Sashe 57
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Abba ya ja baya da sauri ya zauna saman kujera mafi kusa da inda yake, yayinda Humaira ta yi mutuwar tsaye. Ita kuwa Raihana kwasa ta yi a guje zuwa bandakin don ganin halin da Ummitan ke ciki. Aikuwa ta iske ta a kife tamkar babu numfashi. Ta kuwa ƙwalla ihun kiran sunan Abba. Kusan da rige-rige suka shiga banɗakin. Mubarak ne ya yi ta maza ya cicciɓe ta bayan ya tabbatar da bugun zuciyarta ya fiddo ta falon ya shimfiɗe saman kujera sai dai duk wani kokari na watsa ruwa da ma sauransu anyi amma babu alamun Ummita ta san ana yi. Ana shirin fita asibiti Mami ta dakatar ta ce gwara a kira makwafciyarsu wata likita gudun fashewar zancen a duniya. Abba ya yi na'am, Mubarak ne ya fita da rawar jiki har gidan Dakta Inteesar an ci saa kuwa ta fito cikin shirin tafiya asibiti. Ganin Mubarak aboki ga babban ɗan ta Najeeb ya sanya ta dakatawa. Roƙon da ya hau yi mata ya sa ba ta iya yi mishi musu ba sai ta shiga motarta suka kama hanyar gidan don akwai ƴar tazara kaɗan ita daga bayansu take. Cikin ikon Allah ta ba Ummita taimakon gaggawa ta farfado sai kuma ta dube su.
"Ya dace a yi mata gwaji sosai din tabbatar da abin da ke damunta."
Ta furta hakan ta yi shiru don jin me za su ce, a matsayinta na likita ta gama tabbatarwa Ummita na da juna biyu. Shiru ta yi musu don ta fi son ji daga bakinsu sun amince da gwajin. Tana sane da labarin abinda ya afku ga Ummita. Su kansu mutanen gida ba su da masaniyar cewa duk yadda suka so da ɓoye labarin fyaɗen Ummitan sai da ya fita ba. A duniyar yanzun ai mutum ake kiwo ba dabba ba, kana abu kana ganin tamkar duniya ba ta sani ba amma zirr ake kallonka.
Abba ya yi yaƙe.
"Babu damuwa Dakta, zamu kai ta asibiti."
Ta lura ba su son zancen ya fasu, ita kanta ta tausaya musu babu kamar Ummita wacce tunda ta farfado uffan ba ta ce ba, kukan ma ta ƙi yinsa sai sauke ajiyar zuciya akai-akai. Haka Dakta Inteesar ta yi musu sallama bayan ta rubuta magungunan da ya dace wanda take da tabbacin zai taimaki Ummita bisa yanayinta na mai juna biyu. Mubarak wanda ke tsaye ya ƙurawa Ummita idanu yana jin abu mai nauyi na taso mishi wanda ya fi kama da tsabar tausayinta da kuma kauna ta ƴan uwantaka. Kamar dai yanda yake tunani. Shi ne ya karɓi takardar magungunan ya fice.
***
Kwance yake idanunsa a lumshe, babu komai a ransa sai Humaira. Yana ji a jikinsa an soma zuwa gaɓar da yake da tsananin buƙatar kasancewarsu tare a inuwar aure. Shi din fa ba dutse ba ne, namiji ne kuma lafiyye da yake buƙatar aure. Soyayya mai ƙarfin da yake yiwa Humaira shi ne silar da ya danne wannan buƙatuwar ya ɗora shi kacokam a kanta yana jiran lokacin da mafarkinsa zai tabbata. Sai dai kuma yaushe ne?
Wannan damuwar ce ta hana shi fita ko'ina, hatta da mai gyara mishi dakuna bai san yana nan ba, shi dai Nura yana falo yana aiki kafin ya shiga É—akin. Hatta shi bai dan cewa Fadeel na gidan ba sakamakon motarsa da ba ta nan tun daren jiya. Æaci ta yi a hanya ya bar ta can makanikinsa ya je ya É—auka.
Daidai lokacin Murja ta faɗo ɗakin da ƙunshin kayan gugan Fadeel din a hannunta wanda ta karɓa a hannun Sadi mai gugansu, dama ta jima a yar barandar da zau sada ta da ɗakin Fadeel tana tunanin dabarar da za ta yi wa Lawal ta shiga. Sai ko ga Sadi ya zo wucewa nan da nan ta karɓa ta ce za ta karasa da shi.
Suka gaisa da Lawal a falo, ta nuna zai karɓa ya shigar da su ta ce masa ya bar shi za ta karasa ladanta. Bai ce komai ba, dama a farko gargadin da Fadeel din ya yi mishi ne ya sanya shi dakatar da ita, ya hana kowa ya shigo masa sashinsa idan ba ya nan matukar dai ba Fu'ad ko Alhaji da Ibb bane. Amma ganin kayan wankin ne kawai za ta ajiye ta fito ya sanya shi ba ta wuri shi kuma ya ci gaba da kakkaɓe kakkaben kujeru da kayan kallo.
A lokacin da ta shiga dakin, Fadeel ya zagaya bandaki, yana dab da fitowa ya ji motsin mutum a dakinnasa, bai kawo kowa ba sai Lawal. Ya san ba shi da masaniyar yana gida bai fita ba. Don haka ya fito daga shi sai singilet da dogon wandon sport.
Daidai lokacin da ta ajiye kayan a gefe ta yi wurgi da filo ta ɗaga katifar gaba ɗaya da zummar sanya layar. Kasancewar idanunta ya rufe ko kadan ba ta ga wayoyin Fadeel din dake gefe ba a ajiye. Tana zuci-zucin ta yi ta ƙare kafin shigowar Lawal ya isketa.
