← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 103

Sashe 86

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yallabai na kalla kawai sai na ga ya juya zai shiga shashen Rabiatu Gimbiya ta bishi tana faÉ—in"Ai ka ji sai ka dawo bangarena sai gobe ne za ka koma mata."

"Ba zan koma ba. Wannan tsarin ku ne ba nawa ba, nawa wanda na sani jiya na shiga É—akin ki, yau da daddare na fita zan kwana a bangaren Rabi'atu."

"Wallahi ba ka isa ba"

Gimbiya ta faɗa cikin ɗaga murya ta juya zai shiga ta sha gaban shi har tana riƙe masa riga.
Ni dai sai na yi tsaye kawai ina ganin ikon Allah.

"Ba ni hanya in wuce."

"Ba fa za ka koma shashenta ba sai gobe wallahi "

"To ni kuma yau a nan zan kwana in kin isa ki hana ni "

"Ni kuma wallahi in har ka kwana a ɗakin yarinyar nan Da haƙƙin kwana na Allah ya isa ban yafe ba"

Gimbiya ta faɗa har tana shan wallahi. Shi kuma Yallaɓai ya fizge rigar shi ya tureta gefe ya shiga yana faɗin" Da sauki tun da ba tsine mini za ki yi ba "
Ta kwashi kururuwa za ta bi shi ciki, shi ko yana shiga ya rufo ƙofar ta ciki sai ta fara bugu tana kiran sunan shi.

"Yusuf ni za ka wulaƙanta? Wallahi in har dai ka kwana a ɗakin nan ban yafe maka ba tun da dai haƙkina ne yau "

Kawai sai ta fashe da kuka ni wallabi ban saba ganin haka ba yasa sai jikina ya yi sanyin da na kasa motsi. Ganin maigadi na gefe yana kallon komai ita kuma tana ta kuka tana buga ƙofa tana Allah ya isa ba ta yafe ba. Yau ba Baban Khalipa Yusuf ne kai tsaye.
Ƙarisawa na yi ina mai saɓe da yumna da ta fara barci a mota na ƙarisa wajen Gimbiya ina kiran sunanta amma ba ta ji na.

"Haba don Allah wannan ba girman ki ba ne. Ki zo mu tafi bangaren ki."

Amna bata saurareni ba, ganin kamar ba ta cikin hayyacinta yasa na saka hannu É—aya na rike ta ina fadin" Megadi na ji fa kar ki jawo mana mutane don Allah."

"Gwara ya ji. kowa ya ji cewa ba ya adalci. Maman Jidda yau fa yana dawowa shashen yarinyar nan ya tare na shiga na yi masa mgana a bangarena yake ya fara masifa shi bai san da haka ba. Ita kanta ta ce masa kin faɗa mata amma bai yarda ba ya kira ɗin ma ya tabbatar daga bakin ki amma ki duba fa a gabanki ya shige ciki saboda zalunci har yana rufe mini ƙofa saboda tozarci?

Ta faɗa tana kuka, abin da Yallaɓai ya yi bai kyauta ba amma ita ta ja ma kanta, da ƙyar na lallasheta na ja ta bangarenta. In da Allah ya taimaka yara suna bangarena tare da Baby. Haka na zauna ina ba ma Gimbiya haƙuri amma tana ta kara shan wallahi in dai ya kwana a bangaren Rabi'atu ba ta yafe masa ba

"Ki yi hakuri mana. Ki yi masa uziri tun da bai sani ba."

"Da bai sani ba amma ai yanzu ya sani."

Ta faÉ—a tana jan majina.

"Ki yi haƙuri zuwa da safe sai mu yi magana gabaɗaya "

"In yana so na saurare shi to ya fiti daga É—akin yarinyar nan in kuma ya kwana wallahi ba zan saurari kowa ba "

Jin haka yasa na ɗaga waya na kira Yallaɓai sai da ta katse na sake kira ya ɗaga ko mgana bai yi ba daga gani ranshi na ɓace ne.

"Yallaɓai don Allah ka fito mu yi magana."

"Ba zan fito ba. Ke ma ina mai ba ki shawara karki dame ni in ba haka ranki ya ɓaci."

Ya faÉ—a a fusace.

"Ka yi haƙuri ka fito don Allah."

"Ta ce Allah ya isa to zan kwana Allah ya bi mata haƙƙin ta kamar yadda ta ce."

"Ba za a yi haka ba. Ka dai yi haƙuri "

Da ƙyar na samu ya anince zai fito mu yi magana da ya fiton ma cewa ya yi ba zai shiga bangaren Gimbiya ba jan shi na yi zuwa bangarena mu ka yi magana, ina ba ma Yallaɓai haƙuri yana yi mini tsawa.

"Ina ruwan ki? Ki ƙyaleni kar ki dane ni "

"Kar ka yi haka. Ka je ka kwana ba gobe ba ne shike nan!

