Sashe 15
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Kasancewar gidan cike yake da jama'a ƴan uwa, makwafta har ma da abokan arziki ne ya sanya Ibb zagayawa ta ɓangaren Alhajin ya shiga ainahin falonsa na karɓar baƙi. Kamar yanda ya yi tsammanin hakan ya tarar, wato dai Alhajin ba shi ɗaya ba ne a falon, yana tare da babban yayansa Baffa Gidado sai ɗan gidan Baffa Gidadon, Harɗo. Sai ko ƙannensa guda biyu dake zaune su ma a gefe ana ɗan taɓa hira, kallo ɗaya za ka yiwa fuskokinsu ka fahimci su na cikin annashuwa. Sallamarsa ce ta katse hirar tasu wadda ke gudana da harshen fulatanci, suka dube shi gaba daya, ya karaso yana ƙara miƙa gaisuwa a karo na biyu domin dazun daga gidan ya fita. Alhaji ya amsa gaisuwar yana bin fuskar Ibb da kallo ganin yadda yake wata irin fara'a na musamman wadda rabonsa da ganin kwatankwacinta tun a baya kafin afkuwar wasu lamura marasa daɗi. Ganin bakin Ibb na ta motsi amma ya kasa magana ya sanya Alhaji miƙewa tsaye wannan karon kirjinsa bugu yake da sauri-sauri.
"Muje." Shi ne kawai abin da Alhajin yace, aikuwa kamar jira yake har da tuntuɓe a kokarinsa na bin bayan shi. Wata ƙofa suka bi wacce kai tsaye main parlour din Alhajin na cikin gidan suka faɗa. Ko zama Alhaji ya kasa hakurin yi su na karasawa tsakiya ya juyo gaba ɗayansa.
"Ibrahim, ya ake ciki? Meke faruwa?"
Madadin ya amsa sai kawai ya rungume Alhajin kafin ya sake shi yana dariya.
"Mafarkinka ya tabbata zahiri Alhaji."
Alhaji hannunsa har rawa yake ya kama kafaÉ—un Ibb har idanunsa sun cicciko da kwalla.
"Ya..ya..ya..da..wo?"
Ya yi maganar da rawar murya, jinjina kai Ibb kafin ya amsa.
"Eh, FADEEL ya dawo."
Alhaji ya sauke nannauyan ajiyar zuciya.
"Alhamdulillah, Alhamdulillah. Yana ina yanzu? Muje ka kai ni na gansa."
Ibb zai musa amma babu dama domin dagasken dai ba abin da Alhaji zai saurara. Don haka sai kawai ya juya, Alhaji biye da shi suka fito. A farfajiyar gidan suka yi kiciɓus da Ango Fu'ad wanda shigowarsa gidan kenan daga Hotel din da abokan karatunsa suka sauka. Ya karasa ganin irin rawar jikin da Alhajinsu ke yi, ga Ibb na kokarin buɗe mota.
"Alhaji, fita za ku yi ne?"
Alhaji ya dafa kafaÉ—arsa fuska a sake ya ce.
"Maza shiga mota." Ba musu ya zagaya ya shiga har sannan fuskarsa dauke da mamaki, ya kuma kasa tambaya. Ibb bai ko hana Alhaji wannan yunƙuri ba don ya sani Fadeel zai yi farin ciki kwarai da ganin ƙaninnasa.
***
 Ya yi wanka ya shirya tsaf cikin riga body hug fara ƙal sai blue jeans. Yana zaune yana kurɓar ruwan shayin da aka kawo mishi, hankalinsa kaf yana wajen Mahaifinnasa, wata zuciyar na ce mishi ya je ya gan shi, wata kuma na kwaɓarsa. A hankali ya ajiye mug din dake hannunsa ya jingina kai jikin kujerar yana mai lumshe idanunsa. Dogayen gashin idanun suka kwanta luf saman fatar wurin. Ji ya yi ana buga ƙofar, ya buɗe su kafin ya miƙe. Yana da tabbacin Ibb ne. Hakan yasa koda ya bude bai tsaya kallonsa ba ya juya ya koma cikin ɗakin gami da faɗin.
