Sashe 46
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Kayya Ƙasim, ba dai su ba. Ba su da wannan rawar kan, da ace dai Raihana ka ce shi ne zan yarda. Ni dai jikina yana ba ni akwai matsala."
Ƙasim ya yi shiru, sai ya shiga kiran layukansu amma gaba ɗaya a kashe.
"In sha Allahu lafiya kalau suke. Ku kyautata zato."
Fadin Ladidi jiki a sanyaye. Itama ta rasa nutsuwar zuciya, a wannan lokaci da satar mutum sukutum ba shi da wuya, lallai dole ko rabin awa suka yi hankali ya tashi, balle kuma kusan awanni uku zuwa huÉ—u? Abin dai akwai É—aga hankali.
"Bari nayi sallah."
Mami ta furta gami da miƙewa ta yi ɗaki. Ladidi ma ficewa ta yi kicin don kwashe tuwon da har ya soma kamu yayinda Ƙasim shi ma ya fice a sanyaye zuwa masallaci.
***
Tasleem kuwa, Raihanana ajiye waya suka dube ta ita da Fauziyya da ta maida gidan na Tasleem gidan zuwanta hira da kuma kallo.
Â
 "Meyafaru da su Humairar ne?"
Cikin halin tsananin firgici ta faÉ—amata abin da Mamin ta ce. Tasleem ta yamutse fuska kaÉ—an tana ci gaba da taunar tsamiyar da ke bakinta.
 "Ke yanzu kin yarda ɓatan suka yi kenan? Kika sani ko Ummitan ta yiwa rakiya ɗakin Sahabi?"
Maganar ta dake Raihana, wannan wane irin baƙin ƙazafi ne marar daɗin ji? Ba ta taɓa tsammanin jin makamancinsa daga bakin Tasleem ba musamman ma a gaban ƙanwar mijinta. Fauziyya kuwa ta ce.
Â
"Kai Anti Tasleem, wannan Humairar da na gani dai kamar ba za ta aikata irin haka ba. Ummitar ma ba ta yi kama da Æ´an iska ba."
Sai a sannan ita ta tuna ashe ba su kaÉ—ai ba ne. Don haka ta yi saurin gyara zancenta gami da nuna tarin alhini a saman fuska.
"Hakane, amma kinsan zamanin nan, samarin yanzu Æ´an iska don su hurewa mutum kunne ba komai ba ne. Allah dai ya tsare, ya sa su koma gidan."
Raihana wacce ta lula tunanin inda ya kamata ta kira don jin ko su Humairar sun je ta dawo hayyacinta, firgigit ta miƙe tana fadin.
"Nidai wallahi ba zan iya zama ba ana neman Æ´an uwana, gida zan koma."
A fusace Tasleem ta ce.
"An fadamaki nima ban damu ba ne? Ai daren bai yi ba, kika sani ko napep din da suka shiga ne ya samu matsala? Toh wallahi babu inda za ki je ki jira har sai mun ji ya ake ciki."
Raihana kamar ta yi magana sai kuma ta fasa, a fusace ta shige ciki tana jin kuka na taso mata, ta ina za ta iya nutsuwa alhalin ba a ga ƴan uwanta ba? Fauziyya ganin haka ta miƙe ta bi bayanta, ita kuwa Tasleem da sauri ta bi hanyar da suka yi da idanu sannan a gaggauce ta fiddo wayarta ta rubuta text ta tura kamar haka.
  *_Aikin har ya kammala ne da wuri haka?_*
Tana aikawa aka maido mata amsa.
*_Tukunna dai, wani abun ya faru?"_*
Ta yi shiru ta kasa maida amsar wannan tambaya, jikinta ya É—an yi sanyi. Ita kanta ba ta da tabbacin abin da ke shirin faruwa.
***
 Mami tana jin shigowar Abban falo ta miƙe da sauri har ya dube ta da ɗan mamaki.
"Lafiya Maryama, ya na ganki a rikice?"
Kawai sai ta fashe da kuka. Ya shiga tashin hankalin ganin haka, wannan ya sa shi saurin riƙo hannuwanta.
