← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 103

Sashe 50

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na faɗa ina masa dariya har ina aika masa da jinjina. Miƙewa ya yi bayan Jidda ta koma kitchen mai da kofin da ruwan, Yunma ke zillo za ta wajen shi sai ya ƙarbeta yana faɗin" Ke kuma za ki shiga wasan ne?
Ina jin haka da sauri na ce" Yallaɓai don Allah kar ku wahalar mini da ƴa'"
Amma ki saurarena bai yi ba sai ma ya juya yana ce ma su Baby" Mun samu ƙarin patner.'

Suka fara ihi kafin in ce me ina zaune an dadumar mini yarinya na miƙe ina kiran sunan Yallaɓai amma ya yi biris da ni shilla sama yake yi yana caɓewa maimakon ta yi kuka sai dariya kwantar da ita ya yi a ƙasan cafet yaran suka rufu kanta suma mata wasa suna kai mata hannu itama jaira tana kamawa.

Ihu na yi musu ina faÉ—in" Wallahi Yallabai kada kai da yaranka kun halaka mini yarinya to."

Ko sauarara na ma ba su yi ba da na ga za su ma yar da ni mahaukaciya sai na bar musu falon amma ina cike da fargaba kar su naushe mini yarinya. Kitchen na shiga na ɗibo abinci na koma ɗakina na ci na koshi, har lokacin ba su bar wasan ba har daga ɗaki ina jin iface ifacen su Yunma ina jiyo dariyanta na ɗauka za ta ga ji ta fara kuka sai ta ba ni kunya ko kukanta ban ji ba. Sai da aka kira mangariba Yallaɓai ya hakura da wasan nan ya zo ya yi wanka ya tara su Khalipa zuwa masallaci Yunma kuma an kawo mini ita ina ba ta nono na cire mata pampers na sake yi mata wanka da ruwan zafi sai barci ina ta masifa ni kaɗai.

"Ai dole ki yi barci kin sha wuya."

Falo ma da na fita bayan na yi salla kaca kaca Baby ba ta gyara ba ai da muryan ɓacin rai na fara kiran sunanta sai ga shi ta fito da hijabi alamun salla ta idar.

"Ke ubanki kika bar ma falon ya gyara ko ni?

Sai ta fara sosa kai kafin ta ce" Umma na gaji ki bari da safe sai na gyara."

"Ko mutuwa za ki yi yau sai kin gyara mini falo na aike ki ki yi mugun wasa har ki gaji?

Sai ta girgiza mini kai shammatanta na yi na ƙarisa gabanta tana shirin guduwa na damki kunnenta ɗaya na matse ina faɗin" ba ki da hankali ashe ban sani ba Maimuna?
Sai ta fara kukan shagwaɓa tana faɗin" Umma zafi kunnena."

"Ke namiji ce da za ki je kina wasan maza?

"Umma Abba ne ya ce na shiga."

"Abban ne ya ce ki shiga ko? Ya ce ki shiga dole ne? Ba ga Æ´ar uwan ki nan ba kin ga ita ta shiga ne?

"A'a"

Ta faɗa cikin kuka har ta fara hawaye, ƙara jan kunnen na yi ina faɗin" Wallahi in na sake ganin kin shiga irin wannan wasan sai na yi fata fata da ke a cikin gidan nan"

"Kin ji ko ba ki ji ba?

Na faɗa cikin tsawa da sauri ta ce" Allah ba zan ƙara shiga ba Umma."
Dundu mai lafiya na yi mata a baya sannan na sake ta ina faɗin" Ki ma ƙara ki gani ɗin. Maza ki gyara mini falo wawiya kawai kin girma amma kina cin ƙasa."

Sai ta yi gefe tana sosa kunnenta lokaci ɗaya tana faman hawaye daidai shigowar su Yallaɓai ganin tana kuka ya sa ya kalleni yana faɗin" Me ta yi miki kika da ke ta?
Na yi masa banza na wuce, ina jin sa yana faɗin" Sadiya ki daina duka mini yarinya fa. Na faɗa miki ba na so amma kin ƙi jin magana ta."

Na yi shigewata Bedroom ina masifa ni kaɗai yarinya na mace amma tana yin abubuwa irin na maza shi kuma Yallaɓai ba zai fahimci illa abun ba sai nan gaba ni ko ina uwa ba zan zauna in yi shuru ba.
Daga yaran har Yallaɓan ban ƙara ganin su ba sai bayan sallar isha'i da ya zo ya shirya ya ce mini za su ta fi saboda su Khalipa na fito ina da jakar lilipop na ɗauko na ba su shi da Anwar na Yumna ne da Suwaiba ta kawo mata tun da ta shan zaƙi, abinci ma na fara ba ta mai ruwa ruwa kamar tea kwai da sauran su ruwa daman tun haihuwanta na ce zan yi exclusive Yallaɓai ya ce ya bi Exclusive da gudu ba takalmi in har na yi ma yarinyar sa mugunta na hana ta ruwa bai yafe mini ba, shi ya sa ba mu yi ba sannan ga shi ta sha madaran yara sosai shi ya sa kullum ƙara ƙiba kawai Yumna ke yi tana ba ma masu ɗaukanta wahala ni kaina sai ina nishi in zan ɗaga ta.

