← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 103

Sashe 14

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jidda na ɗaki tun da suka daina zuwa makaranta in dai ba aiki za ta yi ba tana cikin ɗaki tana karantu Baby ce yar falo mu yi ta hidiman mu, itama ɗin yau ta na can falon Abban na su ta na zane zane a takardu ta bar ni, ni kaɗai ina ta danna waya ta. To tun da an kulle mu a gida sai kafafen sada zumunta suka zama ababen debe mana kewa. Na ji shigowarsa suna mgana da Baby a falo ban tashi daga zaunen da nake ba sai ga shi ya shigo cikin shigar ƙananun kaya ni Yallaɓai har mamaki ya ke ba ni shi bai son ya girma ba ne? Ko don jikinsa ba ya nuna shekarun sa? Ya kama kafar wajen shekaru arba'in da bakwai amma kuma yana jin kansa kamar ɗan shekaru talatin.

"Wannan kallon fa Madam?

Ya faɗa lokaci ɗaya yana jan hancina. Ashe ya ƙariso har gaba na ban sani ba.

"Ko na yi miki kyau ne?

Ya sake faÉ—a yana mini murmushi har yana kashe mini ido É—aya.

Sai na yi dariya kafin na ce" Wani kyau? Ina kallon ka ne, a raina ina cewa Yallaɓai na ya fara tsufa"

Yana zama gefena yana faÉ—in" Ko? Ke dai ce da mganarki amma ni har yanzu ji na, na ke yi kamar É—an saurayi mai shekaru talatin."
Sai na buge kafaÉ—ansa ina dariya kafin na ce" Jidda fa Æ´'ar ka ce? Ko ka manta ne?
Sai ya jawo kafaɗata saman tashi ya saka hannunsa guda ɗaya ya zagayo ƙuguna da shi.

"To sai me! Ke in ba fa na faÉ—a ba É—an Saurayi a ke kallona. Kuma tsab in na tsai da budurwa yar sha za ta tsaya mini"

Hararan sa na yi kafin na ce" Wai ko dai ƙara aure da za ka yi da yarinya ƙarama ne Yallaɓai?

"Me kika gani?

Ya faɗa yana dariya ƙasa ƙasa.

"To na ga da an fara mgana sai ka ce ko yanzu za ka iya auro yarinya yar sha sa'ar Jidda."

"To in ma da gaske ne Haramun ne?

Ai sai na buɗe baki ina kallon Yallaɓai. Ganin na kasa mgana ne ya sa ya rufe mini baki yana mini dariya sai na ture shi gefe ina hararan shi. Shi kuma ya na ƙara naniƙe ni ina ture shi yana minidariya.

"My Sady kishi"

"Ina ruwana ai ba a kaina za ta zauna ba kuma ai ni ka gama mini kishiya. Gimbiya ce a kan layi "

Dariyan nishaÉ—i ya yi kafin ya ce" Ka ji ta kamar gaske"
Na yi masa banza saboda na ga alamun ya na so maganar ya yi dariya ya na jin nishaɗi. Da gaske nake yi ai ni ya gama mini kishiya ko wata zai aura sai dai Gimbiya ta ji ƙwatan ƙwancin yadda na ji a lokacin da ya auro ta. Kallon sa nake yi yana tambaya ta Jidda na ce ta na ɗaki sai ya tashi ya shiga dakin na bi shi da kallo. Yallaɓai bai taɓa ce mini yana sha'awan tara mata ba amma ni a ƙasan raina na ke jin giyar kuɗi za ta iya ɗibar sa ya ji mun yi masa kaɗan kuma wannan wargajenjen filin da na ji labarin ya siya ba, ba iya ni da Gimbiya ba ne. Wataƙila shashen mata huɗu ne zai gina a hasashena tun da bai taɓa furta mini haka ba. Ya ce sai an gama ginin kamfanin shi an buɗe shi sannan zai fara ginin gida can kwanaki ma da muka bi ta hanyar na ga Kamfani ya yi nisa kaɗan ya rage a ƙarisa.

In ana misalin maza jajirtattu masu jajircewa da juriya to sunan Yallaɓai zan fara kamawa a shekarun da na san shi sama da shekaru goma sha takwas ya jajirce domin mafarkinsa ya tabbata na gina kamfanin shi, domin ya taimaki matasan da aikin yi to ko a haka ya tsaya wallahi ya cigaba domin matasan da suke aiki a ƙarkashin shi shi kan shi bai san iyakar su ba. Da masu ilimin da ma waɗanda ba su da ilimin duk na shi ne, masu ilimin suna aiki a bangaren ma'aikatan shi mara sa ilimin kuma suna aiki a bangaren kwangilan gine ginen shi. Kuma ya na da tausayi da kyautatawa ga kuma mu yadda ya ke kyautatama mu da iyayen shi, shi ya sa Allah ba zai bar shi ya taɓe ba.

"Ke wai me ke damun ki kike yawan shiga tunani ne?

