Sashe 97
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban É—auka lamarin ya lalace haka ba ni da ta ce suna faÉ—a na É—auka cacan bakin da suka saba ne, ashe ashe abin ya yi muni ko da na shiga bangaren Gimbiya a tsakiyar falon ta na iske Gimbiya kan ruwan cikin Rabi'atu tana kilarta, Rabi'atu na kuka tana neman É—auki Gimbiya ko maruka take kai mata lokaci É—aya tana faÉ—in.
"Don ubanki na yi miki kama da sa'arki ce? Ni za ki ja da kokuwa? Yau sai na nuna miki bambamcin aya da tsakuwa."
Da gudu na yi kan Gimbiya ina salati ina ƙokarin ɗagata amma tana fizgewa.
"Subhanallah. Gimbiya me ye haka? Don Allah É—agata haba mana."
Amma ba ta jini ba kai mata duka kawai take yi itama bakin Rabi'atu bai mutu ba.
"Allah ya isa muguwa, an ja ki da faÉ—an ke din banza."
Sai da na ce Salima ta matso tare da ita muka samu muka É—aga Gimbiya daga kan Rabi'atu.
"Haba Gimbiya me ya kai ki yin dambe da Rabi'atu? Ba girman ki ba ne wallahi sannan kar ki manta ba ke kaɗai ba ce fa."
Na faÉ—a ina rike ta, tana haki ta fizge hannunta tana gyara wuyan riganta.
"Bar ni Maman Jidda, yadda yarinyar nan ta raina ni gwara da nuna mata ƙyaleta na ke yi amma ba ta fi ƙarfina ba."
Lokaci É—aya tana hararan Rabi da Salima ta taimaka mata ta É—agata.
"Me ya faru ne? Ke Rabi'atu me ya sa wai ba ki jin mgana ne?
Kawai sai ta fashe da kuka tana faÉ—in" Ai ita ce ba ta da gaskiya daga na zo ina mata mgana shi ne ta shiga zagina."
Gimbiya ta tare ta da faɗin" Maƙaryaciya. Yarinyar nan yar bariki ne,"
"Wai me ya haÉ—a ku ne?
Na fada ina katse su saboda na gaji da hayaniyarsu.
"Kan turaka dai Maman Jidda, shekaranjiya da zan karbi girki haka na iske shashen kaca kaca ta fita ba ta gyara ba, ban yi mgana ba na gyara nima ko yau de zan fita na ce ba zan gyara ba na bar mata shi ne da ta je shashen ta gan shi haka ita ishasshiya ta zo har shashena tana faɗa mini mganar banza. Na je na gyara yau Mijinta zai dawo ban isa na kwana da miji ta yi mini bauta ba, ni kuma sai na ce ai bauta ta gama tun da sai da na jagwalgwala na ba ta take suɗewa daga faɗin haka sai yarinyar nan ta ce wai in ban tashi na je na gyara ba zan ga abin da zai faru ni kuma na ce in ta fasa, saboda tsabar ta raina ni kawai ta jawo ni ina kan kujeran nan sai da na faɗo ƙasa ni ko da raina ya ɓaci ina miƙewa na kifa mata mari shi ne ita ishasshiya ta jani da dambe shi ne na nuna mata ba ta isa ba."
Gimbiya ta gama bani labari tana faman haƙi
Kallonsu kawai na ke yi ina mamaki har yauahe ne za su daina fada kan wancan turakan da Yallaɓai ya samar da ita a cikin gidan nan ne? Shi kamar ma jin daɗi yake yi suna ta kara kaina akansa.
Kai na girgiza kafin na ce" Haba don Allah wai mene ne da Turakan nan? Ko da yaushe a kanta ne kuke faÉ—a?
Na faÉ—a ina kallon su gabaÉ—aya
"Ita ta ja, da ta san ba ta gaskiya me ya sa ba ta tashi ta je ta gyara ba? Kuma ai Abba ya ce duk wacce za ta fita ta gyara abin da ta ɓata."
"Ba zan gyara ba, ke da kika fita a gyaren kika bar mini? Sai ke ce mai bakin mgana? To na ƙi na gyara ki ɗau matakin da za ki ɗauka."
Gimbiya ta faÉ—a har tana sake rike kugu, ga cikinta har ya fito amma ba ta ko jin nauyin jikinta.
"Za ko ki gani wallahi."
Rabi'atu ta faÉ—a tana cije baki, har ya tasa ga jini a lebenta ta daku, ganin ga Salima a wajen yasa na kalleta ina faÉ—in" Salima koma bangaren Rabi'atu ki zauna da su Ayush."
Sai ta amsani da to ta sake ta Rabi'atu sai ta ce tare za su tafi ni kuma na ce ta tsaya ina da mgana da su ita da Gimbiya sai da Salima ta fice sannan na kalleta ina faÉ—in"
"A wannan rigimar gaskiya ke ce ba ki da gaskiya Rabi'a."
"Ni kuma"?
Ta fada tana wani tura baki, na ko haɗe rai ina faɗin." ƙwarai ke fa, ai ke ce ƙarama, yau ko da Gimbiya ce mara gaskiya ya dace ki biyo ta bangarenta kina yi mata rashin kunya? Ban da Yallaɓai da auro ki ya goga kafaɗarki da ta mu ke kin isa ma ki haɗu damu a hanya ki yi mana mgana ballanta har sa'in sa ya haɗa mu? Na fahimci kwana biyu nan kina ji da rashin kunya to ki kama kanki ko ba aure Gimbiya ba sa'ar yin ki ba ce ballatana tana gaba da ke a gidan nan, abin da kika yi ba dai dai ba ne, tun da kin yi itama ta rama ba shike nan ba? Amma saboda fitina sai ki biyo mata har bangarenta ki ja ta da Dambe? Ai gashi nan kin sha wuya gaba ma sai ki ƙara."