Fadeel ya bude kofar ya fito, hakan ba karamin razanata ya yi ba ta saki layun dake a hannunta suka zube a ƙasan darduma. Mamaki mai tsanani ya kama shi har ya bude baki ya kasa magana. Ya karasa sosai ya kara kallo, tabbas layu ne. Nan da nan ya tamke fuska tamkar bai taɓa wani abu wai shi dariya ba.
"Zamanki a gidannan ya ƙare. Wallahi kin ji na rantse maki ko yau Anti Amarya ce ta haifeki dole ki bar gidannan. Ni Fadeel na fi ƙarfinki, na kuma fi karfin duk wani da zai sanyaki aikata mugun abu don ki ci galaba a kaina."
Jin haka sai kawai ta hau tsuma da borin kunya.
"Ni..nifa ba.."
"Shut up!"
Tsawar da ya yi ya sanya Lawal faÉ—owa É—akin. Nan da nan hankalinsa ya tashi, shima idanunsa suka sauka kan layar dake ajiye a tsakar dakin. Fadeel ya hau shi da faÉ—an don me ya bari ta shigo masa daki alhalin ya gargaÉ—eshi.
"Ka yi hakuri Yallaɓai, wallahi na yi nayi da ita ta bani kayan gugar na kawo ta nunan ita za ta kai. Shi ne.."
"Shi ne me?!"
Fadeel a zafafe ya tari numfashinsa jikinsa har ɓari yake yi ga tsikar jikinsa da ya tashi gaba daya. Abin da ya faru shekarun baya kawai ya fadomasa a rai, sadda ya kama Mamar Fu'ad tsamo tsamo a ɗakin Mahaifiyarsa tana barbaɗa magani. Daga ranar ya tsane ta, rashin wayo da wauta kuma ya sanya bai yi tunanin sharewa ba. Tun daga kuma sadda mahaifiyarsa ta taka wannan magani ba ta ƙara zaman lafiya ba da Alhajinsu, har dai a karshe Alhaji ya yi mata sakin wulakanci. Shi kuma ya sha baƙar wahala a hannun Mamar Fu'ad. Ya ji ya ƙara tsanar Murja ninkin ba ninkin. Kuma yanda ya rantse ba zai yi kaffara ba sai Murja ta bar masa gida ubansa idan ko Alhaji ya ƙi to fa shi zai bar gidan gaba ɗaya.
Murja cike da kunyar kamen da aka yi mata ga uwa uba Lawal dake tsaye ya ƙi fita yana kallon ikon Allah, ta durkusa ta kwashi layun ta fice tana dakawa Lawal wata uwar harara kamar idanunta zasu zazzago.
Fadeel ya dafe kai yana mai runtse idanu zuciyarsa na tafarfasa tamkar an kunna ruwan heater.Â
"Ka yi hakuri in sha Allahu zan kara kiyayewa."
Gyada masa kai kawai ya yi gami da yi mishi alama da hannu akan ya fita, Lawal ya juya ya fice mamakin wannan hali na Murja da bai taɓa zato ba. Lallai mutum ba abin yarda bane.
Shi kuwa Fadeel sai da ya samu nutsuwa sannan ya fada wanka, ba shi da niyyar fita daga gidan amman daga faruwar al'amarin ya ji gaba daya gidan ya fita a kansa. Kai tsaye wurin Ibb ya tafi, dama tun jiyan yake faman kiransa akan zancen bikinsa da ya taso yana ƙin zuwa yana ba shi uzurirrika saboda damuwar Humaira da batun auren Ibb ke taso masa da shi.
Murja kuwa tana zuwa ta shiga haɗa kayanta, ta gwammace ta bar gidan da ace Fadeel ya fasa zancen nan har Alhaji ya tsane ta ya kuma ƙi jinin haɗa zuri'ar ɗansa da ita. Anti Amarya kadai ta fadawa, nan da nan hankalinta ya yi mugun tashi, ta hau ta da faɗa tamkar ta ari baki. Babban baƙin cikinta ma ba ta yi shawara da ita ba ta yi raɗin kanta.
"Ba ki da wayo ko kaɗan Murja! Wa ya fadamaki samun Fadeel a hannu abu ne mai sauki? Ke kinsan irin karfin ibadar wannan yaron? Toh wallahi ko wani Malamin ba zai nuna masa tashin dare da nafilfilu ba ko an fadamaki baƙin tabon sallar dake goshinsa da goge dutse a goshin ta same shi? Kai Murja! Toh kuwa ya zama dole ki bar gidannan! Ni zan samu shi Fadeel din nasan siyasar da zan mishi don kar magana ta je kunnen Babansa."
Murja ta kara jin wani malolon abu ya tsaya a ƙahon zuciyarta. Dama ta sani Anti Amarya ba za ta taɓa goyamata baya ba. Ta kuma soma yarda da yayarsu Rabi da ta ce Anti Amaryar kanta kawai ta sani, ba wani so take yi ta tallafe ta ba shiyasa ta ce ta sauya dabi'u ta nuna ita wata salihar ce. Ban da haka ai ta san wannan ba abu ne mai sauki ba da kuma zai yiwu kawai a yi duka ɗaya lokaci daya a wuce wajen.
Ta shareta ta cigaba da hada akwatin kayanta. Kafin wani lokaci ta kammala ta fice abinta, Anti Amarya ba ta kara cewa uffan ba, ba karamin ɓata ranta ta yi ba, ita yanzu babban tashin hankalinta yanda za ta rufe maganar kar ta je kunnuwan Alhaji. Ta tsinewa Murja ya fi a ƙirga. Wannan ya sa ko kallonta ba ta yi ba da ta fice. Allah ya taƙaita Hannatu ba ta gidan ta je wurin dangin Alhajinsu.