Sashe 69
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta yi wajen wata biyu sannan Amina ta dawo da ita. Yumna ta ɗan rame sannan ta kara girma sun kawo ta da sha tara na arziki ita da mijinta Yallabai na ta fadan wai na tura musu ɗawaniya. Na ce na ji ba komai ai ƙanwata ce in ta yi mata ba ta faɗi ba.
Rayuwa dai alhamdulillah tana tafiya cikin farinciki. Yallabai yanzu fa na neman ya sha kwana. Kuɗi kawai yake facaka har mota ya sauya wata jeep ce itama mai tsada. Adnan ya faɗa mini da muke hira da shi za ta kai miliyan huɗu daga nan na yi shuru. Sannan ya bude shagunan sai da kayan gini, komai na na'uin gini akwai, kofifi, interlock, simnti, kayan aikin tiolet, kwano, ba abin da babu a wajen ƙasan wajen kuma ya saki shagunan masu aski da wasu yan kasuwan sun kama sannan ginin gidan shi ya yi nisa har an yi linfter an saka kankare tuni yanzu ma rufe yace mini ake yi, an ma kusa gamawa da ya nuna mini a hoto. Sai ina ta mamakin gaggawan da yake yi a kan ginin nan sai da na yi masa mgana.
"Ina so ne ko ba ku tare ƙarshen shekaran nan ba to a farkon shekaran 2023 mu tare a sabon gida in sha Allahu."
"Allah ya amince mai girma Md."
Na faɗa ina dariya har ina jinjina, saboda maganar gaskiya Allah ya buɗa ma Yallabai kwangolili ne wasu na jiran wasu malam. Kuma in dai aka bashi kwangila ya yi shike nan duk wanda ya gani sai ya yaba yace a haɗa shi da shi sillar gasikiya da amana da aiki ba ha'in ci. Mu kan mu mun shaida Mijin mu na da kuɗi yanzu, abinci sai dai mu yi kyautarsa. Duk wani abu na daɗi muna ci, suturu kuwa na kece raini muke sawa mu da yayanmu. Ba mu ba har iyayen shi ma yana yi musu nima ba abinda zan ce masa sai godiya. Ya ba ni kuɗi na kai gida ya kai kayan abinci komai fa sai godiya. Da shi da Kawu sun yi ma Tariq fintikau shi duk cikin su ba shi da ƙarfi tun da aikin Gwammati yake yi. Su kuma yan buga buga ne da man.
****
BAYAN WATTANI HUÆŠU.
A watan october 2022 Baaba ta gama idda sai ga shi karshen ta dai gidanmu ta dawo da zama ita da sauran ƙannen Ma'u su Zainab. A ɗakin Hajiya Dubu su Ya Hamza suka gyara mata daman tarkace ake sawa a ciki. Baaba duk ta yi laushi kamar ba ita ba, ni ce wai za mu zauna muna hira da ita har muna dariya abin da ban taɓa tunanin fatuwarsa ba. Datti ya samu aiki a NNPC reshen jihar kaduna har an saka masa rana zai yi aure zai auri wata abokiyar karatunsa tun suna KAsu ba ta yi aure ba har ta yi masters tana aiki itama. Duk kuma a kusan lokaci ɗaya aka saka musu ranar aure tare da Adnan, wanda shima ya fara aiki a ma'aikatan Yallabai a matsayin Engeanaring na karatu.
Tuni ginin gidanmu ya yi nisa ko na ce cikin kashi uku an yi biyu saura É—aya. Tun da ko wancan satin da hanya ta bi da mu ni da Ma'u da su Ya Aina na É—auko su a motata mun je gaba da in da gidanmu na mu yake, gaisuwa yayar Zaitunan Ya Abubakar ne ta rasu muka je mata gaisuwa. Na bi da su ta gidan har sauka ma muka yi suka gani, Mun shiga ciki ma'aikata ne sama da ashirin suna aiki, wasu sun sanni suna ta faman gaisheni waÉ—anda ba su sanni ba suna faÉ—a musu matar injiniya ce.
Mun iske suna ta saka inteelock na tsakar gida. Wasu na ciki ɗakunan suna yin filista, wasu na ma an gama ana saka kofofi daman POP da wearing din wuta ana gama rafta Yallabai ya ce an yi su. Na ga har fulawoyi aka shushuka a gidan har sun girma daman Yallaɓai akwai son shuke-shuke a gida. Ya Aina da Ya Balki suna santin girman gidan da kyan shi, Ma'u ko har da guzarin kasar wajen da yake tana da ƙaramin ciki sha take yi wai ta yi mata daɗi.
Muna tafe a hanyar komawarmu Ɗorayi Ya Murja ta ce"Gidan nan da girma yake. Amma na ga shashi huɗu ko aure Baban Jiddan zai ƙara?
Ya Balki tace" Ni ma abin da zan ce kenan bayan shashin Sadiya da na abokiyar zamanta nata ga biyu nan kusa da juna."
"Nima fa ina ta mamaki."
In ji Ma'u dake gidan Gaba su suna can baya ne.
Ina dariya na ce" To Allah masani. Mu ma dai haka muka gani da na yi magana ya ce É—aya na shi ne É—aya na baki. Daga karshe yace ga shi da yara maza ya yi awadace ne."