"Ba zan kwana ba "

Ya katse ni, sannan ya cigaba da faÉ—in" Kina faÉ—a mini wai ta fada za a dawo kwana biyu ni kun faÉ—a mini ne? Kuma ma haka za ta zo tana mgana da ni gaban Rabi'atu tana yi mini rashin kunya?

"Ka yi haƙuri ai ta fada mini laifina ne da ban faɗa maka ba"

"To kema ki fita idanuwana. Ke ce ke aurana da za ki riƙa yanke hukunci a gidana ba tare da sanina ba?

Ai ina jin haka sai na yi shuru, ya riƙa masifa har da rantsuwan  zai gyara bangaren shi da yanzu sai dai bishi can in ya ga dama ya kori kowa ya kwanta shi kaɗai.

"Ka yi haƙuri '

Nawa kenan ban haƙuri, dakyar na samu ya amince zai kwana a ɗakin Gimbiya.

"Ka yafe mata Allah ya isa da ta yi sheÉ—an ne "

"Ke ina ruwanki da abin da zan yi mata? Sadiya kina mini abin ba na so wai nan gidan gidan ki ne ko gidana?

Ina dariya na ce"Gidanmu dai Ranka ya daÉ—e "
Sai da na saka shi dariya. Na samu dai ya shige ban san yadda suka ƙare ba, yara ma a bangarena suka kwana da safiyar Allah Gimbiya ta bugo mini waya tana sharban majina wai da na sani na ƙyale Yallaɓai ya yi kwanciyarsa a in da yake so.

"Tun da ya shigo ya ke faÉ—a sai abin da ya manta bai faÉ—a mini ba. A falo ya kwana a kan kujera da asuba da na gaishe shi wai in na ma sake gaishe shi zai yi mini Allah ya isa."

Ni gabaÉ—aya ma sun sakani a tsakiya. Yallabai tun bakwai na safe ya fita na kira shi a waya
Yace kar na dame shi kamar ya san maganar Gimbiya ne ya taka mini burki.

"Sadiya in dai ba ke kika auro mini Saudatu ba to ki fita a mganata da ita. Tsakanimmu ne ba ruwanki."

"To ta zo tana mini ƙorafin kai ma kace in ta sake gaisheka Allah ya isa."

Kawai sai ya yi tsaki kafin ya ce" in ta sake zuwa ki kore ta. Ki faÉ—a mata ni na ce ba ruwanki"

Zan yi magana ya tare ni da cewa"Wallahi kema zan yi miki Allah ya isa in baki ƙyaleni ba haba."
Ai ina jin haka na kama kaina daga ƙarshe ya ce in na sake yi masa magana wallahi zai yi mana yaji kuma in ya tafi ba zai dawo ba sai ya ga dama."

"Abin har ya kai haka? To Allah ya huci zuciyarka "

Ya ce Amin a fusace ya kashe wayarsa tun da na ji haka na cire kaina a ciki. Da Gimbiya ta dawo tana faɗa mini wai ita Baban su Khalifa zai wulakanta saboda wata zaunar da ita na yi na faɗa mata gaskiya da cewa ta yi haƙuri ta kauda kanta a kan Yallabai da Rabi'atu in ba haka ba wata rana komai zai iya faruwa. Ta koma gefe ta zama yar kallo amma ba ta ji ba.
A cikin kwanakin ma sun sake wata rigima wai in ya shiga ɗakin Rabi'atu da daddaee zai yi mata sallama yana ɓata lokaci, rigima suka yi sosai Gimbiya ta sake masa Allah ya isa a kan haƙkinta shi kuma ya ce ya gaji ya ɗaga waya ya kira Nene ya faɗa mata. Sai da Nenen ta zo gidan sulhu ne na ji labari gabaɗaya ta taramu ta yi mana faɗa shi dai ta jadadda masa ya yi adalci ne.

"Nene ina iya bakin ƙoƙarina. Saudatu ta cika ƙorafi sannan ba ta da hakuri tun da na yi auren nan ba ta bar mu mun zauna lafiya bq"

Ita kuma tace me ya sa yake mata rashin adalci in yana da gaskiya ai ba za ta riƙa mgana ba.
Rabi'atu dai shuru bata mgana, Yallaɓai ya rantse ya ƙara rantsewa  in  Gimbiya ta sake masa Allah ya isa zai dauƙi mummunan mataki a kanta Nene ta yi mata faɗa ta kuma sakata ta bashi haƙuri nima ta yi mini faɗa da nariƙa nuna ma Gimbiya wani kuskureta in ta yi wani abun

"Ko ta nuna mata wannan zata ji ta ne? Wallahi Nene Sadiya ba ta taba ɗaga mini hankali da zan auero Saudatu  ba a wannan auren ma bata ɗaga mini ba. Amma kin ga wannan y'ar taki? Haƙuri na ne ya ƙare amma ta yi mini diɓar albarka ba adadi ina shanyewa."
Chapter 86 · 0% Book details