"Wato gadina ka koma kenan?"
"Muhammadu." Ya tsaya cak a tsakar É—akin, kaf duniya mahaifinsa kaÉ—ai ke kiransa da ainahin sunansa, da hanzari ya juyo, tuni lumsassun idanunsa sun kaÉ—a. Alhajin ya taho da sauri ya rungumeshi, shi kuwa ya tsaya kamar wanda aka dasa a wajen ya kasa motsi. Fu'ad da bai san wainar da ake toyawa ba sai yanzun, kawai kuka ya sanya tsabar murnar ganin yayannasa da ya nisanta da su saboda wasu dalilai. Ya karaso da sauri ya haÉ—a daga Alhajin har Fadeel ya rungume yana kuka. Duk jarumta irin ta Fadeel sai kawai ya ji hawayensa sun zubo. Suka saki juna Alhaji da kansa ya sa hannu yana share masa hawayen.
"Ashe da raina da lafiyata ban mutu ba zan ga wannan rana? Alhamdulillah."
Abin da Alhajin ya furta kenan. Fadeel ya yi murmushi da gefen kumatu yana dafa kafaÉ—ar Fu'ad.
"Ango, har ka girma za ka yi aure."
Suka yi dariya har Ibb, Fu'ad kuwa yan sunkuyar da kansa gami da shafar ƙeya. Nan fa Alhaji ya matsa akan lallai sai ya tattara sun tafi gida da shi. Anan ne kuma ya tamke fuska kwarai, ya koma Fadeel ɗinsa na ainahi.
"Muddin tana gidan nan ba zan iya shiga ba. I am sorry Alhaji."
Jin haka Fu'ad da Alhaji suka kalli juna suka yi murmushi. Shi sai a lokacin ma ya ji nauyin Fu'ad din, wai uwarsa yake ikrarin ba zai shiga gidan idan tana ciki ba.
"Yaya Fadeel, Mama ba sa tare da Alhaji, tayi wani auren a garin Kogi. Sai dai ko Anti Amarya our new Mum."
Sai Fadeel ya kasa cewa komai, ya maida dubansa ga Alhajin, ya gyaɗa masa kai don ya ƙara tabbatar da abin da Fu'ad ya faɗi.
"Yanzun ka shirya bin mu?"
Ya jinjina kai yana murmushi. Ibb tuni ya soma haɗa mishi shirginsa. Fu'ad ya karɓi akwatin suka fito baki ɗaya, suka yi mota yayinda shi kuma Ibb ya tsaya a reception.
Isar su gidan kai tsaye suka nufi sittingroom wajen su Kawu Gidado, sai dai tuni sun fice masallaci gabatar da sallar La'asar. Koda dawowarsu ganin Fadeel gaba É—aya dakin ya kaure da murna. Magana dai ta bazu a gidan Fadeel ya dawo, babban É—a namiji a wurin maigidan. Nan fa mata gwaggonninsa Æ´an uwan mahaifinsa kowa ya fito zuwa falon. Murna kam ba a magana. Yayyunsa mata waÉ—anda kaf dinsu su na da aure sai guda É—aya bazawara da aurenta ya mutu take zaune a gidan da yaranta, su din ma kowaccensu ta halarci falon. Kallonsu kawai yake yi yadda kowacce ke haba-haba da shi, murmushi kawai ya ke yi don ba shi da tabbacin ko abin nasu ya kai zuci ko aa. Sanin da ya yi musu daban a baya, ba shi da masaniya akan yanzu.
***
 Raihana ce zaune a can lungun gadon Tasleem ta maƙure a gefe tana zuba kuka ga waya saman kunnenta. Musaddam take ta ba hakuri adalilin ya ƙi ya huce tun sadda Humaira ta gasa mishi zafafan maganganu. Ya kuma ci alwashin ko don ya nuna wa Humaira ba ta isa ta tsaida shi daga abin da ya yi niyya ba, sai ya kusanci Raihana ko ta ƙarfi kuma ya yi hotuna don ya shayar da ita mamaki. Yana sane da gangan ya ƙi ya huce saboda kawai ya ƙara fahimtar irin matowar da Raihanan ta yi a kansa.
