← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 2 OF 101

Sashe 2

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

A gefenta kuwa halittar fuskarsa take ƙarewa kallo. Eh, tabbas suna kama, fuskarsa doguwa kuma siririya irin nata, yana da dogon hanci masha Allah, sai kuwa bakinsa daidai. Idanunsa manya kamar naya hatta da cikar halittar girarsa da gashin kai, duk kuwa da cewa shi nasa gashin ya yi fari fat na manyanta amma kamanninsu da shi sun fito fes har tsawon. Ba ta ƙara gani ba sai da ya saki dariyar farin ciki, anan kuma baki hangame ta ce. "Kai!" Ta furta a fili ba tare da ta shirya ba. Gaba daya suka juyo su na dubanta. Ta kama bakinta da sauri gami da ƙara sunkuyar da kai, mutumin ya matso ya durƙusa a gabanta, zuciyarsa ta yi wani irin nauyi, abubuwa da dama suka shuɗe a tsawon shekarun baya suka dawo mishi sabo fil. Ita kuwa kunya ce ta kama ta, bata ma gaida shi ba, ta gaishe shi a hankali don a zaton ta ma bai ji ba, amma ga mamakinta ya amsa.

"Barka da zuwa Mamana. Ki saki jikinki nan gidanku ne, gidan Abbanki, ba ki da inda ya fi nan kinji ko?"

Da ya fadi haka wai sai ta kalli Kawu, hakan da tayi ya ba su dariya. Kawu ya gyaÉ—amata kai.

"Idan eh kike so nace ko aa, toh eh Shatu, gidan mahaifinki kenan. Abin tunƙahonki."

Ta yi murmushi tana kara duban wanda ya kira kansa da Abbanta, sai nan da nan kwalla ta cikamata idanu. Wannan fargabar ta kau, so da kaunar suka dawo daga hutun da suka je, ta rungume hannunsa ta saki kuka sosai. Abubuwa da dama take tunawa, tabbas ta yi kewarsa a rayuwa. Koda ace ba ta rasa ci, sha da sutura ba daidai da kwana É—aya a rayuwa, to ta rasa wannan kusancin na É—a da mahaifi, shi din na dabanne. Ko ma dai tace ta rasa soyayyar iyaye gaba É—aya.

"Kiyi hakuri Mamana, ba zan ƙara yin nesa da ke ba, wancan ma ƙaddara ne, amma wannan karon in sha Allahu ni da kaina zan miƙa ki ɗakin mijinki. Allah ya ji ƙan Mahaifiyarki da Hajiya Dada."

Suka amsa da amin. Nan kuma ya shiga jan ta da hira kadan har ta sake, waya ya zaro a aljihu ya danna kira, sunan wata ya ambata, Ummita, ya ce ta zo yanzu. Daga haka ya  juya ga Kawu suka yi ta hira yana ba shi labarin rashin lafiyar Dada har zuwa rasuwarta. Suna nan zaune ita kam ta kasa ɗquke ido akan Abban, suka tsinkayi sallamar wata ƴar budurwa da ba ta wuce sa'arta ba. Baƙa ce, irin baƙin da hutu ya ratsa, riga da wando ne a jikinta sai dai ba su ɗame ta ba, ta saka hijabi iyaka kafaɗarta. Ta gaida Kawu sannan ta maida hankali ga Abba.

"Yauwa Ummita, kama hannun ƴar uwarki ku je a ba ta abinci ta ci ta yi wanka. Ki kuma faɗawa Maminki ina da baƙo a shirya masa abinci kafin mu yi sallah. A kawo ruwan sha."
Ummita ta amsa da toh tana kallonta fuskarta a sake ta ce.  

   "Lah Abba wallahi kuna kama sosai."

Duk sai ta ba su dariya, Abba ya dubi Aisha Humaira kafin ya maida duba gareta.

  "Itama ƴata ce, ita ce mai sunan Umma."