Kawai sai yarinyar nan ta saka kuka tana faɗin" sai ki yi son kai ki goyi bayan ta ? Sai kawai ki yi ta mini faɗa akan gaskiyata ai Abba ne ya ce kowa ya ɓata ya gyara."
"E an yi miki faɗan, kin yi ba dai dai ba ba za a gaya miki ba? Abba ya ce wacce ta gyara ta bata kema kin ɓata ta gyara itama ta ɓata ba sai ki gyara ba? Da gaske ne ba ki da kunya ki kuma daina wannan halin ba zai ɓulle da ke ba, ni dai gaskiya na faɗa miki."
Kawai sai ta juya har tana yi mini tsaki.
"Mtswww. Bari Abba ya dawo wallahi sai na faÉ—a masa."
"To in kin fasa faÉ—a masa kin raina kan ki. Shashaaha kawai."
Raina ya baci daga faÉ—an gaskiya bayan fitan kan ta Gimbiya na koma ina ta mata fadan me ya kai ta dambe da wannan yarinya a ga shi nan ta raina ta nan gaba ko a ina ne ba za ta ji shakkar jan ki da faÉ—a ba
"Da ko da ta daku wallahi kambu"
Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce" Ba ki kyauta ba me ye sa kika biye mata ba."
"Har fa É—akina ta biyo ni? Sai na raga mata?
Ni haushi ma ya hana ni mgana na bar mata bangarenta na koma nawa, ina barcina sun hanani sukuni, dole na yi wanka na iske Baby ta soya doya da ƙwai sai na hada tea na ci da shi, ina yi ina tsaki saboda takaici da man kwana biyun can rashin kunya na fahimci Rabi'atu na fama da shi, ba kuma kowa ya ja ba sai Yallaɓai shi ya ja mana wannan wulaƙancin, ya sa ƙaramar yarinya tana ganin ɗaya take damu, ni wallahi daga Yallaban har matan na shi da gidan sun fita daga raina, ina can cikin yan uwana na ma manta da wannan hatsaniyar.
Yini na yi a bangarena ban fita ba, har yamma daga Gimbiyar har Rabi'atun ban san isalinsu ba, su Baby sun dawo ba daɗewa sai ga Yallaɓai ni da na ga ma Yamma ta yi ban ɗauka a ranar zai dawo ba sai ga shi, kuma a turakarsa ya sauka, ni kuma ban yi rawan jiki zuwa na gaishe shi ba, ina idar da sallar mangariba na zauna ina duba wayata, Baby da sauran yaran suna shashen Gimbiya.
Kawai sai ga kiran Yallaɓai ban kawo ma kaina har Rabi'atu ta kai mganar nan ba sai da na ɗaga kiran na ji shi a fusace har yana yi mini ihu a waya.
"Ki zo bangarena yanzu Sadiya."
Kuma yana gama faÉ—in haka ya katse wayar, wayar na koma ina bi da kallo cikin mamaki kafin na furta a fili" Ikon Allah!.
Na yi niyyar zuwa a lokacin amma ina miƙewa sai cikina ya karta, shi ya sa na tsaya sai da na shiga tiolet na rage ciki ina fitowa da man na yo alwala jin ana kiran sallar isha'i na tsaya na yi sallata ina yi ko sai kiran wayata ake yi tun kafin na sallame na san shi ne, ban ɗauka ba saboda na san ihu zai yi mini shi ya sa da hijabin jikina na fita zuwa bangaren Yallaɓai.
Ina shiga na gan su tsaye a falo cirko-cirko shi da matansa, Gimbiya na tsaye kiƙam rike da kugu shima haka hannayensa a bayan shi yana ta kai gauro da mari a falon Rabi'atu kuma na zaune tana sunne kai, falon na sake bi da kallo kaca kaca, alamun dai Rabi'atu ba ta gyara ba kamar yadda ta rantse.
Tun kafin na kariso ciki Yallabai ya tare ni da hargagin shi da ya koya yanzu.
"Sadiya ni za ki wulakanta? Ni za ki yi ma wulaƙanci?
"Me na yi kuma?
Na faÉ—a cikin mamaki, domin ganin su Gimbiya kawai na tabbatar mini da Rabi'atu ta kai masa labarin abin da ya faru É—azu.
Ni ko ina ruwana da zai sako ni a ciki don Allah?
"Ban sani ba. Na ce ban sani ba kar ki raina mini wayau kin ji ko?
Kallon shi na yi ganin shi a fusace kamar yana jirana ina kokarin danne abin da ke taso mini na ce" Gani ina fatan lafiya?
"Ko lafiya lau ya dace na kira ki sama da minti talatin ki shanya? Kin kyauta kenan?
Ina yamutsa fuska na ce" Ka kirani ina shirin zuwa cikina ya motsa na shiga makewayi, bayan na fito na ji ana kiran salla shi ne na tsaya na yi salla, ban É—auka ai kana jirana ba ne"
Na faÉ—a ina mai zaman kan kujera mai zaman mutum É—aya domin na gaji da tsayuwa.