"Uhm ya dai ce muku ne amma da wahala bai ƙara ko dayan ba ne ballanta yanzu da giyar kudi ke ɗiban shi "
In ji Ya Aina ni ko na saka dariya ina ba su labarin diramasu da Gimbiya.
"In Yau Yallaɓai ya ce zai yi aure ai akwai yaƙin duniya na uku shi da matarsa."
"Ta yi ta gama. In dai ya yi niyya sai ya yi."
In ji Ma'u ita da ta ga zahiri, ga amarya har ta haihu, itama an zama daya da ita.
Ni dai ina ta dariya har muka kariso gida, Rahila ba ta je ba, ba ta da lafiya ta ce sai gobe za ta leko, muna gidan har bayan la'asar muna ta hira da Baaba da Gwaggo. Har a raina ban kawo ma Yallaɓai aure yanzu ba, ba kuma don ban ji a raina zai ƙara ba amma sai don ina ganin wataƙila akwai sauran lokaci. Sai dai me? Sai na fara ganin canje-canje daga wajen shi, yana yawan kafa-kafa da wayarsa a kwanakin nan. Abin da a baya bai dame shi ba in ba aiki zai yi a ciki ba ko an kira shi ta yini a in da take bai taɓa ba ya fi amfani da laptop ɗinsa a kan wayarsa
Amma a kwaanakin nan Yallaɓai na kan wayarsa har murmishi zan ga yana yi wani lokacin, na rasa me ya ke dubawa ko kuma me ya ke karantawa? Sannan wata rana in yana gidana zai dawo ya yi wanka ya ci uban gayu ya fita in na yi magana sai yace akwai mutanen da zai gani ne. Ni kuma samin shi da jama'a da hulɗodi sai ban damu da fitan na shi ba amma a kwanankin na fara zargin Yallaɓai yana yin wani sabon abun da bai saba yin shi ba, sannan ranar ma Yumna na wasa da wayarsa da ya ijiye a saman kujeran falon sa ya shiga tiolet, sai na karɓa abin mamaki na san code ɗin buɗe wayarsa date ɗin aurenmu ne, amma sai na gwada ya ƙi buɗewa kenan ya canza. Da ya fito ya ga wayar a hannuna ya ɗan yi wani iri, da sauri kuma ya karɓe wayarsa ni kuma sai na ce masa Yumna ce za ta yi masa wasa da shi na karɓa
Tambayarsa na yi ashe kuma ya sauya code É—in buÉ—e wayarsa.
 "E na sauya."
Bai kuma faÉ—a mini abin da ya sauya da shi ba sai da na tambaye shi.
"Date É—in ranar da na buÉ—e ma'aikatana ne."
Haka kawai ya faÉ—a daga nan kuma ya koma ya zauna ya cigaba da duba wayar tashi. Har yana wani mirmishi na yi kasake kaawai ina bin sa da kallon mamaki amma na kasa magana.
Na ɗauka ni kadai ce na fahimci Yallaɓai na yin wasu baƙin abubuwa. Sai da Gimbiya ta yi mini magana a chart, da man tun bayan faɗan da na yi mata muke yar daɗi da ita in ma wani abu ne ya shige mata duhu akan mijinmu za ta kira ni mu tattauna.
"Maman Jidda."
Na amsa mata lokacin Allah ya sa ina online itama haka.
"Kin fahimci Daddy na yin wani abu a boye wanda ba ya so mu sani!?
Sai na ce mata ban fahimta ba, saboda ko na ce na fahimta ba ni da hujja tun da ban ji ba, kuma ban gani ba.
"Me kika gani? Me ya sa kuma kika ce haka?
Sai na rubuta mata tambayoyin na tura mata sai na ga tana yi mini Vn
Yana shigowa da sauri na buÉ—e.
"Maman Jidda Daddy na yin wani abu gaskiya. Yanzu fa kafa kafa yake yi da wayar sa kuma a da ba haka yake yi ba. Maman Jidda Daddy fa yanzu sai ya kai 1 na dare yana online sai ka rasa da wa yake yin charting da na yi magana sai ya ce wai da abokan hulÉ—arsa ne. Sannan sai ya rika yin wanka ya ci gayu ya É—au mota ya fita sai dare yake dawowa ni fa gaskiya na fara ji a jikina anya anya kina ganin ba wata ce can a waje ta fara É—auke masa hankali muna nan zaune ba mu sani ba."
"Hmmm."
Kawai na tura mata na ma kasa magana. Ashe dai ba ni kaÉ—ai na lura da wani abu na É—aukan hankalin Yallabai a kwanakin nan ba.
"Ki yi magana. Ke ma kin fahimci haka,?
"Nima na fahimta amma na kasa gane me ya jawo haka."
Na amsa mata
"Kin ji ko. Wallahi mu tashi tsaye da bincike kar muna zaune wata shegiya ta É—auke masa hankali.'
Sai kawai na ce mata to zan bincika itama a ɓarayinta ta bi komai a sannu sai ta amsa ni da to, wai har da cewa ta sanni da sanyi wani lokacin wannan karon ba abin yin sanyi ba ne sai kawai na tura mata dariya.