa. Hankalin Wizzy gaba daya ya yi kansu, Ummitan ta ci wani irin kwalliya da blue lace ta yi kyau tsaf. Ahmad din ma shigar ƙananun kaya aka yi masa, ya yi ɓulɓul abinsa. Yana kallonsu cike da wani irin kauna da bai san daga sadda ta faro ba. Ya bi Ummita da kallon sama har ƙasa, ta ƙara zama wata yarinya sharr da ita.
Daidai sadda wani ya karasa kafin Humaira ta kai ga sa hannu ta karɓi Ahmed, ya ce Hajjo ta miƙa masa shi. Wani ƙululun bakin ciki ya tokare a wuyan Wizzy, wannan wane ɗan iskan ne haka? Dama ya kula da irin shishshigin da yake yiwa Ummitan, toh kuwa bai isa shiga tsakaninsa da ɗansa ba. A yau zai raba su da wannan farin ciki ya ɗauke jininsa idan ya so daga baya ko Ummitan ya dawo ya sace. Shi ya ji ma zai iya aurenta su rayu tare.
Ummita ta dubi Ridwan. Ya kashe ta da wani sassanyan murmushi, ta yi ƙasa da kanta. Ganin haka Hajjo da murmushi ta juya ta bar musu wurin tana mai fatan alheri a can ƙasan ranta. Ta tabbatar idan har wannan aure ya tabbata toh shakka babu Ummita ma tana cikin layin masu dace a rayuwa. Tana da labarinsa a bakin su Raihana da Humaira a sadda suke koɗa shi duk don su nemi kafa shi a zuciyarta.
"Ni ake ta yiwa yanga? ÆŠan nawa ma rowar ganinsa ake yimin?"
Duk sadda ya kira Ahmed da É—ansa wani daÉ—i take ji amma ta ke kannewa. Yanzun ma ba ta ce komai ba sai kauda kai gefe.
Ya taka zuwa inda ta mayar da fuskarta. Idanunsa ya kai ga Wizzy, ganin haka Wizzy ya kauda kai da sauri yana kallon wani ɓangaren, shima sai ya ɗan share amma tun sadda aka shigo yake lura da shi, gaba ɗaya zuciyarsa ba ta yarda da shi ba.
"Mama tana tambayar yaushe za ki je ta ganki? Kinsan fa na ce mata sa ranar kawai ya yi saura. Kin amince."
Ya karashe da É—an É—aga gira, ta zaro ido gami da É—an dafe kirjinta.
"Ni da bakina na ce maka na amince?"
Ya É—an bi bakin da kallo yana murmusawa kafin ya maida idanunsa kanta. Ta kauda kai, ta rasa dalilin da idanunsa ke mata wani irin kwarjini.
"Ko ba ki furta ba ai idanunki sun fallasa sirrin dake cikin zuciyarki."
Ta kasa cewa komai sai giftashi da ta yi ta wuce murmushi dauke a fuskarta. Shi dinma bin bayanta da kallo ya yi cikin murmushin har sai da Idris ya ɗan buga kafaɗarsa. Ya basar gami ga miƙa Ahmed ga ƴar yarinya kuma jika ga Baba Amina dake ta faman miƙa hannu wai ya ba ta shi. Ta karɓe shi kuwa ta yi gaba tana masa wasa. Dukkan wannan abu akan idanun Wizzy suka faru. Ya gama shaƙar baƙin cikin wannan soyayyar da Ummita ta samu, ya kuma ji kwarin gwuiwar ganin wata ƴar albarkar ta rage masa aiki ta hanyar karɓar Ahmed da kuma nufar hanyar ƙofa da shi inda ƙawayenta yara suke tsaye ana wasa.
Ya faƙaici idanun jama'ar dake wurin ya yi saurin yin baya. A wannan fakar idanun Ummita idanunta suka kai kansa, har abada ba za ta taɓa mance wannan mummunan fuskar ba duk kuwa da irin shigar manyan kaya na kamala da ya yi ba a can da yake shigar ƙananan kaya, kayan ma na ƴan duniya irinsa. Kirjinta ya hau bugu, ta ga ya juya zai fita, ta kasa sukuni ta bi bayansa, ta kasa magana saboda ta fi buƙatar tantance komai da idanunta kan ta yanke hukuncin ihu za ta yi ko kuwa gudu za ta yi. A yayinda hankalinta ke kan Wizzy, shi ko Ridwan nashi hankalin ya koma kanta ganin ta zo ta tsakiyarsu inda za'a yi hoto ta wuce ba a hayyaci ba. Ya juya da sauri ya bi bayanta daidai sadda Wizzy ya sa hannu ya karɓi Ahmed da yaudararriyar murmushi da ya sakarwa yarinyar gami da fadin ta ba da shi ya ga wannan fine boy din. Daga haka ta ga ya nufi wajen falon da shi yana ɗan yi mishi wasa. Ihun da ke maƙale a fatar bakinta shi ta saki gaba ɗaya iyaka ƙarfinta. Wannan ya ankarar da Wizzy, da wani irin sauri ya zura Ahmed cikin babbar riga ya soma gudu zai fice. Ai cikin wani irin zafin nama Ridwan ya bi shi da sauran mazan dake a wurin. Waɗanda ke waje kuwa suka yi nasarar cafke shi, Ummita kam tuni ta fita hayyacinta kira take "Shi ne! Wallahi shi ne! Ya zo ya ɗaukemin ɗa!"
