← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 98 OF 101

Sashe 98

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Tana nan kwance ta ji ihun Ummita da ya karaɗe gidan. Ta mike har zaninta na faɗuwa tana ja tana ɗorawa. Jiki na rawa ta ɗauki dogon hijabi ta zura. Saɗaf saɗaf ta bude ƙofar ta fita lokacin hankulan jama'a duka ya yi waje an fita an bi Wizzy. Ba ta fahimci wa Ridwan ya riƙe ba sai da kunnuwanta suka ji muryar Humaira na sanar da Fadeel  wai shi ne mutumin da ya keta haddin yar uwarta. Ai cikin Mami sai da ya yi wani irin kaɗawa. Jiki na rawa ta nemi hanya ta koma ɗakinta ta datse gam! Gumi fa ko ta ina ya shiga tsastsafo mata. Tana nan ta dauki waya amma rawar da hannunta ke yi ya sanya ta kasa koda bude wayar balle kuma ta kira. Ta yi wurgi da wayar sakamakon cikinta da ya shiga murɗawa ai sai ta nufi bandaki ta hau gudawa. Can ta ƙara fitowa ta yi jim a jikin ƙofar ɗakinta don jin me ke gudana, wani sabon al'amari ta ji, Anti Maijidda ke kuka da hamdala wai Allah ya toni asirinta. Yau gashinan Wizzy ya ce tare da ita ce suka haɗa baki suka yi garkuwa da su Ummita.

Ai Mami sai ta sulale a wurin ta zauna daɓas! Wannan tashin hankalin da me ya yi kama? Duk da ta sani babu wata hujja da Wizzy zai nuna ya ce har da ita ciki amma wannan furucin nasa babban barazana ce a gareta. Haka ta wuni ta ƙi fitowa a ɗakin, duk irin bugun duniya da kiran wayarta da aka dinga yi amma ta yi biris ko kallon wayar ta kasa balle ta ga mai kiran. Tana ji wasu na rantsuwar tana ciki wasu kuwa cewa suke yi ga dukkan alamu dai ta fice a gidan tunda akwai wadanda suka ce sun ga fitowarta sanye da hijabi.

Raihana kuwa a ranar asibiti ta kwana saboda tsananin ciwon kai da zazzaɓin da ya yi mata dirar mikiya.

Hakanan a wannan daren Abba yace babu abin da zai sa a jinkirta kai Humaira ɗakin mijintaz da wannan tashin hankalin suna kuka suka rungume juna ita da Ummita tamkar kar su rabu. Ga ƴar uwarsu can a asibiti kwance, haka aka tsitsa ƙeyar Humaira bayan sun yi sallama da Abba ya yi mata nasiha zuwa gidanta na aure.

***
Washegari kuwa tun asuba Mami ta shiga wurin Abba, yana dawowa daga masallaci sai ganin mace ya yi a zaune tana faman kuka. Ya kalle ta bai ce uffan ba ya kama hanyar shiga É—akinsa. Ta tare shi da sauri ta rike kafafunsa tana kuka kamar ranta zai fita.

"Abban yara, kada dai ace ka yarda da wannan baƙin ƙazafin da aka shiryamin? Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Wallahi Abban yara muddin aka ce kai ma ka mara wa masu zargina baya nikam ban ga wanda zan kama ba. Ni Maryam me marayun Allah suka yimin da zan cutar da rayuwarsu?"

Abba kallonta kawai ya ke yi da idanunsa da suka tasa ga dukkan alamu bai samu wani baccin kirki ba. Murmushin yaƙe ya bita da shi.

"Ni kin ji na ce maki ina zarginki ne Maryama? Kin ji wani abu daga bakina?"

Sai ta mike tsaye suna duban juna.

"Ba ka faÉ—i ba, amma shirunka ya nuna ka aminta da zargin masu zargi."

Ya kauda kai don wallahi ji yake yi a duniya a yanzu babu abin da ke mishi muni ya kall sama da fuskarta.