"Ki samu nutsuwa ki faÉ—amin, meke faruwa?"
Muryarta dakyar take fita ta amsa.
"Kasan na aiki yarannan gidan Tasleem amma babu su babu dalilinsu. Ba su je gidan Tasleem din ba, kuma wayoyinsu gaba É—aya a rufe. Hankalina ya tashi."
Tabbas ya san da maganar amma kasancewar ya shiga tsananin ruÉ—ani ya ce.
"Su wa kenan? Ni ban fahimci komai ba. Wa kika aika?"
"Humaira da Ummita da na ce maka za su je gidan Tasleem kai mata saƙo."
Abba jin haka nan da nan ya soma haÉ—a zufa.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Kun tabbata ba sa gidan ita yarinyar?"
Mami ta amsa ta hanyar gyaÉ—a kai da motsa lebba don sautin muryar ma ta kasa fita. Jin haka Abba ya zari mukullin mota daga shi sai jallabiya sai ko wayoyinsa ya fita yana fadin.
"Ina zuwa." Har ya kai ƙofa sai kuma ya juyo ya dubi Mami.
"Maryama, ki kira dukkan inda kike tunanin za su iya zuwa ki ji ko can suka tafi, ni bari na je ofishin Æ´an sanda na sanar."
Ta kasa magana sai gyaɗa kan da ta yi. Daga haka Abban ya fice. Kai tsaye babban station ɗin mandawari ya je ya yi report ya ba da hotunan su Ummita, ba shi da su sai da ya sanya Raihana ta turo masa. Anan ne itama hankalinta ya kara mugun tashi ta tabbatar dagasken dai an sace su.
***
Raihana ta birkicewa su Tasleem ita lallai a daren take son komawa gida, kuka take yi ba ta jin koda rarrashi, wannan ya sanya ba shiri suka miƙe har Tasleem din suka nufi can gidan a motar Hamza.
 Su na isa Raihana ta faɗa cinyar Mami ta ƙara ƙarfin kukanta. Wannan ya ƙara karyar da zuciyar Mamin, ta dafa Raihanar tana ɗan hawaye. Tasleem ta ƙaraso ta zauna fuskarta ɗauke da damuwar kukan da Mami ke yi ta ce.
"Kiyi hakuri Mami, in sha Allahu za a gansu. Bana tunanin an sace su, idan da hali ku kira Sahabi ku ji ko..."
"Malama ya isheki hakanan! Haba! Da wanne kike so a ji? Da ɓatan su ko kuwa da baƙin ƙazafin da kika ƙokarin yi musu na zuwa wajen saurayi? Ɗazu dama na maki shiru ne darajar Fauziyya, yanzu kuwa daidai nake da ba ki amsa. Ki faɗi muji, tarbiyyar wa kike shakku a cikin su biyun? Ke da kanki a bayan idanunsu kin sha yabon nutsuwarsu, ki dai ji da abin da ke jikinki ba ki zauna zaman ɗaukar haƙƙin mutanen da ba su ɗaukeki yadda ke kika ɗauke su ba!"
Tasleem wacce ta cika ta gama batsewa da wannan kalar maganganun da ta ke musu kallon rashin kunyar Raihana gareta tuni ta harzuƙo za ta soma caccakawa Raihanar zagi sai Mami ta dakamata tsawa.
"Ya ishe ni! Ya isa! Ku marasa tunanin ina ne? Da wanne zan ji ne? Ashe ba kwa hangomin abin da nake hangarwa kaina?! Ba ku hangen ire-iren maganganun da zan sha wajen jama'a sanadiyyar ɓatan yaran amana da nake riƙo? Da ace cikinku ne wa zai ce sakacina ne?!"
Mami na kaiwa nan ta ji kukanta ya ƙaru har da sheshsheƙa, ƙarshe kawai sai ma ta miƙe ta fice zuwa sashin Anna don tana da tabbacin ba ta sani ba.
***
Duhun da É—akin ya yi ne ya sanya suka matsu a gefe guda suka cure jikinsu ga uban sauro da ke yawo a kunnuwa yana kuma cizon fatar jikinsu.
