← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 103

Sashe 6

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na fahimci manufarsa ya yi saurin kiran Ya Hamza ne ya faɗa masa saboda ni ya rigani wanda ko daga baya na faɗi wata mgana ba za a goya mink baya. Yallabai ya san ni sarai kamar yadda na san shi ciki da bai. Ya san ba zan taɓa zuwa na kai ƙaran shi ba ya kuma san ba zan taɓa fasa mganar faɗan mu ba amma ya san ina da kafiya zan iya ƙin dawowa a lokacin da ya so ya kuma san in ba Ya Hamza ko Ya Auwal ba, ba wanda zai matsa mini na koma shi ya sa sai ya yi saurin kiran Ya Hamza. Ya san da gangam na ƙi ɗaga wayarsa ya kuma sha jinin jikinsa ko kunya ne zencen ban sanin masa ba. Sai yanzu ne ya tuna da ina da amfani a rayuwarsa? Wallahi tallahi sai ya raina kansa kuma bashin gorin da ya yi mini na gida da na haihuwa watan tara na zai biya su. Sannan ya yi sanadiyar na rasa gudan jinina bana jin ko da na yafe masa laifinsa to ba na jin zan iya yafe masa wannan kasadar da ya ja mini na rasa wani abu mai muhimmaci a rayuwata.

Zan koma ba domin Ya Hamza ya yi min mgana ba sai domin ina da niyyar komawar. Amma kuma kiÉ—a ya sauya dole rawa shima ya sauya. Na daÉ—e ban yi barci ba ina tunanin mafitan da zan nema ma kaina in na koma gida.
Na yi tunanin zan koma makaranta na yi masters ɗina sannan zan inganta sana'ata ta hijabai har ma da ƙarin wani sana'o'in na daina dogara da Yallaɓai na kuma daina dogara da duk abin da ya ke takaman ya mallaka. Daga ni sai ƴaƴana domin nan duniya su ne kaɗai na aminta da ɗari bisa ɗari ba za su taɓa juya min baya ba.

Da safiyar talata na yi shirin komawa Kano. Tare muka fita da Amina za ta je saloon ita da Yasir ne Afra da Sumaiyya na makaranta Amina sai sha'awata take ba ni ta iya driving ba in da ba ta zuwa a garin Kaduna da yar motar ta da Dr ya siya mata. Ni ma a raina na kudiri niyyar zan dukufa da sana'a har nima na mallaki mota ta kaina da gumina. Ita ta kai ni tasha na samu mota sannan muka yi sallama sai da motar ta tashi na bar ta a tasha. Kuma har kuɗin motar ita ta biya mini da cewa Dr ne ya ce ta ba ni na ƙara riƙewa a hannuna. Mun rabu ina ɗaga mata hanmu tana ɗaga mini nima.

Motar mu ta tashi goma saura ba mu isa Kano ba sai biyu na rana. Daga tasha na hau adaidaita zuwa gidana. Ba kowa a gidan sai da na saka makulli na buɗe gidan na shiga ko'ina ya yi ƙura. Na shiga cikin bedroom ɗina na ijiye akwatin hannuna da jaka sannan na zare mayafi na shiga tiolet na kama ruwa na yo alwala na taho na yi salla ina idarwa na tashi na shiga kitchen, shima dai duk ya yi ƙura amma dai ba a yi amfani da komai ba.

Gas na kunna na dafa ruwan zafi na sha tea, sai ƙwai da na soya guda uku bayan na gama na koma ɗaki na ɗauko wayata kamar in kira shi sai na fasa. Domin ban bi umarnin Ya Hamza, jiya ban neme shi ba shima bai sake nema ba ina da tabbacin wata ƙila ya sake kiran Ya Hamzan ne shi kuma ya faɗa masa na ce yau zan koma gida.

Ganin ba zan iya kiran shi ba sai kawai na tura masa saƙo.

"Na dawo gida."

Ina gama tura masa sai na kira wayar Salisu direba bayan mun gaisa na ce masa yau in ya dauko su Jidda ya kawo mini su gida na dawo. Yana ta min sannu da zuwa na gama waya dashi kenan Balaraba ta kira ni ta na faɗa mini  Saude ta sauka duk sai na ji ɓacin raina ya tafi ina mata barka ta samu megida tun da namiji ta haifa. A Lokacin na kira wayar sai mijinta ya ɗauka ya ce ta na wankan da yake ba a asibiti ta haihu ba a gida ne amma sun kira anguwan zoma. Mun rabu a kan cewa in ta fito zai faɗa mata za ta kirani. Sai ko gashi ta na fitowa ta kira ni muka yi magana abin hamdalar shi ne ta haihu lafiya ba wata matsala na yi mata mganar za ta dawo gida ne ko anan za ta zauna sai ta ce min ita ba ta sani ba, ni ko kai tsaye na ce mata gwara dai ta dawo gida a kula da ita ko bayan suna ne sai ta ce mini za ta yi magana da megidanta na ce ya kamata.

