Sashe 37
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Uhm." Shi ne amsar da ta ba ta. Fadeel kuwa lumshe idanun ya yi ya ji sautin Uhm din har tsakar kansa, gaba ɗaya sai da ya ji tsikar jikinsa ya tashi. Kamar kuma haɗin baki sai ga gidan rediyon sun saki waƙar Breaker mai taken Kalmar So. Humaira sam hankalinta ba ya jikinta, ji take kamar ta buɗe motar ta dira a cikinta. Gaba daya koina a jikin rawa yake, Ac ke kaɗawa a motar amma ita zufa take. Ta tuna da ambaton Allah ba shiri ta shiga ambata a ƙasan ranta a hankali ta soma dawowa cikin nutsuwarta.
A bangaren Ummita da Ibb, hira suke ɗam taɓawa kaɗan, shi kuwa Gogan da Humaira ba ka jin komai daga bakinsu, babu kamar Fadeel da yake jin waƙar ta zo daidai da yanayin da yake ciki. So yake ya tambayi ya take? Ya lamuran rayuwa? Ba ta hakura ba har yanzu? Ba ta amince ya turo iyayensa ba? Sai yaushe? Amma ina! Babu ko kalma ɗaya da yake jin zai iya furtawa, ba ya fatan rabin shekarar da ya kusan cinyewa ya tashi a banza balle ya ga shekarar ida da rai da lafiya, wannan ya sa yake takatsantsan ya kuma jure bai ƙara kallonta ba tunda ko ya kalli side mirror ba ya ganin komai face danshin ruwan dake kwarara sai ko hasken fitilun motocin dake saman titi.
Har suka iso gidan ba ka jin uffan daga Fadeel, shi kansa Ibb sanin halin mutumin ya sanya bai takale shi da hira ba ko sau ɗaya. Ya dai san yau Humaira ta fama mishi inda yake mai ƙaiƙaiyi.
"Ko mu karasa da ku har cikin farfajiyar?"
Wannan kalmar ya sa Fadeel cire gilashin idonsa, ya dubi gidan su Humaira, wato har an iso kenan.
"Aa, mungode sosai. Bari mu karasa ciki."
Cewar Ummita. Humaira kuwa har ta kama ƙofar ta bude, amma ina, iska mai karfi da ruwan da ya fesomata ya sa dole ta koma ta rufe. Fadeel ganin haka ya juya bayan, sai a sannan ya kara kallonta ido cikin ido, da sauri ya dauke idanunsa ya dan kai hannu baya ya dauko lemar dake ajiye a wurin. Fitowa ya yi ya buɗe lemar, babba ce don ta fi ta Ummita girma, Ummita kam tuni ta fita itama ta bude nata lemar da ba zai ishe su ba su biyu koda a dazun ne. Kofar Humaira ya bude gami da miƙamata lemar. A sanyaye take dubansa.
"Karɓa mana Humaira." Ibb ya furta, ta kalleshi.
"Mungode sosai, Allah ya kiyaye hanya." Daga nan ta fita, sai ya kasance su biyun a ƙasan lemar. Kan Fadeel a ƙasa ba ya son kallonta gudun ɓarowa kansa aiki, ta sa hannu ta karɓa sannan ta dan ja baya kaɗan.
"Idan na shiga zan aiko a kawo."
Murmushi ya yi mai kyau har a sannan bai kalleta ba ya amsa da toh. Daga haka ya fice ya koma cikin motar ya rufe. Ita ma ta nufi kofar da gudu-gudu.
"Muje."
Ba musu Ibb ya yi reverse ya juya kan motar suka bar layin. Ƴar dariya ya yi.
"Fadeel kana son Humaira."
Fadeel bai iya kallonsa ba ballantana ya samu amsa. Ya kara cewa.
"And you know what? Kun dace sosai."
Nan ma bai kalleshi ba sai dai ya yi murmushi. Ganin ba ya son magana ne ya sa Ibb rabuwa da shi.
***
A can kuwa Humaira na shiga ta bada lemar a miƙa musu, ɗan aike ya dawo ya ce babu kowa a wajen, ta karɓa a sanyaye ta shige ɗakinsu da shi. Madadin ta karasa ciki sai ta ajiyeshi a ɗan gefen don ya sha iska. Suka sauya kayan jikinsu saboda jiƙewar da suka ɗan yi. Ummita ta ɗauro alwala sannan itama ta ɗauro, koda ta idar da sallah kwanciya ta yi saman dardumar don kanta har lokacin sarawa yake yi kamar jijiyoyin kan nata za su tsinke. Tuna Fadeel kaɗai yana haifar mata da rawar jiki da ciwon kai, daga haka kuma sai ta ji kamar ana mata ihu a kunne. Kafin ka ce wannan sai ga Humaira ta soma kuka sosai. Ummita da ke kwashe jiƙaƙƙun kayansu ta juya da sauri ta juyo. Allah ya taimaka su kaɗai ne a ɗakin ta roƙi yanmatan akan su fita ta gyara don sun yi kaca-kaca da shi. Tuni ta fahimci matsalar jinnunta ne, ta sha mamaki ma da bai tashi a mota ta yiwa su Fadeel rashin mutunci ba.
Da sauri ta fice zuwa kicin, can baya ta zagaya inda ake dora babban tukunya a icce saboda yawan da aka yi. Garwashi ta zuba cikin kasko ta dauka da sauri gudu-gudu ta nufi dakinsu. Mami dake kokarin shiga kicin don ganin kwandunan kayan miyan da Abba ya ce an kawo na girki ta tsaya cak hankalinta ya yi kan Ummita wacce ke tafiya kamar wani abu ya faru. Da sauri ta bi bayanta.