Humaira da Fadeel da sauran jama'a hankalinsu ya tashi, Fadeel ya riƙe Humaira gam ganin yanda jikinta ya hau wani irin mazara, aka fita gaba daya zuwa farfajiyar gidan inda Ridwan ke riƙe da Wizzy gam! Ahmed ko yana hannun Dawud. Ummita na zuwa ta karɓi Ahmed ta rungume tana ja baya sosai daga Wizzy, kallonsa take yi a mugun tsorace jikinta na ɓari, Anti Maijidda da Hajjo suka riƙe ta sosai. Wizzy kuwa idanunsa sun raina fata, Humaira ta bishi da kallon tsaf. Tabbas shi ne. Ta hau nuna shi da yatsa itama.
"Fadeel wallahi shi ne ya ketawa ƴar uwata haddi! Shi ne baƙin azzalumin da ya cuci rayuwarmu!"
Sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, Fadeel ya rungumeta sosai cikin alamun rarrashi. Nan dai Ridwan ya yi waya ga abokan aikinsa akan su iso da gaggawa.Â
Abba da jama'arsa dake zaune a falonsa na saukar baƙi jin wannan labari suka fito, ya nufi Wizzy ya bishi da maruka hagu da dama.
"Yanda ka shigo hannu da yardar Allah ƙarshenka ya zo. Muje ni da kai shari'a yanzu aka fara. Azzalumi!"
Wizzy dake cika da batsewa yana hura hanci kamar tsohon salansa sanadiyyar marin da ya sha na Abba ya tari Abban da sauri.
"Ka dinga yin jam'u ai Yallaɓai! Azzaluman ai biyu ne ba ɗaya ba! Akwai azzaluma irin matar mai wannan gidan?! Ita ce ta sanya muka aikata wannan mummunan aikin don ta samu ta mallaki dukiyarka!"
Ana ga wata ga wata! Nan fa kallo ya koma sama! Jama'a suka yi caa ana maganganu, kowanne da abin da yake faɗi. Abba kuwa ai sai da ya ji duniyar na juyamasa, yana ji abokan Fadeel suka yi caa a kansa akan ya ƙara shirga wata ƙaryar sai sun fasa bakinsa. Shi kuwa Wizzy ya dinga rantse-rantsensa cewar har da hannun matar Abba. Daidai lokacin motar ta iso aka titsa ƙeyarsa aka tafi. Su Fadeel ma babu jinkiri suka tafi, shi kam a son ransa ya so a ba shi matarsa kawai su fice tare don ya tabbatar wannan lamarin sai ta dinga kuka a kansa. Ibb ne ya nunamasa ba a haka tunda dai su na cikin rashin nutsuwa ya ƙyale su samu hankula su kwanta.
Magana dai har yamma ana ta yi, kallo sai ya koma sama. Madadin hirar da ta shafi biki da kuma sabga ta mata sai gulmar Mami. Da yawa sun cika da al'ajabi sun kuma yi rantsuwa kan cewar za ta aikata. Wasu kuwa sun ce sam! Mami ta riƙi yaran da zuciya daya, kawai dai akan auren Humaira ne aka yi yaƙi da ita don a fili ta nuna ba ta ra'ayin Fadeel, zai kuma iya zamtowa akwai dalilinta. Anti Maijidda kuwa kuka sosai ta shiga yi tana hamdala da Allah ya nunamata ranar da kusan kowa ya gane wace ce Mami.
***
Wai ina Mamin?
Tun shigowar su Fadeel tana ɗaki, ta yi wanka sai dai ta kasa fiddo kaya balle ta sanya. Baƙin cikin wannan gidan arzikin da Humaira za ta shiga shi ya tsaya a ƙoƙon ranta, ƙarshe ma kuka ta shiga yi. Abin mamaki, kuka na baƙin ciki da jin inama ta mutu kafin wannan rana. Wai ɗiyar Fatima ce kishiyarta, ita ce dai ta samu wannan ɗaukaka ta ko'ina. Ita kuwa nata yaran daga bazawara mai ƙananun shekaru sai ko wata can da aurenta ke gantali, su kansu mazan sun ƙare karatunsu babu aiki. Kasuwar ma Abba ya dakatar da su daga zuwa saboda irin ɓarnar da ya ce suna yi masa. Yassar da Abban yace zai samar masa koyarwa ya rantse ba zai yi ba, shi kam Allah ya kiyaye a ganshi yana koyarwa. Wannan ya hasala Abban har ya fita hanyarsa ya ce ya yi duk yanda ya so.