← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 47 OF 101

Sashe 47

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

Kawai sai ta sa kuka hakan ya sa Ummita itama da take danne nata sai kawai ta sake shi. Wannan karon ma babu mai rarrashinsu, su suka gaji suka yi shiru sai faman sheshsheƙa.

***
KAMAR WASA...

®️Rufaida Umar
     *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Kamar wasa, ƙaramar magana ta zama babba. Babu su Humaira ba labarinsu har aka yi kwanaki biyu, wannan ya ƙara tayarda hankalin iyalan gidan sosai. A ranar ne kuma Jannat ta diro gidan, labarin ɓatan yana risƙarta ta hau buga salati, cikin sanyin jiki ta ce.

"Koda ace ba na kaunarsu, bana murnar ɓatan su. Allah ya sa a gansu."

Mami ta amsa da amin, Raihana kuwa ba ta um bare um um a kwanakin nan sai kallon kowa da idanu. Tasleem itama dai tana gidan ba ta koma gidanta ba, Abba ne ma ke faɗan zamanta acewarsa zaman ko rashinsa ba shi zai sa a gansu ba. Wannan yasa a ranar ya ba ta umarnin tattarawa ta tafi. Jannat ce ta ce za ta kai ta tunda Hamza ya tafi ofis. Anna kuwa nunawa tayi ko a jikinta, cewa ta yi ba ta yarda ma da batun ɓatan ba, ta fi tunanin dai wani yawon nasu suka je za su dawo. Babu wanda ya ce mata komai a wannan bahagon tunanin nata. Zancen dai zuwa lokacin ya yaɗu har gidajen rediyo da social media inda Raihana ta ɗora hotunansu a dukkan shafuka tana mai tagging shafin Humaira saboda abokan kasuwancinta su taya ta yaɗawa.

***
*_Tafkeken fili ne babu gida gaba da baya, tafiya kawai yake yi yana jefa ƙafafunsa yana faman kwala kiran sunan Humaira ga wani irin baƙin hadari da ya cakuɗe a sararin samaniya sai walƙiya dake haskawa akai-akai har bai ankara ba ya cimma ƙarshen hanyar yana shirin afkawa ƙaton ramin dake a gabansa ya ji an riƙo hannunsa da ƙarfi. Juyawa ya yi yana mai duban mai shi, wata mace ce dattijuwa fara tas, tana sanye da farin hijabi har da na hannu, komai na tufafinta fari ne ƙal. Hawaye ne kwance saman fuskarta ta ce. "Ka taimaka ka ceci rayuwar Humaira, tana cikin hatsari. Ka kularmin da ita. Duk runtsi kar ka rabu da ita. Alheri ce a gareka." Zuciyarsa ya ji ta tsinke, ya dawo da baya murya a sama ya ce "Ina Humaira ta ke?" Kawai sai ta nuna masa ramin dake gabansa, Humaira ya hango saman wani ƙaton dutse a kwance gaba ɗaya gaɓɓanta an sanya wasu sarƙoƙi an ɗaure ta tamau. Sannan ya maida duba ga Matar shima lokacin hawaye yake. "Ba ta sona, ba za ta amince na taimake ta ba." Matar karo na farko ta yi mishi murmushi "Kaf duniya babu matar da za ta so ka sama da Humaira. Tana sonka, ka bata lokaci ka zama mai hakuri." Tana kaiwa nan ta saki hannunsa ta soma tafiya da baya tana cewa "Ka ceci rayuwarta daga hannun azzalumai. Ina roƙonka a matsayina na mahaifiyarta._*

Yana kai wa nan ya soma jin kiraye-kirayen sallar asuba a kunnensa, firgigit ya farka ya miƙe zaune yana ambaton Allah. Na'urar sanyaya jikin dake aiki bai hana zufa wanke mishi fuska da jiki ba hakan ya sanya shi saurin yaye bargon yana ajiyar zuciya kamar wanda ya yi tseran gudu. Kansa ya ji yana sarawa, wannan wane irin mafarki ne kuma? Wace ce? Meke faruwa da Humairar? Kwana biyu kenan rabonsa da duk abinda ya shafi social media balle ya samu damar magana da Raihana ko tambayar lafiyar Humairar, hakan kuma ya faru ne sanadiyyar ayyukan ofis da suka yi mishi yawa saboda shirye-shiryen tarbar baƙin ƙasar waje da suke yi a kamfaninnasu. Addu'a ya yi sannan ya miƙe jiki a saluɓe gabansa har lokacin na bugu da ƙarfi yana jin kamar ya kira wayar Humairar a sannan ya ji ko za ta amsa. Hakura ya yi ya shiga ya ɗora alwala ya zura jallabiya ya fice zuwa masallaci. Koda ya dawo wayarsa kawai ya ɗauka, ba ya jin zai iya haƙuri da kiran Humaira koda ace hakan na nufin rusa tsawon jiran da ya yi, ya gaji zai tunkareta kawai da batun aure. Zantukan matarnan da ya gani cikin mafarki da kuma yanayin da ya ga Humairar sun fi komai ɗaga mishi hankali duk da yana kyautata zaton alheri ne mafarkin.

Ya kira ya fi sau uku amma amsar É—aya ce, a kashe. Don haka ya yanke shawarar kiran Raihana, shi dai babban burinsa jin muryar Humairar.