Ita kuwa Ummita, tun cikin babbar sallah da ta je Bichi ta karɓowa Humaira hayaƙi a wurin ɗan uwan mahaifiyarta hakan yasa Humaira na fara kuka ta yi niyyar turara mata. Abin mamaki har ta isa yanayin kukan Humairar bai sauya ba. Ta ciro maganin ta barbaɗa cikin kaskon ta ajiyeshi kusa da Humaira. Nan da nan kanta ya soma juyawa. Daidai lokacin Mami ta faɗo ɗakin. Abin da ta gani ne ya sanya ta kallon Ummita,
"Lafiya? Meke faruwa da Humairar? Wannan wane irin hayaki ne kuma?"
Ummita ta sha jinin jikinta don gaba daya ba ta sanar da Mami ta karɓowa Humaira hayaƙi ba.
"Ba komai Mami, kukan nan ta soma wanda take yi idan aljanunta suka tashi shi ne.."
Mami ta daka mata tsawa.
"Shi ne me?! Shi ne kike yi mata hayaƙi ba tare da kin sanar da ni ba? Haba Ummita, yanzu idan Abbanta ya ji wa zai yiwa faɗa? Maza ɗauke hayaƙin nan."
Ummita ta dauka ta fitar zuwa bandaki ta kashe, ta sani ta yi kuskure amma kuma cikin ikon Allah Humaira ta yi shiru sai gumi take haÉ—awa da alama kuma bacci ya É—auketa.
Ummita ta kai duba ga Mami, zuwa lokacin tana zaune gefen gado.
"Ki yi hakuri Mami."
Girgiza kai Mami ta yi.
"Ba laifi kika aikata ba Ummita, na sani kulawa ce da yar uwarki, amma ko mene ne ya dace na sani saboda nima ina nawa kokarin a kanta don har na yiwa Abbanku maganar wani mai bada magani zan kai ta wurinsa bayan biki ya ga mece ce matsalarta."
GyaÉ—a kai Ummita ta yi tana murmushin farin ciki. Ba ta da fatan da ya wuce ta ga Humaira ta samu lafiya ta amince da auren mai kaunarta irin Fadeel.
"Toh Mami. Allah ya sa a dace."
Mamin da murmushi ta amsa da amin. Har ta mike ta kai ƙofa ta juyo.
"ÆŠaukomin maganin da kike turara mata, idan ya so sai na yi mishi bayani."
Ba musu Ummita ta É—auko ta ba ta, murmushi ta yi ta juya ta fita a dakin.
***
BIKI BUDURI....
®ï¸Rufaida Umar.*LITTAFIN NAN NA KUÆŠI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
Yau ranar ta kama ranar Kamun ƴanmatan Mami, Futuha da Tasleem. Tun safe Humaira ba ta zauna ba, tana tsaye akan aikin suyar snacks da aka haɗa tun ana saura kwanaki biyu aka sanya a firij, sai da aka ci rabin aikin kafin ta bar wurin bisa umarnin Mami acewarta yanda ta kwashi gajiyarnan gwara ta je ta huta kafin lokacin da za a tafi event center da aka tanada don Kamun. Haka ta karasa ɗakinnasu a mugun gajiye tana jan ƙafafunta da suka yi tsami. Hayaniyar ƴanmatan dake ɗakin ko kaɗan bai mata ba, ji ta yi da ace tana da hali da kaf sai ta sa an fice an bar ta ta huta. Hakanan dai ta karasa tana amsa sannun da wasu ciki ke mata tana murmushin yaƙe. Ummita tun safe ta raka Anti Jannat ƙunshi har lokacin ba su dawo ba. Ita dai daga wannan kwanciyar tana jira ta a fito daga bandaki ta shiga wanka, ba ta san ya aka yi bacci ya yi awon gaba da ita ba.
 Ba ita ta farka ba sai da aka kira sallar la'asar, nan ɗin ma Raihana ce ta tashe ta.
"Kai, har kin ban tsoro. Kin fa jima kina baccin nan tun É—azu nake safa da marwa ba ki tashi ba."
Humaira dake dubanta da manyan idanunta da suka kaÉ—a suka yi ja ta ce.
"Har an tafi ne?"
Harararta ta yi.
"Jimin ke É—innan, an tafi ne za ki gan ni anan? An dai soma kwalliya da shirin tafiya. Ki tashi kiyi sallah ki wanka mu tafi lar mu makara."
"Ina kuma za mu je?" Humaira ta tambaya da mamaki. Sai kuma don kanta daga yanayin kallon da Raihanar ta jefamata ta tuna.
Ta gyaɗa kai tana hamma da miƙa lokaci guda.
"Oh na tuna, kin ce wajen kwalliya za mu je ashe. Toh ita Ummitar ta dawo?"
Raihana da tuni ta miƙe ta hau fiddo karamin akwati da zummar daukar sarƙa ta amsa da eh. Ji tayi kamar ta rufe Humairar da duka, dama dakyar ta amince za ta yi kwalliyar. Ba ta kara bi ta kan Humaira ba, itama ganin haka sai kawai ta ja zani ta faɗa banɗakin. Ranta ya ɓaci ganin yanda aka yi kaca-kaca da shi, ba ta iya wanka ba sai da ta wankeshi tas har Raihana na kwankwasa kofar tana mitar ta san wankin bandaki take tayi biris da ita.