← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 69 OF 101

Sashe 69

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Nidai ina tare da Babana ne a nan Kano, Mamana asalinta ƴar ƙasar Ghana ce. Toh tana aiki a Misra ne gidan wasu larabawa ne kamar ban dai sani ba. Toh matar ce ta ba wa Mamana aiki kan ta nemo mata wanda ta san zai iya yaɗa labarin ƙarya akan case din Ummita da Humaira kuma itama ba aikinta bane sanya ta aka yi ta nemo wanda zai yi a biyashi. Wannan dalili ne ya sa Mamana kirana ta yimin bayanin komai, nan da nan batare da dogon tunani ba na aminta zan karɓi aikin nan. Tun daga nan magana ta koma tsakanina da ainihin matar da zan yiwa aikin ba Madam din da Mama ke aiki a gidanta ba, ta instagram oage dinta muka soma magana na lura sabon buɗewa ne shafin nata, anan ne ta ke yimin bayani sosai na aikin har ma da ƙara jaddadamin wadannan kudaden da za ta bani. Toh shi ne na shirya labarin na aikamata ta lambar da ta turon na can Egypt ta ce da zarar na kammala na aikamata ta whatsapp, hakan kuwa aka yi nantura mata, sai da ta tabbatar komai ya yi kafin ta yimin umarnin samun lambar da ba a san ni da ita ba na yaɗa. Ta sanya na buɗe shafukan media sababbi da ba a sanni da su ba, har sai da labarin ya yaɗa yanda take so sannan ta bani umarnin rufe dukkan akawun din. Kuskuren da nayi sai na sanar da abokaina su huɗun nan da ku ke gani, suka goyamin baya amma suka ce sai na ba su kasonsu a kuɗin da za'a ban, akan kuɗin mun samu matsala da su. Sai kuma da aka sa kuɗin da ya ninka na aikin da aka bani cewar ana neman wanda ya aikata laifin shi ne suka ci amanata suka fallasa. Kun ji yanda abin ya kasance. Ita kuma matar tun bayan lamarin ta yi blocking dina bayan ta sallame ni. Mamana ta ce kada na ƙara tayar da zancen bisa umarnin Madam dinta, kuma kada na bari Babana ya sani. Sannan ni ko sunan wacce ta sanya ni bansani ba, Maman ba ta taɓa ambatonta da sunanta ba. Wannan shi ne abin da ya faru Yallaɓai. Ku gafarceni."

Fadeel ya dunƙule hannunsa bai ce komai ba, Ridwan ya yi umarni aka mayar da Joshua ma'ajiyarsa sannan ya dubi Fadeel.

"Ita kuwa wannan mene ne dalilinta ko ribarta na aikata hakan? Abu É—aya dai da na fahimta, ko wace ce tana da relation da su biyun nan. Hakanan kawai ba za ta sanya a yaÉ—a rumours akan su ba."

Fadeel ya jinjina kai, tabbas hakane amma kuma shi a iya tunaninsa kamar dai ba su da wani dangi a ƙetare.

"Hakane Yallaɓai. Yanzu mene ne abin yi?"

"Abin yi ɗaya zuwa biyu, zamu karɓi lambar ita Matar da ma Mamansa idan ta kama. Idan binciken zai kaimu har can gidan su Humairar toh sai a je."

"Shikenan hakan yayi. Zan yi waya da Abbansu na sanar da shi komai."

"Ok ba damuwa. Nima nan zamu yi kokarinmu."

Daga haka suka yi sallama Fadeel ya bar ofishin.

***
Ranar sunan ɗiyar Tasleem yarinya ta ci sunan mahaifiyar Hamza wato Asma'u suke kiranta da Husna. Sunan da kusan rigima aka yi tsakanin Tasleem da Hamza don ta rantse sai dai ya sanya sunan nata uwar shi kuwa ya rantse ba zai fasa sanya Husna ba. Hakanan aka ci suna idanun Mai jego duk a kumbure saboda kukan baƙin cikin da ta yi, uwa uba sai ga tsohuwar budurwar Hamzan kuma yar uwarsa ta kawo mata kayan barka. Ta ci uban kyau da rantsetsan leshinta ruwan ƙwai an mata adon stones. Black beauty da ita fuskarnan ta sha make up sai ƙamshi take yi. Bisa shawarar Jannat ne Tasleem ta danne ɓacin ranta sai yaƙe. Tana ji dangin Hamzan na tsokanar budurwa da sunan Amarya amarya amma sam ba su kawo komai ba. Jannat na dariya ta ce.

"Toh kin gani ma ashe ta kusa aure kike wani tada hankalinki."

Sai a lokacin itama Tasleeem din ta ɗan saki ranta. Gwara ta tattara ta yi auren ko ta huta da jarabar bibiyar mijinta da take yi. Futuha kuwa a tsaisaye ta leƙa sunan ta kuma wuce da Humaira da Raihana don su taimaka mata da tattara kaya saboda kaurar da zata yi sai wani rawar kai da ƙafa take yi.

Hakanan suka tattara sannan ta ce su yi gaba a mota a kai kayan tare da su don tuni an kai dukkan kayan katakonta an kuma jera, sai na sanyawarta a jiki suka rage. Wannan duk budurin da ake yi ba ta ga gida ba. Humaira da Raihana suka bi umarninta zuwa gidan, yayinda ita kuwa ta wuce gyaran gashi don ta ce gwara mutan unguwar su ganta tsaf ba raini don Yakubu ya ce mata unguwar Æ´an gayu ne.

