Sashe 61
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 5 min read
Ta ja mata tsaki ta mike ta nufi dakin Anna amma ta gama ƙudurtawa a ranta babu fashi. Idan har ƙimar ita kanta ƴar tiktok Futuha zai taɓu a zage ta a idanun duniya toh wannan daidai ne. Gwara ma su yi hakan kawai.
***
Mami ta taushi Ummita dakyar ta samu ta yi shiru, ta yi musu Æ´ar nasiha sannan ta fito. Kai tsaye dakinta na nufa ta dauki waya ta kira Hajiya Lubna. Komai dake afkuwa ta zayyane mata. Ta kara da faÉ—in.
"Yarannan sun tada hankali lallai sai dai a zubar da cikin Ummita, kinsan dai yadda muka yi da Sadik Wizzy. Ina tsoron su kwatanta wani mugun abun."
"Haba Maryam, sai ka ce ba ke kika haife su ba. Ba za ki yi musu jan ido ba? Wai ni Maryam duk ba wannan ba, ina aka kwana batun kai Humaira wajen Babandi?"
Mami ta sauke ajiyar zuciya gami da ƙara gyara zaman wayar.
"An kashe wannan zancen, gobe zan kai ta. Na fi so a yi a ƙare, na gaji ba zan iya ci gaba da wannan pretending din ba. Idan an hana ta auruwa a tura ta bariki kawai mana ba shikenan ba? Na tsani wannan Fadeel mai baƙin nacin tsiya, Babandi ya tabbatarmin muddin dai bai fice a rayuwarta ba to lallai shi zai rusa komai. Mun kasa jefa mata ƙiyayyarta a zuciyarsa kamar yanda ita muka jefamata, ba na nasa kaɗai ba har na dukkanin wani namijin da zai furta mata kalmar so. Kamar kuma yadda muka yi wa FATIMA har ya zamo silar rabuwarta da Yusuf. A ƙarshe kuma muka zama ajalinta ta hanyar yi mata turen aljani ya kashe ta."
Wannan zancen ne ya yi dirar mikiya a kunnuwan Futuha wacce ta nufo Mami don sanar da ita yanda suka yi da Tasleem, ta tsaya cak a ƙofar ɗakin cikin wani irin kakkarwar jiki da zufa.
Juyowar da Mami za ta yi ta ga mutum tsaye cak a bakin ƙofa, ba ƙarama razana ta yi ba wannan ya sanya ta ajiye wayar cikin rawar murya ta ce.
"Ke kuma me ya kawoki nan?"
Futuha ta karasa shigowa dakin sosai har lokacin bakinta a hangame saboda tsananin mamakin da ya gama baibayeta.
"Mami, duk ke kika aikata waÉ—annan abubuwan?"
Cikin sauri Mamin ta ƙarasa ta rufe ƙofar ɗakin, ita dai Futuha bin ta take yi da kallo har lokacin kamar a ranar ta soma ganinta a duniya. Cikin kausasshiyar murya ta amsa.
"Eh ni ce, na aikata kuma ina kan aikatawar, ina kuma gargadinki da babbar murya! Bar ganin kin fito daga tsatsona na rantse maki matukar kika yi gangancin tonan asiri koda a wurin yan uwanki ne sai na manta da ni na haifeki, zan iya daukar kowane irin mataki muddin dai buƙatana za ta biya."
Futuha ta jinjina kai ta kasa ma cewa uffan don gani ta yi tamkar wata Mamin ce daban a gabanta. Sai kuma ta daure ta hadiye fargabanta ta ce.
"Mami, kenan duk wannan kauna da muke gani kamar kin fi yiwa su Humaira a kanmu duk ba gaske ba ne? Har fa kidnapping din da aka yi naji kin ce ke ce."
Ta juya tana wani mugun murmushi ta karasa ga madubi tana kallon kanta.
"Wawaye, ina ku ka taɓa gani ko ji uwar da ta so ɗan wani sama da nata? Babu ita kaf faɗin duniyarnan. Idan ma akwai toh ni Maryam ba na cikinsu."
Sai ta ƙara sakin murmushi mai haɗe da ƴar dariya.
"Tun auren Yusuf da Fatima, nake ƙunshe da baƙin ciki a zuciyata, kakkarfan shaidar da aka yimin a garinmu da ma makwaftan da muka zauna da su a garin nan kafin rasuwar mahaifina na cewa ina da baƙin kishi kuma har akan kishin ne na taɓa marin (wani ɗan uwana da mahaifina ya so na aura) a bainar jama'a, na zazzagi uwa da ubansa kawai don ya ambatamin sunan tsohuwar budurwarsa kuma yar uwata da aurensu bai yiwu ba yana mai yabonta a kan idanuna. Tun daga wannan ranar ne na fasa aurensa. Ba shi kadai ba, na rabu da mutane da dama saboda kishi, saboda tsanar da na yiwa kishiya, mahaifina ya taɓa neman aure na wanki ƙafa har gidan da ya je nema na ɓata sunansa kuma aka fasa auren. Baƙin shaidar da na samu sanadiyyar zazzafar kishi ya sanya da Yusuf ya shigo rayuwata matsayin saurayin da bai taɓa aure ba, ya shiga zuciyata sosai. Na sa a raina ba zan taɓa nunamasa zazzafar kishina ba saboda a lokacin labarin komai da na aikata a baya ya je kunnensa ta wurin munafukai, wannan ta sanya ya yimin gwaji kala-kala kamar ya yimin wasan yana da mata auren haɗi, yana da budurwa da dai sauransu. Ni kuma na danne bana nuna masa ɓacin raina har sai da ta kai ya ƙaryata zantukan mutane a kaina. Amma fa duk radda ya yimin irin wannan idan na koma gida ranar ko tsinke ba zan ɗauke da sunan aiki ba, kuka kuma zan yi shi. Babu wanda ya isa ya taɓa ni a ranar ya sha. Mahaifina ya rasu dab da aurena da Yusuf. Bayan aurenmu babu irin faɗi tashin da ba mu sha ba saboda rashin kuɗi. Soyayyar da nake yiwa Yusuf ta sanya ban taɓa gujemasa ba daidai da kwayar zarra. Kasuwanci iri iri babu wanda bai yi ba har siyar da kayan miya, gwanjo, da dabino. Kowanne sai an fara rimi-rimi sai lamarin ya ɓaci."
Mami ta haɗe girar sama da ta ƙasa ta juyo tana duban Futuha dake tsaye tana sauraronta ta cigaba da magana.