"Humaira, ya zamu yi? Babu ruwan alwala a banɗakin nan da na duba, bamu yi sallolinmu ba. Maƙogwarona ya bushe ƙishin ruwa nake ji."
Ummita ta yi furucin cikin shaƙaƙƙiyar muryarta da ya dashe sanadin kukan da suka sha, itama Humairar wacce ƙishin ruwa da kuma yunwa suka galabaitar gefe guda ga wani fitsari da ya cikamata mara ta ce.
"Ban sani ba Ummita, ban sani ba. Fitsari nake ji amma tunanin wannan banɗakin da muhallin ya sa na kasa yi. Sun bar mu a duhu kamar waɗanda ke cikin maƙabarta, ko a maƙabartar muna saka rai da rahmar Ubangijinmu. Mu cigaba da addu'a, ba zamu rasa mafita daga gareShi ba."
"Toh." Shi ne kawai abin da Ummitan ta iya furtawa, ta koma ta nannaÉ—e a jikin bango ta runtse idanunta tsabar tsoron wurin, cikinta ya É—uri ruwa sosai, ta cigaba da jan dukkan wasu addu'o'in da suka zo bakinta.
Suna a haka suka soma jin muryoyin garada daga waje suna dariya har da kyakyatawa abin babu dadin sauraro. Kafin su tantance komai suka ji alamar buɗe ƙofar, gaba daya suka ƙara ruƙunƙume juna don fargaba. Aka haske musu fuskokinsu da torchlight mai shegen haske, wannan ta sa suka yi amfani da hannuwansu wurin kare hasken sakamakon ƙarfin da suka ji ya yiwa idanunsu da suka jima cikin duhu. Wannan karon matasan ne su ukunsu gaba ɗaya suka shigo.
"Don uwarku ku saki juna, Æ´an iskan banza kawai."
Sun ji ciwon zagin sai dai tsoro ya sa da azama suka matsa gefe, kowaccensu babu inda jikinta ba ya rawa. Shi ne dai baƙin azzalumin na ɗazun.
"Wizzy, a ina aka kwana ne?"
Anan suka ji ashe sunansa Wizzy, ya watsawa mai maganar mugun kallo.
"Kai Babba, don't kawo yaawa mana. Ka yi everything a muhallinsa mana ok? Here is not good to ce wani abu. Sai mun go out."
Wanda aka kira da Babba ya amsa da.
"Na fahimta Oga."
Daga haka Wizzy ya yo gaba ya dan sa ƙafa ya shuri Humaira.
"Ke gwanar na iya, koda wasa wallahi ki ka kara try din zagina sai na kasheki na yi killing banza! Kuma a nan za ku zauna har sai mun gama sanin makomarku! Badboy, a ba su abincin da ruwa, ka ajiye musu fitilar ba don halinsu ba shegu."
Yana kaiwa nan ya sa kai ya fice yana ba wa Babba umarnin ya biyo shi su yi magana. Shi kuwa Badboy ya ajiye musu leda da ruwan sha na purewater sinƙi guda, sai kuwa fitilar daga nan ya fice ya garƙame ƙofar. Da sauri Ummita ta jawo ruwan hakanan itama Humaira, suka sha suka yi kat, daga nan haka suka daure suka kama ruwa a banɗakin ba don suna so ba, suka yi alwala, ɗankwalayensu suka mayar darduma, suka yi sallah.
Humaira ta yi shiru ta zuba uban tagumi tana ɓarin hawaye, Ummita ta jawo ledar, shinkafa da miya ne garau garau.
"Ke kika ce kina jin yunwa É—azu, ki daure ki ci."
Ta É—an dubi abincin sannan ta dubi Ummita ta girgiza kai.
"Ba zan iya ci ba Ummita, innalillahi wa inna ilaihir raaji'un, haka za mu yi ta zama tare da waÉ—annan azzaluman? Yanzu nan wurin zamu kwana? Su Abba na can hankalinsu a tashe Ummita. Wayyo Mami."