Saboda Baby ba ta da hankali ta yi ɗamara za ta bi su, kallo ɗata kawai na yi mata ta shiga taitayin ta Yallaɓai na cewa ta ɗauko kayan makarantar ta, ta je can ta kwana cikin masifa na ce" Ba za ta je ba.
"Saboda mene?
"To me za ta je ta yi? Su Khalipa ne kuma ba ga su nan sati uku tare damu yau ne za su koma ba?

"To ina ruwanki tana son ta je. Ba ta gaji da ganin su ba."

"Sai dai ko ta mutu amma ba yau ba. Ba za ta je ba."

Yallaɓai zai yi magana na tare shi da faɗin" Wallahi ba za ta je ba, ka ji ma na rantse."
Yallabai ya kasa mgana ya kira sunana na yi kamar ban ji ba, na shafa kan Anwar ina faÉ—in su gaida mamannsu.
"Bye Umma."
"Bye Khalipa."

Na faɗa ina ɗaga musu hannu, na yi shigewata ɗaki ina jin idanuwan Yallaɓai a kaina na ki yarda ma mu haɗa ido. Ai suna fita na sake fita falo suna ɗakin su Jidda na ninke ƙananun kayanta da ta wanke Baby na kan gado tana kuka saboda na hana ta zuwa. Ban yi wata ba ta ɗaka mata duka a baya sai ta banƙare tana ganina ta yi tsalle ta yi ƙarshen gado tana matse kukanta.

"Kuka kike yi mini saboda wannan mganar?

Sai ta fara girgiza kai cikin kuka kafin ta yi magana na tare ta da cewa" To kukan me kika hau gado kina yi mana a cikin gida?

"Ba komai."

Ta faɗa  tana hadiye kukan ta.
Kallonta na yi kafin na wata dariya ina nuna ta da yatsa kafin na ce" Kin ga Jidda na yin haka? Ke ce mara jin magana ko? ke Yarinya ce?

Nan ma ta girgiza mini kai zare mata ido na yi kafin na ce' Wallahi ya zama na ƙarshe in sake yi magana a gaban babanki ki ce za ki yi mini gaddama kika ga yadda zan yi ƙulin kubura dake a cikin gidan nan."

"Ki yi hakuri Umma"

Ta faÉ—a cikin kuka sai ta ba ni tausayi amma ban nuna mata ba.

"Ki yi haƙuri Umma ba za ta ƙara ba."

Jidda ta faɗa cikin sanyin ta sai na yi ƙyafci na fita daga ɗakin fuu har ina bango musu ƙofar na koma ɗaki ina masifa ni kaɗai daga baya sai na koma ina dariyan kaina. Na rasa haushin wa na ke ji? Yallaɓai ko yayan shi? Tun daga cikin Yumna na samu wannan ɗabi'ar abu kaɗan yake harzuƙa ni in ta faɗa kan abin da bai kai ya kawo ba.

******
Jidda ta gama jarabawarta gabaɗaya sannan Walimar saukar su kuma za a yi a farkon watan August ne, sai kawai na ce za mu haɗe shi da waliman gradution ɗinta da birthday ɗin ta na cika shekara  sha tara a duniya duk da ta ɗan gota amma zan haɗa mata kayattaciyar Walima. Yallaɓai ne wani lokacin ko na ce za mu yi sai ya ce a'a na dai yi musu tun suna yara amma suna kawo girma sai ya riƙa hanawa iya fa mu kaɗai a gida amma sai Yallaɓai ya ce wai birthday haramun ne.

Wannan karon dai na ci karfin sa ya amince. Tun da har da Waliman saukar su sannan Amarya ta saka baki Gimbiya ba. Shi ya sa ya bari sannan ya saki kuɗi aka yi ta shirye-Shirye kuma dai daman Jidda is his fav Daugther. Ba wani gayya muka yi ba iya yan makarantan su na boko sai ƙawayenta na Tahfez su goma ne mata za su yi sauka sai maza huɗu. Sun yi ankon Hijabai masu ruwan ƙasa da dogayen baƙaƙen riguna sannan sun haɗa kudi kowa 20k amma Yallaɓai 50k ya ba ma makarantar suna ta godiya.

Ni dai daga gida na yi mata memo da yar jaka ƙarama, ita kuma Gimbiya ta yi mata kayan su Snacks, Mimisco ta yi mata sabbin kaya kala huɗu har da jallabiyoyi da takalma sannan ta yi mata jaka na takarda babba a ka saka hoton ta. Ai na ci dariya domin ni da na ce zan yi na hoto Yallaɓai ya tuma ya ce bai amince ba sai ga shi Mimisco ta yi da ya gani sai ya kasa magana. Anty Maimuna ta siya maltina katan goma da ruwan gora. Anty Bahijja ta yo abinci mai rai da lafiya, Suwaiba ta kawo mata sabon alqur'ani da casbaha. Naja ta kawo mata darduma na Makka da hijabi, sauka ne Jidda za ta yi da walimar Graduation amma ta samu kyatttuka sai da na yi mamaki kaf dangin Babanta sun nuna mata bajinta. Hatta Babanta Usman ya aiko mata da 50k. Ya Auwal Laptop sabuwa ya aiko mata da shi Ya Hamza kuma ya gwangwaje da kayan su chaculte kala kala sama da guda biyar. Musbahu kuma ya gwangwaje ta da sabuwar waya. Jidda sai da ta yi kuka da ta ga irin kayan da a ka haɗa mata Baby na ta tura bakin ba a kawo mata ba ta ce sai ta yi ƙoƙari itama ta sauke Qur'ani sai a yi mata abin da ma ya fi haka.
Chapter 50 · 0% Book details