"Maryama, abar zancen. Tunda shi wannan baƙin azzalumin ya shiga hannu, gaskiya za ta yi halinta ai yanzu. Ki kwantar da hankalinki masu zarginki za su bari muddin komai ya bayyana."

Yanayin da ya yi zancen sai ba ta gamsu babu komai a zuciyarsa ba dangane da ita. Ta dai matsa mishi kamar yanda ya buƙata ya faɗa ɗakinsa.

***
Ina labarin Humaira da Fadeel?

***Afuwan zuwa gobe zan ɗora in sha Allah. Kuyi hakuri Dukan Ruwa saura ƙiris ya yi maku bankwana in sha Allah. ***Kukan Humaira ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Abubuwa da dama ne ke ƙara mata ƙarfin kukan. Wannan tashin hankalin na jin wai da sanya hannun Mami a garkuwa da su ya tsaya a ranta. Ta dinga tunano kalar rayuwar da suka yi da ita a gidan tsawon shekarun da ba su da yawan da za a kasa ƙirgawa, irin kulawa da nuna kaunar da ta dinga yi mata. Ita kuwa komai da Mamin ta ke mata ta ɗauke shi da zuciya ɗaya, ba ta taɓa kawo wani abu na mugun zato a kanta ba idan aka cire sanin da ta yi Mami ba ta farin ciki da aurenta da Fadeel. Sai yanzun abubuwa da dama suke mata yawo a kwakwalwa, wai dama ya za'a yi macen da ta haifi yara da kanta ace ta fi kaunarsu akan abin da ta haifa? Kenan ta tabbata batun Hajjo da ta ce da biyu Mamin ta dakile ta daga karatun boko? Toh idan ita din ta kasance ɗiya ga tsohuwar kishiyarta da ta rasu, me Ummita ta tare mata? Me ta yi mata a rayuwa da har sa ta nakasta rayuwarta har haka? Ta maida ita ƙaramar budurwa kuma bazawara? Tayi sanadin da aka keta alfarmarta har wannan masifa ke bibiyarta wato Wizzy. Ta yi sanadin da aka fasa aurenta da masoyinta Sahabi. Mene ne ribar Mami da ta shuka dukkan waɗannan munanan ayyukan. Shin kodai Raihana ta sani ne? Tambayar da ya shiga kwakwalwar Humaira kenan. Ta ɗan muskuta ta share fuskata. Anya Raihana ba ta da wani labarin dangane da Mami? Yarinyar a yan kwanakin nan ta sauya gaba daya ba ta rabo da kuma da damuwa? Sai an matsa da tambaya sannan ta ke saita kanta ta shiga harkokinta? Kai gaskiya tana da tabbacin akwai abin da Raihanar ke ɓoyewa. Sai tausayin ƙanwarta ta ya mamaye zuciyarta, ita ɗin ba ta da wani aibu a yanzu, ta tsarkake zuciyarta daga dattin ƙiyayya da hassada irin wanda yan uwanta Tasleem da Futuha suka ɗorawa kansu. Tana kaunarsu tana kuma zaune da su da zuciya ɗaya babu wani abu bayan hakan.

Turo ƙofar da aka yi gami da sallama cikin tausassan murya ya katse tunanin Humaira, ta ƙara sunkuyar da kanta tana ɗan sakin numfashi irin na wacce ta ci kuka kuma take kan yinsa. A can ƙasan zuciyarta ta amsa sallamartasa.

Ya ƙaraso cikin dakin sosai, ya yi wanka ya sauya sutura zuwa jallabiya fara ƙal wacce ba ta ɓoye kyakkyawan tsarin halittar da Allah ya yi mishi ba. Sai baza ƙamshi yake yi ta ko'ina. Ya ɗan bi ɗakin da kallo kaɗan yana murmushi da alfahari da zaɓin da ya yiwa Humairar na kalar da ta fiso wato kore. Sai adon ɗakin ya kasance farin da kore. Zama ya yi a gefenta har kafaɗunsa na gugar nata. Fadeel kenan, shigowarsa babu aboki ballantana ɗan rakiya.

