← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 70 OF 101

Sashe 70

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Sai kuma ta yi ɗif jin hasalalliyar zuciyarta za ta sa ta yi katoɓara. Ummita kuwa ta fahimci tsaf abin da Mamin ke ƙoƙarin faɗi, sai ta shiga kokwanto akan anya dagaske Mamin da kanta ke wannan batun ko kuwa dai, don haka ta ɗago ta dube ta ita kuma ta kauda kai karshe ma  ta miƙe ta bar falon.  Shakka babu ita ɗin ce da kanta, maganar ta tsayawa Ummita a rai. Bazawara fa take kokarin kiranta? Mami da kanta? Sai kawai ta ji wasu sabbin hawayen sun kwaranyo. Zuciyarta na ce mata eh ga kuma zahiri na idanunta na kara tabbatarmata da haka ɗin ne amma wani ɓangaren na zuciyar na kokarin kare Mamin da tunanin ajizanci na kowane ɗan adam, mai yiwuwa itama suɓutar baki ne saboda ɓacin rai ba hakan ta so faɗi ba. Wannan dalilin ya sanya ta share hawayenta ta tattara kur'anan su Muhsin ta maida kowanne a jakarsa sannan ta kwashi jakunkuna zuwa ɗakinsu.

***
Ƙaramin gida ne wanda ya ji fenti daga waje ya sha kyau, ciki kuwa kana shiga, babu batun farfajiyar gidan saboda wani tsukakken wuri ne sai famfo a gefe ga bishiyu ƙananu an mishi ado da su. Daga ciki kuwa kai tsaye falo za ka faɗa, ba shi da girman da zai cinye manyan kujerun Futuha sai raba su aka yi wasu aka kai safayar ɗaki falle guda dake  a ƴar tsakar gidan. Ɗaki ɗaya ne a ciki sai store da kicin ɗinta ƙarami wanda hatta da freezer dinta bai shiga ba sai a zagayen baya gefen kicin aka sanya shi. Hakanan babu matsugunin kayayyaki da yawa na wuta na amfani kicin dole hakanan suka cuccusa su da taimakon ma'aikata tsohon gidan da suka kawo kaya. Gado dai ya shiga ɗaki amma fa ya cinye kusan rabin ɗakin. Raihana da Humaira sai kallon kallo da mamaki, ita dai Humaira ba ta tanka ba sai Raihanan da ke ta jajen lamarin da hango rikicin da zai faru idan Futuha ta ga gidan da take ta yiwa rawar ƙafa har Tiktok ta yi na bidiyo tana a tayata da addua za ta tare a sabon gidan da mijinta ya gina mata, har da alƙawarin za ta yiwa followers dinta bidiyon gida kamar yanda suka buƙata su na ɗokin su gani.

Ana kammala jeran komai wadanda ba su samu wuri ba aka sanya su a store, bayan fitar masu kawo kaya Humaira ta dubi Raihana.

"Nifa gaskiya binsu zan yi a sauke ni a gida ba zan zauna har ta zo ba."

Ganin haka wuf Raihana ta dauki mayafinta.

"Balle kuma ni, ta ina zan zauna a yi borin nan a gabana? Wallahi ba da ni ba. Mu ba su muƙulli idan ya so su yi mata waya ta faɗi inda za su kai mata ko kuma ai za ta koma tsohon gidan ta yiwa Uwargidanta sallama, kinga sai ta karɓa a can."

Murmushi Humaira ta yi, har ta tausayawa Futuha ganin yanda ta ke rawar ƙafar shiga gidan da a yanzu ko na Tasleem ya fi shi tsari da wadatuwa. Tana ji koda suka kama hanyar tafiya gida bayan sun bada muƙulli sai da ta ƙara kiran Raihana ta gama masifar dalilin da yasa ba su jirata a gidan ba salon ace ta shiga babu ɗan rakiya kafin ta hau tambayar yanda girman parking space din gidan yake wai ko zai iya cin mota biyu. Raihana ta amsa da ita dai idan ta dawo ta shiga ta ganewa idanunta daga hakanta kashe wayar baki daya. Duk yanda Humaira ta kai ga son riƙe dariyarta sai da ta kufce mata, Raihana ta taya ta.

"Allah kuwa ta ban tausayi kuma ta ban dariya idan na tuna yanda take ta wani jijji da kai da É—ora bidiyo wai a taya ta murnar tariya a sabon gidanta."

Humaira cikin faÉ—aÉ—É—an murmushi ta amsa.

"Kin ga illar son a sanin da ta ke yi a idanun duniya kenan, yanzu da ace asirinta a rufe yake ba ta sanar da kowa ba shikenan babu mai ji balle gani. Ba ki ji ta ce washegari za ta yi walimar tariya ba har fa abinci kina dai ji a gabanmu ta ba da odarsa tana cewa akwai sabuwar mai abincin da ake yayinta a bukukuwa."

Takaici sosai ya kama Raihana.

"Ai shikenan, sai ta shirya naÉ—e tabarmar kunya da hauka."

Haka suka yi ta hirarsu har suka ɓullo gidan Tasleem inda anan za su wuce tare da Jannat wacce ta maida gidan wajen yininta. Wannan karon ba ta zo da yaranta ba saboda makaranta ta bar su can hannun kanwar babansu dake aure a Misra. Gargadin Abba ne bai aminta su kara shiga ɗan sahu ba idan har ba wasu kwakkwaran dalilai ba ne da ya yi zafin da sai an nema an shiga. Wannan ya sa suka yanke hakuri da zaman jiran Jannat ta gama ta wuce da su a motarta gudun kar su je Abban ya yi musu faɗa. Su kansu tsoron shigar suke yi yanzu musamman Humaira.

