← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 103

Sashe 10

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi aure a cikin garin Kano nan amma ban taɓa zuwa gidan ta ba na dai je bikin da Rahila ta matsa mii  kuma har gida Maijiddan ta kawo min IV da mintin gayyata. Kaf waɗanda muka yi karatun jami'a da su ba na zumunci da kowa. Wasu ina ɗan kiran su a waya jaje ko murna shima na zo na daina daga baya nima tun suna bina har kowa ya rabu da ni ina dai cikin group ɗin kuma ina ganin ana ta abubuwa in sha'ani ya tashi na ɗayan mu a haɗa kudi kuma a je, ni dai na kan ba da wani lokaci amma zuwa ban taɓa yi ba. Sai dai in ga ana turo hotuna suna zumunci su amma ni na ware kaina kamar saniyar ware. Ban taɓa jin abin ya dame ni ba sai yanzu amma a ƙasan zuciya na ƙudiri a raina nima yanzu zan nemi jama'a domin na fahimci jama'a rahama ne.

Ranar ma sai dare Yallaɓai ya zo gidan kuma again a ɗakin barcin mu ya sameni ina ta rubutu.

"Madam wai labarai kika fara rubutawa ne?

"Me ka gani?

Na ɗago ina kallon shi bayan na dakata da rubutun da nake yi. Gyara zama na yi a gefen gadon lokaci ɗaya ina gyara zaman doguwar rigar  material ɗin dake jikina.

"To gani na yi kwanan nan kina ta faman rubuce rubuce."

Kallonsa na yi ina tuna yaushe ne ya ganni ina rubutu? Ni dai ina tunanin wannan ne na biyu amma zai ce wai kwanan nan ya na ganina ina rubuce rubuce.

"Kawai abin kasuwanci ne. Ina rubuta waɗanda suka karɓi hijabai ne."

"Da kyau Hajiyar Business"

"Ya Hanya?

Sai na kau da maganar ganin duk ya gaji daga yanayin ma yadda ya ke mgana.

"Lafiya lau. Amma na gaji sosai"

"To ka zauna mana."

Na faÉ—a ina nuna masa gefen gado saboda na ga yana tsaye kuma ga shi ya ce ya gaji."

"Bari kawai na ƙarisa gida na yi wanka na huta gabaɗaya."

"Kuma fa haka ne."

Na faɗa ina kau da tunanin ya ƙi amsar ta yi na ne. Ni fa taimakon sa na yi ganin ya ce ya gaji kuma yana tsaye kamar wani dakaren soja.

"Maganar mu fa Sadiya?

"Wacce magana?

Na tambaya ina kallon shi.
Sai ya gyara tsayuwa yana mai harɗe hannayensa a ƙirji kafin ya ce.

"Mganar da na ce in kika dawo za mu yi. Domin mu warware rashin jituwan dake tsakanin mu."

Sai na yi mirmishin takaici kafin na ce" Muna gabar ne har yanzu? Ai ina jin kamar mun warware komai."

"A'a.

"To me ya yi saura?

"Komai ma."

Ya katseni ya na mai tsareni da idanuwansa.

"Kin daina gaba da ni amma kuma kin ƙi komawa kamar yadda kike a baya Sadiya."

"Mun daina gaba da juna za ka ce ko?

Ya na kallona na cigaba da faɗin" Tun da kaima ba ka yi mini magana Yallaɓai."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Duk na ji na amsa laifina shi ya sa na ce mu zauna mu yi magana domin mu fahimci juna."

"Na ji za mu yi in sha Alkahu."

Na faɗa ina ƙokarin komawa in cigaba da rubutuna.

"To yaushe?

Sai da na É—ago na kalle shi ido na cikin ido sannan na ce.

"Sai ranar da na karɓi girki."

Murmishi ya yi kafin ya ƙariso gaba na ban yi aune ba kawai ya ɗan rankwafa ya sumbaci laɓɓana kafin ya miƙe ya fice yana faɗin.

"Sai da safe Sadiya ta."

"Sai da safe."

Na amsa masa a saman laɓɓana bayan fitan shi har ina shafa wajen. Yaushe rabon da a yi haka! Tun kafin faɗan mu da shi a kan Khalipa. Yaron na raina ina son tambayan shi amma na fasa tun da ya nuna min iyakata ya je amma ƙaunar da nake yi ma jininsa ba zan fasa saboda shi ba, ko faɗan mu ne ya sa kwana biyu tun da na dawo bai tarkatomun Khalipan ba, amma na ƙudiri niyyar in na ga ba a kawo shi ba zan kira Gumbiyar na ce ta kawo shi ya yi mini kwana biyu na saba da shi duk da ɓarnar shi, shi kuma na san ya yi sabo da gidana sosai kawai dai kwana ɗaki ɗayan da Yallaɓai ya tsiro da shi na ga ana cutata shi ya sa na yi magana amma ba da niyyar Khalipa ya daina zuwa ba tun a baya ban hana shi zuwa ba sai yanzu?.

******

Tun da yau Yallaɓai zai dawo gida na na kira Maman Nana na ce in ta samu lokaci ta zo ta yi mini kitso. Da safen ko ta zo ta yi min 2step ƙananu. Kuma kitson ya yi kyau tun da na duba a cameran waya ta na gani. Sai azahar ta tafi bayan na yi mana girki duk dai macaroni na dafa mana muka ci da ranar. Bayan tafiyan ta na gyara gidan na yi shara na saka turare ɗan kwanciya na yi na ɗan huta zuwa la'asar na tashi bayan na yi sallar la'asar
Sannan na É—ora ma su Jidda girki da man macaronin guda É—aya na dafa.

