← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 22 OF 101

Sashe 22

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Raihana ta yi dariya, ita kuwa Tasleem dogon tsaki ta ja. Ba wanda ya ce mata ci kanki a cikinsu. Kasancewar ta yi wanka kafin zaman guga kuma ba ta da sallah hakan yasa ta kawai ta shiga sauya kaya. Itama atamfar ce amma nata dark brown ce mai haɗe da milk colour. Tana cikin shafa hoda Futuha ta fito daga wanka tana baza ƙamshin sabon showergel da suka ci arzikinsa a zuwan Antinsu Jannat gidan. Kallon Humaira ta yi kafin ta kalli gadonta ta gani wai ko ta ajiye mata kayan amma wayam. Don haka a fusace ta dube ta.

"Ina kayan da na ba ki guga?"

Humaira ta kalle ta da irin kallon wulakancin da suka saba yi mata itama.

"Ai gugan Mami kika iske ina yi ko?"

"Shekara kika yi kina gogewa Mamin mayafi? Don tsabar is..."

Ba ta kai ga ƙarashewa ba ɗif aka ɗauke wutar, aikuwa Raihana ta tuntsire da dariya itama Humaira sai da murmusa a ranta tana fadin Allah ya ƙara.

Nan fa Futuha ta hau zuba fada wai Humaira na sane iskanci ne ta fara sabo, tunda har ba a isa a sanya ta aiki ta yi ba. Ta tattara ta ba banza ajiyarta duk da cewa ranta wani irin tafarfasa ya ke yi na irin zagin da Futuha ke yi mata. Korar yunwa dai ya ƙi fita a bakinsu, ta kasa jurewa ta juyo, kamar ta maida martani da cewa su dinma asalin uwar Maminsu Nijar din ne, daga can suka fito can kauyen Agadas sai dai ta haɗiye tuna albarkacin Mami. Ummita ta shigo dakin, ita tuni dama ta shirya cikin atamfarta mai kyau ruwan sararin samaniya. Fitar da ta yi aiken Mamin ne zuwa siyan kati.

"Mami ta ce ku yi sauri."

Wannan ne ya katse zancen, kayan da Futuha ba ta sanya ba kenan sai kuwa wani ta sauya. Ba wata kwalliyar hayaniya Humairar ta yi ba amma iyakar kyau ta fito tsaf. Ba su suka yi haramar tafiya ba sai biyar da kusan rabi.

Koda suka fito baki daya, Ladidi kawai aka bari tana musu a dawo lafiya sai kuwa su Muhsin dake can ɓangaren Anna, Ummita ta dube ta da murmushi.

"Kin yi kyau sosai."

Ta riƙe haɓa.

"Idan babu wadannan buzayen a kusa ko?"

Suka yi dariya. Anan farfajiyar gidan suka sha hotuna a wayar Raihana dake faman jan su, su Tasleem na gefe su na kallonsu ita da Futuha, ko me suke tattaunawa?

Mami na fitowa suka shiga mota, kai tsaye ƙawataccen hall ɗin Marhaba suka nufa inda anan ne taron bikin.

"Ba ku mance katinanku ba dai ko? Ba na so a je wurin taro mutum ya yi tsaye kamar wanda ya zo gayyar soÉ—i."

Tasleem ta haÉ—iye dariyar muguntar da ya so kwace mata har sai da Futuha ta É—an zungureta akan ta nutsu. Katin Humaira tun fitarta kiran Mami, ta É—auke shi ta raba gida biyu ta wurga shi bayan gadonta.

Ummita da Raihana suka amsawa Mamin bayan sun duba sun ga katinansu, ita kuwa Humaira ko jakar ba ta buɗe ba tunda dai ta riga ta sani duk wani abun buƙatarta ta jefa a ciki.

"Humaira, Tasleem da Futuha fa?"

Suka amsa da eh su ma yana nan.