Sun zo dab da gidan Tasleem har su na hangowa ne wayar Humaira ta dauki ƙara.

"Idan ita ce please ki ce mata muna abin hawa mun ma yi nisa."

Humaira dai murmushi take don ita abin ma dariya yake  ba ta, gyaɗawa Raihana kai kawai ta yi kafin ta fiddo wayar a jaka ta duba. Fadeel ne. Madadin ɓacin rai ko baƙin ciki da haushi, sai ta ji ranta ya yi wani irin sanyin da ba ta yi zatonsa ba. Raihana da ta leƙa ta ga waye ta kuma ga yanayin dake kwance a fuskar Humaira sai ta ji tamkar da daka tsalle tsabar farin ciki, amma sai ta ƙarawa murnar armashi da ambaton sunan Allah gami da yin hamdala.

"To sai ya katse? Ki É—auka mana please."

Ta kuwa amsa sannan ta kara a kunnenta da sallama. Fadeel daga ɓarinsa ya amsa. Ji ta yi muryarsa na sanyamata wata irin nutsuwa da sanyin ruhi, ta kasa hasko meke shirin faruwa da ita har sai da maganarsa ta katse tunaninta.

"Boddona, nayi kewarki sosai. Kin ji bawan Allahn nan shiru a waya kwanaki biyu amma ba ki nemi ki san ko lafiya ba ko?"

Sunan Boddona ya sanya ta dan lumshe idanu ta buɗe su da wani ɗan guntun murmushi a saman leɓɓanta, Raihana dai kallon ikon Allah kawai take yi tana washe bakin jin dadi na wannan sauyi da aka soma samu daga Humaira.

"Ka yi hakuri, nima ban samu nutsuwar zama ba ne balle har na kira na ji ko lafiya. Fatan komai lafiya? Ya mutanen gidan ya wajen Maman Husna?"

Sai da Fadeel ya yi wani irin dauke wutan da har ta yi tsammanin yankewa wayar ta yi, Raihana ma mutuwar tsaye ta yi domin cak ta tsaya daga tafiyar da suke yi baki a buÉ—e sai kuma ta sa hannu ta rufe. Ganin haka Humaira ta fidda wayar a kunnenta ta kalla, sannan ta É—an juya kadan tana kallon Raihana. Wayar ta maida kunnenta tana murmushin yanayin mamakin fuskar Raihana ta kara magana.

"Ba ka ji ba?"

Wata doguwar ajiyar zuciya ta ji ya sauke da ƙararta sai da ta ji a kunnenta.

"I am with you Boddo, na ji komai. Dukkansu lafiya kalau, nagode sosai da wannan."

Ta yi ɗan murmushi ba ta ce uffan ba har suka tsaya cak a ƙofar gidan Tasleem, Raihana sai ba ta kwankwasa ba tana jiran su kammala wayar bayan ta yi mata raɗa akan ta taimaka ta sa a loudspeaker don ta ji. Ba musu Humaira ta yi hakan.

"Kin yimin iznin shigowa yau? Kiyi hakuri, ina kewarki a idanuna. Na jure Boddo, amma hakurina na neman gazawa da aski ya zo gaban goshi. Please kin min izni na shigo yau mu gaisa koda na mintuna biyar ne?"

Ta ji wani tausayinsa da ba ta taɓa tsintar kanta a ciki ba ya kama ta. Meyasa wai ta ke ba shi wahala har haka? Me ya taɓa yi mata don ya baƙanta ranta? Ta ba kanta da kuma zuciyarta da amsar a'a, wato babu shi. Ta ɗaga kai ta dubi Raihana, da hannu yake roƙonta akan ta ba shi damar. Lumshe idanu ta yi sannan ta amsa.

"Ba damuwa. Ka shigo ka É—ebi lokacin da ya yi maka sannan ka tafi."

Nan ma Fadeel sai da ya É—auke wuta har ya ba su dariya suka gimtse.

"Kamar a mafarki. Alhamdulillah. Ki yi hakuri da shirun da nake yi Boddo, in sha Allah ana yin Magrib za ki gan ni. Nagode."

"Nima na gode. Allah ya kawo ka lafiya. Sai anjima."

"Ba ki ji ba."

"Me?"

"Ba zan gaji da ce maki ina sonki ba."

Yana fadin haka ya katse kiran. Kalaman sun shige ta kwarai, ta ji ta tamkar an yaye mata kaso tamanin na damuwarta. Ba ta sani ba ko tana son Fadeel ba, amma tana matuƙar tausayinsa idan ma tana tunano wulakancin da ta yi mishi a rayuwa da ma wadanda ba su ji ba su gani ba sai ta ji tamkar ta tsire kanta don ɓacin rai. A kwanakin nan dai ta sani tana nadamar abubuwa da dama data aikata a baya, babban tunanin dake cin zuciyarta bai wuce na dalilin aikatawar ba amma ta kasa tuna koda guda ɗaya.

Dariya da rungumar da Raihana ta kai mata ne ya farkar da ita daga zurfin tunanin da ta faÉ—a.

"Son so yar uwata. Allah ya nunamana aurenku da Yaya Fadeel. Ya sauki yar uwarmu lafiya ya ba ta dukkan farin ciki itama."

Ta kasa amsawa sai dan murmushi kawai, tuna Ummita duk sai jikinta ya yi sanyi a kasan ranta ta ce amin din.

"Malama mu shiga ciki kar mu zama abin kallo."
Chapter 70 · 0% Book details