Ko ringing uku wayar ba ta yi ba ya ji Raihana ta É—aga a gaggauce. Sallama ya yi mata ta amsa.

"Ina son jin muryar Humaira, ki haÉ—a ni da ita please."

Kawai sai ya ji ta fashe masa da kuka wanda ba ƙaramin rikita shi ya yi ba.

"Me ya faru?! An yi wani abun ne? Ki faÉ—amin."

Gaba ɗaya ya ruɗe, nan take sanar da shi ai kwanaki uku kenan babu Humaira da Ummita balle labarinsu ta kuma ƙara da cewa.

"Abin damuwar shi ne ba a san su waye ba, idan kidnappers ne, ai za su kira su ce a ba su kuɗin fansa, waɗannan kuwa babu kira ba.." Maganarta ma ta kasa fita sakamakon kukan da ya ci ƙarfinta.

"What nonsense! Takardu da za a ce kawai sun ɓata? Kar ki rainamin hankali mana!"

Daga yanayin yanda yake zancen ma ka san a ruɗe ya ke. Cikin nutsuwa ta labarta mishi duk yadda komai ya faru har da batun cigiyar da aka sanya a jiya a gidajen rediyo da ma hotunan Humairar duk da ta ɗora a media. Ta ƙara da faɗin.

"Ka taimake ni Yaya Fadeel a nemo su, wallahi ba zan iya rayuwa ba idan babu su. Jinin jikina ne."

Idanunsa suka kaɗa, ya ji wani maƙoƙon abu ya tokare masa a ƙirji, ga kansa da ya yi mugun sarawa, bai iya cewa komai ba ya datse kiran. Zama ya yi dabas a ƙasa har lokacin yana riƙe da kansa da yake ciwo tamkar zai fashe. Ashe dagaske mafarkinsa ne zai tabbata? Humaira na cikin tashin hankali?

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Ya furta a fili. Kafin wayewar gari tarr jikinsa ya É—auki tsananin zafi, amma hakanan ya daure ya É—aga wayar Ibb wanda shima ya ci karo da hoton Humaira dake yawo a media. Hankalin Ibb tashe ya ce.

"Fadeel ka ji labarin abin da ya faru da Humaira?"

Shiru ya kasa ba shi amsa sai wasu irin zafafan hawaye da suka kwaranyo saman fuskarsa. Ya runtse idanu, fatansa bai wuce ace mafarki yake yi ba, inama duk abin da yake ji yanzun a mafarkin ne.

"Fadeel, are you ok?"

Ibb ya ƙara tambayar jin ya yi shiru. A sannan ne ya soma magana dakyar haƙoransa har su na bugun juna saboda wani mugun sanyin da yake ji.

"No Ibrahim, i am not, Humaira rayuwata ce. Ibrahim ka taimakamin, ina tunanin mutuwa zan yi."

Yana kai wa nan ya ajiye wayar shi bai kashe ba, shi kuma bai ƙara sauraron abin da Ibb din zai faɗi ba , yana ta faman Hello hello amma shiru kake ji.

Yana nan kwance ya dai ji shigowar Alhaji dakin amma daga nan bai ƙara sanin inda kansa yake ba. Alhaji wanda ya samu waya daga Ibb a gigice ya tallafo shi ya hau kiran sunansa, Anti Amarya itama faɗowa ciki ta yi sanye da hijabinta har ƙasa.

"Ya kamata a tafi asibiti."

Jin abin da ya fito daga bakin Anti Amarya ya ankarar da shi abin da ya kamata ace shi ya ya yi wannan hankalin. Ya ba ta umarnin ta sa a fiddo mota yayinda shi kuwa ya taimaka da kama Fadeel suka fita.

Murja da ta ji hayaniyarsu daga farfajiyar gidan ta fito daga É—akinta tana murza idanu daga ita sai riga da wando na bacci ko sallah ba ta yi ba. Suka yi karo da Anti Amarya da ta shigo sauya sutura don ta bi bayan su Alhajin a wata motar.

"Anti meke faruwa?"

"Fadeel ne ba lafiya."

Nan da nan ta ji tashin hankali, sai kuma ko me ta tuna kawai ta danne damuwarta. Wani abu ya tokare kirjinta kawai sai ta ce Allah ya ba shi lafiya, daga haka ta juya ta koma ɗakinta fuskarnan kamar an aikomata da saƙon mutuwa. Sai da ta dubi ƙofar shigowa ɗakin ta tabbatar babu mai tahowa kafin ta ɗauki waya ta danna kira sau uku ba a ɗaga ba, ƙarshe kawai sai ta aika da saƙo kamar haka.

*_Lokacin aiwatar da aikin ya yi. An tafi da shi asibiti yana cikin halin rashin lafiya kuma bana raba É—ayan biyu a sanadinta ne._*

Iyakar abin da ta rubuta kenan a saƙon ta tura zuwa lambar da ta yi saving da suna BLANK. Ta koma ta zauna gefen gado tana murmushin da ita kaɗai ta san ma'anarsa kafin ta ƙara fiddo wayarta ta lalubo saƙon da aminiyarta Saddy ta aikomata na labarin ɓatan Humaira da kuma hotuna. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ɗaga yatsunta biyu a kan hoton Humaira gami da girgiza kai ta ce

"Good bye Humaira, daga yanzu kin fita daga rayuwar Fadeel, fita na har abada."
Chapter 47 · 0% Book details