Na ɗan kwanta sai la'asar sannan na tashi na yi salla sannan na fara gyaran gidan na share ko'ina na goge na saka turaren wuta gidan ya fara ƙamshi duk da na gaji ban zauna ba na fara tunanin abin da zan dafa na duba friza na sai na ci karo da miyar da na yi ana gobe tafiyata tana nan ba ta yi komai ba kuma ina da sauran kayan miya da kayan lambu sai dai duk sun bushe sai na kwashe su kawai na zubar har da ma su kankana suma duk ƙanƙara ya sa sun yi wani nakwa nakwa saboda daɗewa sai kawai duk na kwashe na zubar a bola na goge firizan. Miyan na sake gyarawa na dafa mana farar shinkafa na gama shidda saura na yamma na goge kitchen ɗin sannan na je na yi wanka na fito kenan ina saka kaya na ji ana buga get a raina na ce to yan makaranta sun dawo.

Wani riga da wando na saka pakistan ne rigar ja ne da baƙi ba ta da hannu sai daga kasa an ɗan zoɓa ta, sai wando sakakke ne bai kama min jiki ba sai na saka hula baƙa mai kwalliya ta sama, kaina akwai kitso a can Kaduna Amina ta yi min shi duk da ba ta wani iya kitson ba amma na gaji da kan ya tsufa sai na tsife na ce ta yi min ko kalaba ne shi ne ta zarga min shi haka, kuma gashi ba ta kama shi da kyau ba duk ya fara sukurkucewa har kunya na ke ji na buɗe kan a gaban mutane.

Silafas ɗin cikin gida na saka sannan na saka mayafi na fita zuwa haraban gidan na buɗe ma yara ƙofa suna ganina har Jidda sai da suka faɗa jikina suna min oyoyo na tarbe su cikin farinciki. Da gaske na yi kewar su sosai musamman ma surutun Baby. Salisu bai tafi ba daman in ya kawo su sai ya tabbatar da an buɗe gida sun shiga ya ke tafiya mun gaisa da shi ya yi min barka da dawowa ni kuma na ce ya gaida iyalan na shi, na rufe gida muka dawo cikin gida ni da ƴaƴana.

"Baby ciwo kika yi? Na ga kin rame ne?

Na faɗa ina tattaɓa wuyan ta lokacin da muka dawo cikin gida.

"Ta yi zazzaɓi na kwana biyu a gidan Anty Gimbiya."

Jidda ta ba ni amsa sai na zauna saman kujera na jawo Baby ta zauna saman cinyata ina shafa fuskarta na ke faÉ—in.

"Ayya sorry My princess Umma ta tafi ta bar ki ko?

Sai Baby ta fara tura baki tana faɗin" Umma ni dai kar ki ƙara tafiya ba ki tafi da ni ba ina ta kuka Abba sai ya yi ta cewa za ki dawo ba ki dawo ba sai da aka daɗe."
Dariya na yi ina mai rumgumeta kafin na ce" Ba zan ƙara tafiya na bar My princess ba in sha Allahu "
Jin haka ya sa ta fara tsallen murna ita dai Jidda na zaune ta na mirmishi. Ranar ni na ta ya Baby cire kayan makaranta ta saka na gida Jidda ma ta sauya ta fito na zubo mana abinci a filet muka ci tare. Na sha labarai wajen Baby duk abin da ya faru da ba na nan sai da ta faÉ—a mini Jidda na gefe ta na cin abincinta tak ba ta ce ba, ashe ranar da na tafi ranar daga makaranta ya ce salisu ya kai su sharaÉ—a ba su ma kwana a gidan ba kenan.

Bayan mun gama Jidda ta tattara komai ta kai kitchen ta kuma share in da muka ɓata. An kira mangariba muka yi alwala muka yi salla a falo, muka yi azkar sannan na ce mun dade ba mu yi karatun Qur'ani su ɗauko mu yi karatu.  Ba mu muka tsagaita da karatun ba sai da a ka kira sallar isha'i sannan muka dakata muka yi salla, muna idarwa na ce su yi aikin makaranta ni kuma sai na shiga ciki na ɗauki wayata ina dubawa sai na ga Yallaɓai ya yi min saƙo.

"Ya yi kyau."
Chapter 6 · 0% Book details