Sati ɗaya kenan da dawowar Yayannasu amma ko kaɗan walwalwarta ba ta dawo daidai ba ga wani irin tsanar Humairar da take ji a ƙoƙon rai amma shakkar kada ta tona mata asiri da ma tsoron ita kanta Humairar ya hana ta labartawa koda Tasleem ce balle Futuha. Sai ƙawarta da ta ba labarin, ita kuwa ƙara hure mata kunne ta yi akan kar ta yarda wata can bare ta raba ta da abin sonta. Da wannan huɗubar da kuma mahaukacin son da take yiwa Musaddam idanunta suka rufe ruf. A wannan yanayin walwalarta ba ta dawo ba sai da ta tabbatar ya haƙura bisa alƙawarin za ta zo gidan su Munirat su gaisa.
Humaira ta shigo É—akin daidai sadda Raihanan ke fadin. "Shikenan zan zo goben idan har ganina zai samar maka da nutsuwa."
Wannan kalmar ta daki zuciyarta, sai dai ta dake ba ta ko kalle ta ba ta ƙarasa ciki, dama mayafin abayarta za ta ɗauka zasu je Shoprite ita da Ummita, Mami ta aike su.
Raihana kuwa ganin Humaira ya sa ta shan jinin jikinta. Ta kasa magana kwakkwara sai um da humm ina jinka. Guntun tsaki Humairar ta ja ta fice, ta sha alwashin ko ina ne a goben sai ta bi bayanta ta kuma kama É—an iskan dumu-dumu ta ci uwashi.
 A falon ta haɗu da Ummita, har suka soma tafiya ta ga dai hira suke amma ita ke kiɗa da rawarta hakan yasa ta dube ta.
"Wai ke lafiyarki kin wani haɗe rai kamar wacce aka aikowa saƙon mutuwa? Koda dai ɓata bakina nake dama ai halinki ne. Amma naga ai yanzun ba kiciɓus kika yi da maƙiyinki naki ba ko?"
Tana nufin saurayi, Humaira ta ja tsaki ta girgiza kai.
"Ba komai fa."
Taɓe baki Ummita ta yi ba ta ƙara magana ba sanin hali. Sai kuma can don kanta ta saki fuska suka hau hira. Kayan maƙulashe irin su Jam, Ketchup, Mayonnaise da sauransu, shi Mami ta bada su siyo na Yaya Mubarak. Sun kammala suna dab da ficewa suka tsinkayi sallama a gefensu. Lokaci guda suka juya ga mai shi, wani matashin saurayi ne gajere mai ƙiba. Irin ƙibar da ba ta da muni. Daga yanayin yadda ya saki fuska za ka fahimci mutum ne mai fara'a. Humaira wacce kallo ɗaya ta mishi ta dauke kai gami da ci gaba da tafiya, ganin haka itama Ummita ta mara mata baya, ya kuma bin bayansu da sauri ya sha gaban Humaira.
"Ranki ya dade, kiyi hakuri na tsayar da ke. Nima kuma na san darajarki da ƙima ta zarce a tsayar da ke a hanya a..."
"Kai Malam saurara don Allah! Ni nan da ka ke gani da mijina a hannu don haka kama kanka. Muje."
Ta fisgi hannun Ummita ta bi gefe suka fice a nan. Hakan da ta yi ba karamin ɓatawa Ummita rai ya yi ba, ba yau farau ba, idan da sabo ya ci ace ta saba da ganin irin cin kashin da yar uwarta ke yiwa samari. Ita har mamaki take yadda gaba daya Humairar ke sauyawa kamar ba ta taɓa zama haɗa hanya da wani abu wai shi mutunci ba. Ta fara gasƙata zancen Raihana da ta ce jinnu ne da ita. Kamar kuma ba ita ba, sai ga shi a hanya ta saki rai sun ci gaba da hirarsu lafiya lau.