Sashe 99
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Sha'anin matanka da komai na su ka sanyani shiga ciki, na shiga saboda ina yi maka kara, lokacin da za ka auro Rabi'atu ka yi abubuwa ba domin na kauda kai ba da ba za mu kawo yanzu ba, ka aurota ka ce na ja ta a jikina na bi umarninka, in ba domin kai ba ita ta isa ne? Ba ta isa ba amma saboda ina yi maka kara bana daga kai akan komai da kake yi mini a cikin gidan nan, ita kanta ta sani bana kishi da ita kamar Jidda na ke kallonta amma ita ka tambayeta ni kamar uwar jidda take kallona?? Ka bata dama tana cin kasuwa a kaina, duk bai isheka ba sai kaima ka zo ka ci kasuwar ka a saman kaina? Komai ya taso na matanka sai ka danganta shi da ni? Ina ruwana a ciki? Na san an yi? Ba sai da suka yi faÉ—ansu sannan salima ta zo ta faÉ—a mini ba? Ka ce na yi son kai na shigar ma Gimbiya saboda muna tare, ka ce mun taru za mu kashe maka mata, Yusuf kai kake faÉ—in haka? Da bakin ka? Yau ko ba auran ka a kan Gimbiya ya dace Rabi'atu ta yi faÉ—a da ita? Sa'arta ce? Balle tana gaba da ita a shekaru, tana gaba da ita a wajenka da gidan nan, in har ina da mutumci da daraja a wajenka ya dace a gaban matanka ka kirani kana yi mini ihun cewa ban yi adalci a kan matanka ba? Ya dace? Me kake nuna musu? Ban da daraja kuma cewar da kake yi ni ce wakiliyarka duk karya ce tun da kalamanka na yanzu sun bayyana yadda ka É—aukeni."
Na dakata ina sauke numfashi, saboda ina mgana ne zuciyata na zafi saboda bacin rai murya ta har ta dishe saboda kuka.
"Sadiya ki bar mganar nan ki yi hakuri kin ji ko?
Yallaɓai ya faɗa cikin lallashi har yana tasowa zai rikeni na matsa baya ina mai ɗaga masa hannu lokaci ɗaya ina faɗin.
" Ba mganar hakuri ba ne, hakuri ai na yi shi da ban yi ba, da ba ka ganni zaune a gidanka ba. Da a ce ina riƙe da irin cin kashin da kake yi mini na rantse da Ubangijina da tuni wata rana ka wayi gari ka ga bana cikin gidan ka.
Kawai ina so ka san cewa kawaici na ke yi maka, kuma shi ne kuskure na, yau da ban nuna maka zan É—auka ba, da duk wannan cin mutumcin bai biyo baya ba."
"Don Allah ki yi haƙuri."
Ya faÉ—a cikin lallashi kamar zai yi kuka, ashe karyan iskanci ne abin na shi.
"Ki yi hakuri Maman Jidda."
Gimbiya ta faÉ—a jiki a sanyayye.
"Ki yi hakuri."
In ji Rabi'atu ita kanta jikinta ya yi sanyi.
"Ba komai ni ce na yi sakacin da komai ma ya faru. Ni na sabama Yallabai da hakan shi ya sa ba ya jin shakkar yi mini ihu akan matan shi, amma ina so ku sani daga yau sai yau, ba ruwana da abin da ya shafe ku, kai ma kar ka kara sakani cikin sha'anin matanka, mganar ni ce wakilayarka ba ta, gida na ka ne dukkanmu muna karkashinka ne, kar ka sake kirana akan su ko ka ce za ka yi mini ihu ko ka faɗa mini mgana nima ba zan sake shiga hurumin su ba, duk kawaicin da na ke yi maka na daina domin na fahimci baka daraja haka."
Ina gama faɗin haka na juya da gudu na bar falon ina jin sa ya biyo ni yana kiran sunana ban jiyo ba sai da na fita haraba na saita kaina har na kai bangarena duhu duhu na ke gani saboda bakinciki, ina shiga na kulle kaina a bedroom ina ta kuka, ya zo ya yi bugu yana yi mini magiyan na buɗe ban buɗe ba, har Gimbiya ta so itama da magiyan na yi hakuri na buɗe itama na yi mata banza Baby ta zo tana kirana da Umma ki yi hakuri ki bude itama na yi mata banza, har Jidda dake makaranta ina jin Ubanta ne ya kirata ta yi ta kirana a waya ban ɗauka ba, kukana na sha, har na koshi sannan na lallashi kaina da alƙawarin Yallaɓai ya gama cin kasuwa kaina in dai akan matan shi ne.
Sai da safe na buÉ—e kofa na fito fuska a kumbure, Yumna da Baby suna rige rigen gaisheni fuska ba yabo ba fallasa na amsa, ba su zauna ba suka shirya direba ya kwashe su zuwa Tahfez tun da jiya ba su samu zuwa ba.
Tea kawai na sha, na koma falo na kwanta, da na kuma san Yallabai zai shigo mini da ɗaki zan koma amma sai ya ritsani, Yallaɓai duƙa mini yayi har ƙasa akan gwiyoyinsa
yana bani hakuri faÉ—i yake yi
"Ki yi hakuri Sadiyata. Wallahi na san ina yi miki wasu abubuwan na kure hakurin ki amma baki taɓa mgana ba. Na sani kina yi miki kara da kawaici ban kyauta ba don girman Allah ki yafe mini."