Hannu ya sa ya yaye rufin fuskarta. Ganin hawaye kwance ya sanya shi saurin riƙo haɓarta da ɗago kan suka dubi juna, ai yanda ya ga idanunta sun kumbure sun yi ja sai ya ji wani sabon tashin hankalin na daban.

"Boddo, kukan kike ta yi? Ya Salam, sai ki janyowa kanki wani ciwon?"

Ya shiga taɓa goshinta da gefen wuyanta don ya ji ko jikinta da zafi, ita kuwa sai noƙewa take shi ko zuciyarsa daya yake yi. Gaba daya ganinta cikin wannan halin bai masa dadi ba ko kaɗan.

"Please ya isa hakanan. Kinga yanzu babu zafi jikinki. Kiyi hakuri tunda komai yanzu yana hannun hukuma. Idan kuma don kin ji ya ambaci Maminki ne kar ki bari wannan ya yi tasiri a zuciyarki. Tunda har ya gan shi a hannun hukuma to zai iya ƙirƙirar kowane sharri ya faɗi. Ki kwantar da hankalinki koma mene ne bincike zai bayyana."

Ta gyaÉ—a kai, ya lalubo tafukan hannunta ya sanya cikinnasa. Rashin sabo da hakan daga shi din har ita sai da suka ji wani yarr.

"Kina da alwala?"

Shi ne tambayar da ya yi mata, nan din ma kan ta gyaɗa ta a kokarin zare hannunta. A hankali ya saki sannan ya faɗa banɗakinta. Can kuma ya fito ya yi mata umarnin zuwa su yi nafila. Ba musu ta miƙe ta gyara zaman laffayarta. Bayan sun idar ya dafa kanta ya yi mata addu'o'i. Daga nan ya kama hannunta ya miƙar suka fita suwa falo. Ta ɗaga kanta a hankali tana kallon falon, hamdala ta shiga ui a zuciyarta, yau ita dai Humaira ita ce ta mallaki wannan irin falon da sai dai ta gani a soshal midiya su na yawo don ko gidan Futuha da ake ta santinsa bai kai rabin nata tsaruwa da kyau ba. Komai a falon adon skyblue ne da fari, iyakar kyau da tsari ya yi.

Jan hannunta da Fadeel ya ƙara yi ne ya maido ta hayyacinta, ta ɗan yi saurin janyewa tana ɗan tura baki. Da alama ita ba ta son wannan baƙon halin nasa na riƙe mata hannu. Ya yi murmushi ya matso dab da ita gami da sa hannunsa saman ƙugunta ya matse ta gam har fuskokinsu na haɗuwa wuri guda.
Idanunsu a lumshe ba ka jin komai sai bugun da kirjin kowannensu ke yi. DaddaÉ—an kamshi babu ko digon wari shi ke fita daga bakunansu.

"Kin zamo mallakina Humaira, babu sauran wata ƙofa da ke buɗe tsakaninmu. Babu kuma sauran sharaɗin da ya yi saura. Ki taimake ni ki bar kokarin yimin iyaka da dukkan inda hannuna ya sauka a jikinki."

Ya yi maganar da muryar da ta rasa na Fadeel ne ko kuwa, har sai da ta buɗe idanunta, aka yi sa'a shi ɗinma kallonta yake yi a lokacin, sai dai ga mamakinta, hawaye ne kwance saman kumatunsa. Ta yi kokarin ja baya a ɗan ruɗe, ya yi saurin ƙara riƙe ta sosai.

"No Humaira, bar ni na ji ɗuminki, na ƙara samun tabbacin Fadeel ba mafarkin da zai iya farkawa yake yi ba. Alhamdulillah Ya Rahman."
Chapter 98 · 0% Book details