"Abba ita ce wacce ka ce tana Nijar ko?" Wannan karon da wani irin zumuɗi ta yi tambayar. Ya amsa mata da eh. Ta kuwa karaso da sauri ba tare da nuna kyankyamin komai ba ta rungumeta tana fadin. "Welcome Sister." Ba ta gane me ta ce ba amma itama ta rungumeta tana mai jin kaunarta har can ƙasan ruhinta.
  Ummita kenan, tana daga cikin mutane masu girma da matsayi sosai a rayuwar Humaira, har abada Humaira ba za ta cire ta a tarihin rayuwarta ba, ta karɓe ta a yadda take, ƴar kauyen Maine. Ƙamshi take a yayinda ita kuwa ba ta ma sani ba, ƙarnin kifin da ta ci a mota take yi ko kuma naman da ta ci ne. Kai ko ma mene ne, ta sani Ummita ba ta irin wannan ƙarnin, ƙamshi ne a jikinta, amma ba ta duba komai ba ta rungumeta. Ta tabbata tana daga cikin masoyanta na haƙiƙa. Ta kama hannunta ɗayan hannun kuma ta ɗauki akwatin kayanta wanda duk ya ci gidansu, akwati ne irin na da da aka yi yayinsa, Dada ta ce nata akwatin tun na auren Mamanta ne.
  Suka nufi wata ƴar siririyar hanya suka fito wurin wani ƙaramin hanya nan ma gefensa duk shuke shuke. Wurin ya burge Aisha Humaira sosai, a daidai ƙofar shiga wajen ma, shukoki ne sun kewaye jikin ƙofar da bango sun ba da zane mai kyau. Ummita ta ci gaba da tafiya har suka nufi wani ɓangaren, baranda ne sai kuwa wata ƙofa, suka shiga Ummita ta shiga kwala ihun kira.
"Mami! Mami!! Fito ki gani!"

Ihun da take tana kira ya sa sauran mutanen dakin suka fito. Maza da mata wadanda sun É—an girme ta sai ko yara.

"Wai Ummita me ke damunki haka? Tun ɗazu bakinki ya ƙi..."

Aisha Humaira ta lura haɗa idanun da suka yi ne ya sa sauran kalaman bakin matar suka maƙale. Kallonta take kamar a razane, ita kuwa kallonta take tana so ta ga ta inda suka yi kama da Ummita don ko kaɗan ba su yi kama ba. Ummita baƙa ce, wannan kuwa ta tsaye a gabanta da alama ma buzuwa ce. Gashinta a tufke a baya, ta kai duba ga wasu a cikin yaran, su ma farare ne ƙal, kyawawa da su.

"Wace ce wannan?"
ÆŠaya daga cikin Æ´anmatan ta tambaya tana bin Aisha Humaira da kallon tara saura. Ummita ta yi dariya ta jawota ta rungumo kafaÉ—arta.

"Mami, mai sunan Umma ce ta zo daga Nijar, Aisha Humaira. Abba ya ce shikenan ta dawo nan da zama cikinmu."

Wacce aka kira da Mami, ta tamke fuska babu ko É—igon annuri, suka kalli juna a kar na biyu. Kallon da ya da ya sa Aisha Humaira ta ji hantar cikinta ta kaÉ—a, dariyar matasan ne ya sa ta maida idanu kansu.
  
"Wai! Ni da yagwalgwal, amma wannan ma a Nijar ɗin a can ƙauyen kike ko?"

ÆŠaya a cikin matasan ya furta yana dubanta, idanunta nan da nan suka cicciko da kwalla.

"Kai Yassar, bana son haka. Sannu da zuwa Humaira, maza Ummita kai ta É—akinku ta yi wanka lokacin sallah ya gabato."