Su na isa bakin ƙofar kowaccensu ta fito, motoci ne na alfarma fake a wurin. Yanmata har ma da manyan mata ƴan gayu kawai kake gani a wurin, kasancewar Angon Shema'u ɗa ne ga kwamishinan ƴan sanda hakan yasa motar ƴan sandan har biyu a wurin su na lura da shige da fice.

Mami ce ta soma gaba suna gaisawa da wata ƴar uwar aminiyarta ta miƙa kati ta shige. Hakan ba karamin dadi ya yiwa Tasleem da Futuha ba sanin muguntar da suka shiryawa Humaira. Suka shige abinsu zuciyarsu fari kal bayan sun miƙa katinansu, Raihana ma tuni ta yi gaba. Ummita kuwa ganin yanda Humaira ta rikice da bincike jaka ya sa ta tsayawa gami da ja baya ta ba wasu hanya.

"Lafiya? Ya kika tsaya?"

Humaira ta ja guntun tsaki.

"Wallahi ban ga katina ba. Kinga ba ya cikin jakar."

Ta dafe kirji.

"Ba dai a gida kika bar shi ba?"

Ta girgiza kai cike da takaici, ta kasa cewa uffan ma. Ganin su na tsaye kawai ya sanya ta duban Ummita.

"Shiga ciki kawai, ni sai na koma gida."

Girgiza kai Ummita ta yi.

"Aa wallahi, sai dai ni na
/24, 9:39 PM] Maman Imaan Nvl Lvrs: Dukan Ruwa 11*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Fitowarsu kenan daga Bristol Palace dake kam titin farmcenter, Ibb ke jan motar yayinda shi kuwa ya kwantar da kai jikin kujera idanunsa lumshe. Babu abin da ya kai su face gaishe da abokin baban Ibb da ya zo daga Kaduna zai tashi zuwa Egypt sakamakon rashin lafiya.

"Hall dinnan ba ya rabo da biki."

Jin haka ya sa a hankali Fadeel ya buÉ—e idanunsa. Cikin iko da hukuncin Ubangiji, dubannasa ya sauka kan Humaira dake tsaye ta harÉ—e hannuwa a kirji fuskar nan a É—aure kamar koyaushe.

"Wait please."

Yanda ya yi maganar da sauri ya sa Ibb shima soma tafiya a hankali gami da neman wurin parking. Sai da ya daidaita motar a gefe kafin ya dube shi da alamar tambaya.

"Lafiya?"

Fadeel ya soma kokarin cire seat belt.

"Ita ce. Ba na so na ƙara rasa damar da za ta kubcemin."

Ganin yana kokarin bude ƙofar yasa Ibb saurin dafe hannunsa. Fadeel ya dube shi.

"What? Kana nufin kar na je?"

Girgiza kai Ibb ya yi.

"No, ba haka nake nufi ba. Sai dai ina so ka ba ni damar muje tare, idan kuma da hali kar ka ce komai. Ma'ana kada ka yi mata zancen soyayya da ma sauransu. Ni zan san ta yadda zan ɓullo mata, ok?"

Fadeel ya sauke ajiyar zuciya yana hangenta ta jikin side mirrow. Ba tare da ya dauke idanunsa ba ya amsa.

"Ok."

Daga haka Ibb ya kashe motar, suka fito kusan lokaci guda. Gaba ɗayansu ƙananun kaya ne jikinsu. Fadeel baƙar tshirt ne a jikinsa mai ƙaramin hannu sai blue jeans.  A tsintsiyar hannunsa kuwa, agogo ne ɗaure na fata baƙi, sumar kansa baƙa wuluk sai sheƙi take yi. Ya fiddo gilashinsa baƙi a aljihu ya rufe ƙwayoyin idanunsa, a yanda ya karanci Humaira a farkon haɗuwarsu hatta da kallo ta tsana. Ba ya jin kuma abu ne da zai iya jure bari ne, wato kallonta, musamman ma da ya kasance sun fi watanni biyu ba su sake haɗuwa ba.