***
Ummita zaune ita ɗaya a falo tana biyawa su Muhsin karatun hadda da aka yi musu a islamiyya, haka Mubarak ya shigo ya risƙeta. Kallo ɗaya kawai ta yi mishi ta maida kanta ƙasa tana gaida shi don a yanzun kwata kwata ba ta kaunar ganinsa ba don komai ba sai irin kallon da yake bin ta da shi da kuma manufarsa na soyayyar da yake nuna mata, koda bai furta ba alamominsa sun nuna. Madadin ya wuce sashin Anna wurin Mami kamar yanda Waleed ya sanar mishi cewa tana can, kawai sai ya ɓige da zama a falon yana duban Ummita cike da wani irin kauna mai tsafta ga kuma tausayi.

"Beauty."

Ko kusa ba ta gane da ita yake ba sai bayan ya ƙara maimaitawa. Ta ɗago idanunta fuska ba walwala ta dube shi. Ya yi mata sanyayyar murmushinsa, kamanninsa da Abbansa ya ƙara fitowa.

"Gobe fa zan tafi Camp, baki da labari?"

Ta girgiza kai tana maida hankalinta kan littafi mai tsarki.

"Ban sani ba. Allah ya kaika lafiya ya sa a kammala lafiya."

Ya lumshe idanunsa ya bude da murmushi saman fuskarsa.

"Amin beauty, nagode. Sai dai zan yi kewarki."

Fadin hakan da ya yi hatta Waleed sai da ya dube shi, nan da nan ya daure fuska ya ce su je su cewa Mami ya zo. Suka kuwa mike har su na rige-rige suka bar falon. Ita kuwa Ummita ta kasa cewa komai sai faduwar gaba fat fat.

"Sun watse sun barki ke É—aya ko?"

GyaÉ—a kai ta yi.

"Beauty ba magana?"

Ta dago ta dube shi da idanunta wadanda suka cicciko da hawaye. Ba ta son har abada abin da zai tuna nata da Sahabi wanda tuni aka É—aura aurensa da yar uwarsa.

"Yaya Mubarak, don Allah ka kirani da Ummita. Bana jin dadin sunan da ka sauyamin."

Ya taso ya ɗan yi durƙuso a gabanta.

"Ba zan iya dainawa ba Beauty. Sai dai zan yi kokarin danne abin da ke zuciyata har Allah ya rabaki da cikin jikinki lafiya. Bana son na furta yanzu amma yana nema ya rinjaye ni. Kiyi hakuri da ni zan ƙara danne zuciyata har zuwa lokacin da ya kamata komai ya bayyana a zahiri. I am so sorry."

Wannan karon da hawaye saman fuskarta take dubansa cike da tausayinsa. Bai san masifar da yake shirin jefa rayuwarsa ciki ba. Ban da abin Mubarak me zai yi da ita, Ummitan da sunanta ya gama ɓaci a idanun jama'a?

"Mubarak!"

Tsawar da Mami ta dakamasa ya sanya gaba daya suka dube ta, ranta a tsananin ɓace take dubansu. Ta ɗan jima kaɗan da shigowa falon amma sam ba su lura ba. Kaf kalaman Mubarak din na karshe a kan kunnuwanta ya yi su. Ummita ta sha jinin jikinta da irin duban da Mamin ke watsa musu.*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Duk iyaka kokarin Mami ta kasa danne zuciyarta saboda abu ɗayannan ba za ta iya ɗaukarsa ba, haɗa zuri'a da ɗiyar Jamila wato Ummita. Mubarak ya miƙe yana dubanta hakanan Ummita tun duban farko sai ta yi ƙasa da kanta kirjinta na dukan uku uku don gani tayi ma kamar Mamin cetonta ta yi daga kalaman Mubarak wadanda suke shiga kai tsaye cikin zuciyarta tamkar mashi. Ko kusa ba ta kawo komai ba face kyakkyawan zato ga Mamin.

"Mene ne haka ne? Kar ka kara yimin wannan sakarcin. Ka riƙe abin da ke ranka kuma ka kauda shi don ba zai taɓa yuwuwa ba."

Mamaki ya cika Mubarak, itama Ummita ta ɗan ji maganar a ranta amma kuma ta basar. To me zai dame ta ma tunda dama ita ba soyayya ce gabanta ba? Ita ta fi kaunar ma ta mutu yayin haihuwa ko ta samu shahada ta huta da baƙƙan cikin duniyarta. Mubarak har ya buɗe baki zai ƙara magana Mami ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga mishi hannu.

"Kar ka cemin komai. Fice harkar gabanka, kai da kake da tafiya a gaba mene ne za ka tsaya kana ɓatawa kanka lokaci kana ɓatawa yarinya itama?"

"Ma.."

"Nace maka bana son jin uffan daga gareka ko? Don haka ficemin a nan."

Ya jinjina kai kawai bayan ya kara duban Ummita da aka yi sa'a itama ta ɗago kai suka haɗa idanu ta mayar, sannan ya fice yana ƙara ƙudurtawa a ƙasan ransa in sha Allahu mallakinsa ce muddin dai ta amince da aurensa.

Bayan fitarsa Mamin ta karaso ta zauna sosai a saman kujera har lokacin fuskarta ba walwala ta soma magana.

"Ke yanzu idan ma wani yace maki ki yi soyayya sai ki dube shi? Yanzu ai babu abin da ya fi maki alheri face ki kula da kanki da abin da ke jikinki har Allah ya rabaki da shi lafiya. Ummita na fi kaunar farin cikinki sama da na Mubarak, yau kika biyewa yaron nan sai ya kaiki ya baro. Ni na haife shi na kuma san ra'ayinsa da ma É—abi'unsa, ba shi da ra'ayin auren bazawa.."
Chapter 69 · 0% Book details