Cous-cous na dafa mai kayan lambu daman kuma Yallaɓai na so shi ya sa na yi. Sai zoɓon da na haɗa daman tun safe na riga na dafa genyen zoɓon haɗawan kawai na yi. Sai sauran kayan marmarin da suka rage mana na yanka na yi mana fruit salad ni da Yallaɓai.
Shidda saura su Jidda suka dawo makaranta ajaran majaran saboda yunwa ko uniform ba su cire ba suka fara cin abinci. Baby na faɗa min Umma cikina kamar an kwashe min kayan cikina ina gefe ina ta yi mata dariya ganin tana cin abinci hannu baka hannu ƙwarya.

"Baby ki ci a sannu kar ki shaƙe.'

"Umma ba ki san yunwan da na ke ji ba ne"

Ina ta mata dariya ni na je na kawo musu da zoɓon ya yi sanyi na saka a firiza.

"Ya Jidda ke ma duk yunwar ba baka sai kunne?

Sunne kai ta yi ta na faÉ—in.

"Umma ni kin ji na yi magana ne?

"Ba ki ce komai ba. Ke dai ci abinci kawai."

Na faɗa ina yar dariya. Yarinya na jin yunwa tana noƙewa.

Bayan sun gama cin abincin sun ƙoshi, suka sauya kaya zuwa na gida lokacin an kira salla sai muka yi alwala muka yi salla yau ba mu yi karatu ba saboda wankin uniform muka fita  ta baya muka wanke su tare da yan riganunan barcin Baby da ƙananun wandunan ta daman Jidda ke wanke musu tare da na ta. Muna gamawa ana kiran sallar isha'i muka sake ɗauro alwala muka yi sallar isha'i. Muna idarwa ni kuma na faɗa wanka bayan na fito na yi gayu na cikin riga da zani na wata atamfata hollond ta na cikin kayan da na siya lokacin auran Yallaɓai da Gimbiya.

Na kashe ɗauri na ture ka ga tsiya na ba za gashina ya sauko har kafaɗuna. Har da su jan baki na saka na kuma zirara gazal a girana, na fita falo wajen yara da dai na ga shuru Yallaɓai bai shigo ba sai na diɓi abincina na ci na kora da zoɓo da fruit salat. Bai kuma shigo ba sai goma har ta ma gota. Tuni har na kaɗa su Jidda ɗakin su na ce su yi shirin kwanciya so ni kaɗai ya iske zaune a falon ina kallo duk da hankalina ba akan kallon yake ba.

Miƙewa na yi ina kallon shi, nufar sa na yi ganinsa da ledoji a hannunsa.

"Sannu da zuwa."

Na faɗa ina karɓan ledojin hannunasa.

"Yauwa Madam ya gidan?

Ya faÉ—a lokaci É—aya yana sakar min ledojin a hannuna.
Na amsa da lafiya lau lokacin da na nufi kitchen na duba ledojin tsire ne sai fura mai sanyi an dama ta a leda. Na san ni ya siyo mawa da yake ya san ina son fura duk da cikina ya cika amma ta ba ni sha'awa zan sha zuwa anjuma in cikina ya sassaɓe.
Naman dai a firiza na saka shi  da safe sai mu ci na san na mu ne Yallaɓai ba ya son tsire ya fi son gashi na naman rago. Sai ya ce wai tsire duk ƙuli ne ba nama ba.

Ko da na fito ba shi a falon ya na ciki sai na koma kitchen ɗin na hada masa abinci na kai dining sai da na gama shirya masa duk abin da zai buƙata sannan na koma bedroom ɗin na iske Yallaɓai ya fito daga wanka ya na saka sauƙaƙƙun kayan zama cikin gida riga da wata ƙaramar riga mara hannu. Sai ma yau na ƙare ma Yallaɓai kallo da gaske kam Yallaɓai ya fara ijiye tumbi da na ƙura ma gashin kansa ido har na hango ƙyali ƙyalin furfura a saman kan shi har ma da sajen shi. A raina na ce su Yallaɓai tafiya ta fara miƙawa.

"Tunanin me Sadiya ta take yi ne ahalin ga ni a kusa?

Ya faÉ—a ya na mai sagalo hannun shi a kafaÉ—ana sai na tattaro murmushi na kalle shi na yi masa.

"Abinci.?

Na faɗa ina kallon shi sai ya shafa cikin sa yana faɗin daman yunwar yake ji. Ya ƙi sakina ya na dafe da ni muka fita can falo sai da zai zauna saman kujeran dinning ne ya sake ni.
Nima gefen sa na zauna na zuba masa cous-cous ɗin da zoɓo sai fruit salaf ɗin sai ya ce na zuba masa leda ɗaya na fura yana so zai sha sai na koma kitchen na juyo masa a wani ƙaramin mug. Ina gefen shi har ya gama cin abinci kuma daga yanayin sa na fahimci ya ji daɗin haka. Barin ma yadda na ga ya ci abincin sosai da alamu dai yau Yallaɓai ya yi ta su Baby ta babuwa ta addabi cikin sa.

"Girki ya yi daÉ—i. Haka ma mai girkin ta yi kyau."

Ya faÉ—a ya na kallona sai na yi murmushi k amma ban ce komai ba.
Chapter 10 · 0% Book details