Da sauri na kalli matarnan, na sha mamaki ganin kamar ba ita ba, ta saki fuska sosai tana murmushi har haƙorin makkanta ana gani. Har Ummita ta faɗi saƙon Abba, Humaira ba ta iya tankawa ba hakanan ba ta iya ɗauke idanu daga kanta ba, itama jefi-jefi tana magana da Ummita tana kallonta ta kuma rasa dalili. Har Humaira ta bi bayan Ummita zuwa ɗaki ba ta daina waigenta ba, kuma itama Mami ta ƙi matsawa balle ta dauke ido a kanta.
   Ita kam Humaira jikinta ya ba ta kamar akwai wani abu.

®️Rufaida Umar.   02

A hankali ta bi kowace kusurwa a ɗakin da ido, gado ne kananu har hudu kowanne a nashi wurin, a gefen kowane gado akwai sif na kaya kamar dai ɗakunan makarantun kwana, babban daki ne mai yalwa wanda har akwai gurbin da ire-iren gadon uku za su samu matsuguni. Daga can gefe jikin taga kuwa, ƙaton madubi ne a saman dirowar gaban cike da kayayyakin kyalkyali na adon fuska da mayuka. Dakin tsaf-tsaf babu ƙazanta, ɗakin ƴanmata kenan. Ummita ta ɗaga akwatin tana shirin ajiyewa saman ɗaya daga cikin gadajen nan, baki bude tana kallon Humaira da niyyar magana, aka daka mata wani uban tsawa daga baya.
Muka juyo, wannan dai budurwar ce ta ɗazu mai ƙibar ciki. Ta zo da sauri ta janye akwatin ta yi wurgi da shi gefe. Idanu cike da masifa ta soma magana.

  "Wallahi kar ki kara  gangancin ajiyemin jakar wannan korar yunwar a gadona, don gulma da kinibibi idan abin naki dagaske ne meyasa ba za ki ajiye a naki gadon ba. Aikin banza kawai, uwar shishshigi. Haka za ki ƙare."

Tana kai wa nan ta  fice daga ɗakin tana mita,  Ummita ta kalli Humaira gami da jifanta da murmushin yaƙe.

"Ki yi haƙuri."

Ta gyaɗa mata kai tana maida mata martanin murmushin sai dai can ƙasan ranta, tana maimaita kalmar da ta ambata "Korar Yunwa". Ta fahimci manufarta tsaf, ta kuma gane ko wace ce ba ta samu karɓuwa a wajenta ba. Koda dai, ba ma ita kaɗai ba, ta lura da irin kallon da Mami ta watsamata. Ko ya zamantakewarta a wannan sabuwar duniyar za ya kasance?

"Hey, tunanin me kike? Amm..nidai bari kawai na kiraki da Humaira, kinga babu damar ce maki Aisha kai tsaye saboda sunan Umman Abbanmu kika ci ko? Hakan ya yi?"

Humaira ta gyaɗa kai karo na biyu tana mai sakin fuska, ta lura Ummita akwai kirki.  Bandaki ta nuna mata, ita kuwa ta yi  godiya, har za ta shige ta dakatar da ita.

"Yauwa Humaira ga wannan zanin ki yi amfani da shi ki goge jiki."

Ta sa hannu ta karɓa, zani ne a wanke a goge. Ummita har ta kama hanyar fita sai kuma ta dawo ta shiga bandakin gami da ba ta umarnin ta bi bayanta. Su na shiga ta kunna mata famfo gami da faɗin amfanin kowannensu. Ta fiddo mata sabon sabulun wanka daga cikin wata ƴar kwaba dake a gefe jikin bangon, sai kuma ta tambayeta ko ta taho da soso, Humaira ta amsa da eh. Hatta da ƙofar banɗakin sai da Ummita ta nuna mata yadda za ta ƙulle kuma ta buɗe, daga haka suka fito, nan ma sai da ta ajiye mata dardumar sallah saitin gabas sannan ta fice ita kuma ta ciro  sosonta a akwti ta koma banɗakin ta rufe.
Chapter 2 · 0% Book details