A ɓangaren Ibb kuwa, blue tshirt ya sa da baƙin wandon jeans. Kallo ɗaya idan ka yi musu sai ka kara. Fadeel fari ne tas kuma dogo, har ya so ya fi Ibb tsawo. Shi kuwa yana da ɗan duhun fuska balle idan ya jera da Fadeel, kai tsaye za a kirashi baƙi.

Tana nan tsaye ba ta motsa ba har suka ƙarasa wajenta. Wani irin bugu kirjin Fadeel ke yi, kallonta yake tun daga sama har ƙasa, ba ya jin ta haura shekaru sha takwas, idan ma ta cika hakan kenan, amma ƙirarta ko a yanzun abin a kalla ne ina kuma ga nan gaba? Ya ja numfashi daidai sadda suka ci burki a gabanta. Sallama Ibb ya yi gareta, ta bar duban wayar da take yi a kokarinta na kiran Mami ta ce mata ita kam gida za ta koma. Zaratan samarin suka sanya wani irin kwarjini ya mamayeta da har ta kasa tantance su ɗin ko su wane ne, ta mance ma a inda ta san su. Daƙyar ta amsa sakamakon nauyi da harshenta ya yi, daga haka kuma ta  dauke kai ta raba jikinta da motar da nufin barin wajen.

    "Kamar ba ki gane ni ba ko?"

Cike da ƙosawar ta tafi ta dube shi. Kallo na ƙurilla don ta fahimci ko dagaske yake ta san shi ɗin, duk da cewa ba wannan ne karon farko da samari suke mata irin rainin hankalin nan ba idan sun ga ba ta kula su ba, amma hakanan a ranta ta ji wannan dai ya yi kama da kamilallan mutum, ba ta jin zai yi mata ƙarya. Bayan gama kallonsa ta maida kwayar idanunta kan Fadeel, ba ta ci nasarar ganin halittar kwayoyin idanunsa ba, shi kuwa wani yarr ya ji tun daga tafin ƙafarsa har tsakar kansa. Dakyar ya iya jarumtar juya fuskarsa gefe kafin ita ɗin ta kai ga ɗauke nata kwayar idanun a kansa. Ta tsuke baki ta ce.

"Ban gane ku ba."

Ibb ya yi mata bayani a taƙaice, nan da nan kuma ta ɗan sakar mishi fuska. Ko babu komai ta ji dadin mutunta da ya yi a wancan ranar wanda tun daga shi, Musaddam bai ƙara gigin shiga hurumin Raihana ba. Ba ta da masaniyar ko Fadeel mai yawan kiranta shi ne tsaye a nan ko kuwa dai wani abokin na Ibb ne daban kusa da ita hakan yasa ta gaishe su a jam'u. Suka amsa, Fadeel kam lebbansa ne suka motsa amma tuni ya yi nisa a kallonta, bai san lokacin da ya ƙara mayar da hankalinsa kacokam kan kyakkyawar fuskarta ba.

'Wallahi ina sonta.' Ya yi furucin a can ƙasan ransa kafin ya sa haƙori ya cije lebbansa ya sauke numfashi nannauya.

A cikin ɗakin taron kuwa, Tasleem da Futuha suka hana Ummita zuwa ga Mami, karshe suka ce ta zauna su za su je su shigo da Humairar wurin taron. Suka fito suka kara amsar katinsu suna dariyar mugunta, kawai burinsu su ga fuskar Humaira a karshe su ce Mami ta ce ta wuce gida ba za ta sanya ta roƙon kati a nan ba. Haka suka fito su na ta rarraba idanu, Futuha idanunta ya kai kan Ibb dake tsaye yana zuba wannan murmushin nasa mai tsada, a gefensa kuwa wani haɗaɗɗen matashi ne da ya zarce shi a haɗuwar. Ta dan murza idanu tana kara dubawa, tabbas Ibb ne.

"Ke, zo ki raka ni. Wayyo zuciyata, me Ibb ke yi a wajen bikin nan? Ko abokin Ango ne?"

Tasleem ta juyo, tuni Futuha ta soma tafiya ganin haka kawai ta mara mata biya.
Chapter 22 · 0% Book details