"Ai da ba yafiya Yusuf da ban sake kallonka ba, da ban sake ba ka wata dama ba
kawai ka kiyaye kar ka ƙure ni na yi abin da ban saba ba."
"Ba zan kure ki ba in sha Allahu. Ki yafe mini Sadiyata"
Duk yadda ya so bai ga dariyata ba, da gaske na ke yi na daina yi masa alfarma kuma ya san haka shi ya sa ya ruÉ—e, bayan fitan shi sai ga Gimbiya itama hakurin ta yi ta bani.
"Ba komai fa, abin da ya wuce, wani abun ai da ba a hakuri da ba a kawo wannan matakin ba maman khalipa"
Itama Rabi'atu ta zo tana bani hakuri itama na ce mata ni ba komai, domin in da ban yi hakuri ba da ba ta zo ta iske ni ba, tun daga ranar na tsame kaina daga sha'anin Yallaɓai da matan shi, kuma daga lokacin na samu sauki daga shi har matan na shi suka fara shakkata domin gabaɗaya na dauke musu wuta, ashe da gangan ne Yallabai ke yi mini wulakanci sai da na buɗe bakina na yi mgana na fahimci yana sane da abin da yake yi, tun daga ranar na shata masa layi sai na zauna lafiya ya kiyayeni suma suka kiyayeni, kuma abu in dai ya shafeni yana rawan jiki, suma haka matan na shi, saboda yadda na fidda kaina daga duk abin da ya shafe su na gyara kuskuren da na yi sakaci tun farko.
Aka ce mai hali ba ya fasa halin shi, ya riga ya saba da kwaso mini ko wata mgana amma yanzu da ya zo ya fara, kallo kawai in na yi masa zai shiga taitayinsa, in ma ban kalleshi ba, banza na ke yi da shi har ya gama ɓaɓatun shi kanzil bana cewa, in ya gaji sai ya ce Sadiya ta ba ki ce komai ba! In ma na ɗago na yi masa wani sakaran shi da kan shi ya ke kama kanshi ya tashi yana kame kame, wallahi aure bauta ne ba domin bautar ubangiji ba da Yusuf bai isheni kallo ba wallahi. Shima ganin yanzu ya fita zuciyata shi ya sa duk wani abu na kyautatawa ba wanda ba ya yi mini. Ni ce wai Yallaɓai ke yi ma tsaraba in ya fita bini bini Sadiya ta ko kina son wani abu? Kafin na yi mgana ya yi mini alheri jikinsa na rawa da zuciyarsa a kaina ni ko bai san na riga na gama sanin shi ba ba kuma wani yaudaran da zai zo da shi ya sake ruɗata. Ni dai tun da sun kiyayeni daga shi har matan shi shike nan na samu salama da zaman lafiya.
*****
*BAYAN SHEKARA ÆŠAYA DA RABI.*
NOVEMBER.
2025.
Alhamdulillah Rayuwa ta miƙa Ubangiji ya ara mana dama. Ya ba mu rai da lafiya sannan ya azurtamu. Ba abin da za mu ce sai godiya ga Ubangijin mu. Yau da jiya da gobe ba su bar komai ba tun muna kirga kwanaki mun koma na wattani ga shi muna kirga shekaru ashirin da huɗu cikin na biyar da auren na da Yallaɓai. Rayuwa ta zama sai godiya kawai mun faro gwagwamarya kuma ba za ta kare ba har mu koma ga Allah amma dai muna fatan ko da yaushe mu yi kokuwa da matsalar mu mu ga bayan ta ba wai ace ita ce za ta ga bayan mu ba.
A halin yanzu shekaruna na haihuwa arba'in da biyar Yallabai kuma girma ya zo an gangangara gidan hamsin da biyu har da É—oriya. Rayuwa ba za ta koma jiya ba sai ta yi ta gaba kana karuwa a fuskantar yarintarta ka. shekarun mu sun mika amma kuma mun samu wadatar rayuwa sai godiya. A shekara É—aya da rabin da suka gabata abubuwa na alheri da aka sin sa duk sun faru amma na alherin da farincikin sun fi yawa.
Gimbiya ta haihu ta samu yarta mace ta ji sunan Hajiyar Tafida. Ahalin yanzu ma Rabi'atu ta na da ciki kimannin wattani biyar. Tuni har ta yaye yan biyu tun da suna cikin shekaru na biyu ne. A gidan Yallabai tsakanin Gimbiya da Rabi'atu ne ake gasan haihuwa da kishi ni kam na koma gefe na zama Umma, sai dai na ba da shawara ko na raba in na ga abin da bai kamata ba.
Na yarda na amince ina da wani hali da ba zan iya barin shi ba, duk yadda na kai ga kauda kaina ga sha'anin Yallaɓai da matan shi in na ga abin da bai kamata ba, ba na iya shuru sai na tanka, na ɗauki hakan a matsayin hallita ce ta Ubangiji, ba ni da riƙo sannan kyakyawan zuciyata ba ta barina na daɗe ina jin haushi wani a cikin zuciyata.