Na ji yana faÉ—a lokaci É—aya ya na mai zama a gefe na. Har ya na wani jawo ni jikinsa yana shafa bayana zuwa kuguna sannan ya cigaba da faÉ—in.
"Uhm mene ne. FaÉ—a mini damuwarki yanzu na yi miki mganin ta."
Kamar abun arziƙi na ɗago ina kallon shi kafin na marairai ce ina faɗin" Yallaɓai wai yaushe za a buɗe gari ne? Tsakani ga Allah ba a kyauta mana ba da yanzu fa mun yi nisa da lectures"

Me Yallaɓai zai yi in ba dariya ba, har ya na ƙyaƙyatawa. Ni kuma sai na haɗe rai na koma gefe na yi bakam. Ina jiran ya taɓo ni sauke masa jin haushin shi da nake ji.

"Ai in za ki shirya zaman gida ki shirya. Domin cutar ma ƙara yaɗuwa ta ke yi ba ma maganar a buɗe gari."

Kallona ya ke yi fa yana tsintsira min dariya.

"Hajiyar Masters. Ki yi wannan master É—in ki a gidan auren ki, taho mu je ciki ni ma ai malamin ne sai na baki karatu"

Ya ma miƙo hannu ya kamani na bige hannun shi ina hararan shi amma bai saka ya daina dariya ba.

"Yallaɓai."

Na kira sunan shi a tsume.

"Na'am My Sady masu kwalin masters"

"Ni dai ko murna kake yi da faruwan wannan abin ne?
Ko daman can da ka ce ka bar ni na koma makaranta ba har zuciyar ka ba ne?

Na ƙarishe ina mai kura masa ido. Ya na danne dariyarsa ya ce" Wallahi har raina na amince miki. Ya za a yi na yi murna da haka?
Ya ƙarishe faɗa yana daga hannu sama amma bai daina mini dariya ba.

"Na ga kamar murna kake yi. Wato gara da a ka yi haka ko?

"Murna kuma! Da girmana Sadiya?

Ya faɗa yana sosa sajensa amma bai daina dariya ba kawai sai na miƙe fuu da wayata ina faɗin"Ohon in ma ka na murnan gwara da a ka yi ne gwara ka daina saboda ba ni kaɗai ba ce a gidan har da ƴaƴan ka"

"Kuma haka ne fa."

Ya faÉ—a yana kuma cigaba da dariya.

"Kuma in sha Allahu, za a buÉ—e gari kuma zan shiga makaranta Ehe."

Na faÉ—a ina mai barin masa falon sai ya biyo ni yana faÉ—a mini.
"In sha Allahu wa ya isa ya hana ki zama mai kwalin masters"
GabaÉ—aya Yallabai ya mai da ni abar nishaÉ—insa na so ina shige É—aki na rufe ne sai ya shammace ni ya biyo ni yana faÉ—in shi fa ba dariya yake yi mini

"Wallahi in na tuna yadda kika ci burin karatun nan sai na ji duk ba daÉ—i. Sorry My Sady in sha Allahu zaman gidan ba zai yi tsawo ba."

Wani kallo na yi masa saboda yana faÉ—a ne amma yana danne dariyan shi kawai sai na fusata na jawo filo na wurga masa ina faÉ—in.
" Ka fita Yallaɓai"
"Na je ina?
Har tsayawa yake yi yana tambaya ta, sai na ƙara rarumo ɗayan ina ƙokarin jifan sa da shi sai ya mamayeni ya rumgumeni yana mini dariya ni kuma ina fizge fizge sai ya fara min cakulcakuli a dole sai na yi dariya. Yallaɓai akwai mugunta wallahi sai da na yi hawaye, har fa sai da na ce masa zan yi fitsari a wando in bai daina ba sannan ya ƙyaleni. Bai bar gidan ba sai da na dai na fushi na dawo ina dariya ni ce har haraba na raka shi muna soyewar mu.

*****

Tun ina saka ran za a buɗe gari na yi registration ɗin makaranta har na cire rai ganin har mun shiga wata biyu muna kwararan na uku, sai na ce gwara na zauna na yi ma kaina tunanin mafita. Tun da karatu dai ba zai yuyu ba gwara na mai da hankalina kan sana'ar hijabai na da yadda zan ƙara ingata shi, sai na fara tunanin sunan da sanya ma kasuwancina. Da ƙwaƙwalwar ta ƙi sai na nemo Jidda na ce ta sama min suna. Haka muka zauna muna ta zaɓe har sunana ta haɗa ni da Yallaɓai SADYUF na ce ba na so da a baya ne zan iya haɗawa dashi amma tun da ya yo mini kishiya na fahimci Yallaɓai ba nawa ba ne ni kaɗai. Ta haɗa da haruffan sunanta da na Baby na ce ba na so sunan ya yi kama da na ma'aikatan Yallaɓai ne. HM TAFIDA AND SON'S LIMITED. Sai na ce a samu dai wani ganin zai yi wahala na ce kawai ta haɗa min da sunana, mun yi kwanaki ba a samu wanda ya yi min ba sai da na ce mata ina so na saro inears wear sai ta ce to bari a haɗa gabaɗaya. Da ƙyar dai Jidda ta samo min SADY S YASHE HIJABS AND MORE. Sai na ji sunan ya kwanta min arai nan take na ce bari mu tafi da wannan sunan kawai.
Chapter 14 · 0% Book details