Sashe 101
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rayuwar gidan Yallaɓai sai abin da ya yi gaba. Domin Rabi'atu mace ce mai tsananin kishi har ta ce ma Gimbiya ba ta iya kishin ba, ga ta da wayau da iya bariki, duk yadda Yallaɓai ya kai ga bacin rai a kanta ta san lagon sa. Ita kuma Gimbiya abin da ke cutar ta har yau rashin haƙurin ta ne da shegen saka baki a komai na yi na yi na raba ta da wannan halin na kasa sai na koma na zura mata ido. Ba sa sati ba su yi cacan baki ba lokacin ma ina Saudiya har Dambe suka yi Yallaɓai bai faɗa mini ba amma ita Gimbiyar da kanta ta faɗa mini. Kuma wai a kan yara ne ita Rabi'tu mace ce mai ƙulafucin ƴa'ƴa ba mai taɓa mata su a gidan nan ya zauna lafiya. Kuma suna ƙananu dole kan manya su taɓa su, masu taɓa su Yunma ce da Ammar iyayen mugunta ni wallahi ko suna yi ba na bi ta kansu ina bangarena Gimbiya ce take fitowa suna tanka tanka. Ga y'an biyun nan da tsiwa da tsokana su kuma su Yumna ba ɗaukan reni sai dai ka ji sun make su. In Rabi'atu na makaranta suna gida ƙanwarta Salima na wajenta tana makaranta tare da su Khalipa in tana gidan itama kamar yayarta ba ta bari a taba su in kuma yayar ta dawo ta faɗa mata ita kuma saboda rashin tunanin sai ta zo ta ce za ta rama musu. An ce hakan ce ya janyo faɗan Rabi'atu ta biyo Ammar har ɗaki wai za ta rama ma Ayush ya daketa. Gimbiya ta ce ba ta isa ba ta kai hannu za ta dake shi Gimbiya ta tare dukan ya sameta daga nan ta ce ita za ta daka ta saka hannu ta mareta sai Dambe. Yallaɓai na zuwa ya ce kowaccen su ta je gida shi gidan shi ba gidan Dambe ba ne shine suka je Gwammaja acan Nene ta kashe faɗan.
Kowa ya san Rabi'atu ce ba ta da gaskiya amma su Anty Bahijja ita suka goya ma baya saboda ta kama su a hannu ta riƙe gam! Kamar ta yi musu sujuda shi ya sa in suka zo gidan nan wani abu ya faru shashenta suke shiga Gimbiya ce ke bin su can ta gaishe su ni dai ko sun ƙi ko sun so na zama turken gida a gidan Yallaɓai ba su da yadda za su yi da ni. Sun buga da ni sun gaji sun bar ni, na san ba zan taba fari a idanuwansu ba, nima ban matsa ma kaina sai sun so ni ba, da man ba kowa ba ne zai so ka, wani har gaban abada ba ya sonka, sai dai in ya gaji ya hakura da adawa da kai in ya ga kafi karfin shi.
In sun zo gidan Har shashena za su leko sannan mu gaisa tun ballatana da suka fahimci ni yanzu ba na ta kansu sabgogina sun sha gabana.
Rabi'atu Da Gimbiya sune faɗa kan turaka ƙananun mganganu dai ba sa ƙarewa. Ni kenan kullun ban hakuri ko faɗan aka yi in Yallabai ya dawo ko da Rabi'atu ce ba ta gaskiya ta iya lauya in ana ma yar da mgana sai dai ta zauna kanta a ƙasa tana kuka ita ko Gimbiya harshe a sama shi ake  cutan ta Yallaɓai kuma ya tsani yana mgama tana mgana yanzu zai harzuƙa kuma da man kuranta ta yi kuka a wajen shi ya riga ya making ɗin ta a matsayin mace mai fitina, in kuma ranar da ya ke jin tsiya ne sai ya ce har da laifina wai yanzu ba ni da amfani a gidan ni ko ta kan shi ba na bi, to lokaci da na ke gidan kenan da na fara fita shago nima ba na gidan ban san sun yi ba,
Kuma sun fi yi da daddare tun da Gimbiya ma na zuwa shagon ta itama Rabi'atun makaranta ba yini muke a gidan ba sai dare ya yi in sun haɗu a yi ta hararan juna. Ni wallahi dariya ma suke ba ni, Gimbiya ce duk ta bi ta raina kanta shi ya sa Rabi'ar ta raina ta Yallabai da man tuni ya dawo rakiyarta tuni aka daina kiran Daughter Saudatu ne itama Baban Khalipa ko Baban su Jidda. Ita kam Rabi'atu Abba ne ko Yallaɓan mu ni kuma da man yara da su kan su Umma ne har Gimbiya yanzu Umma ta ke kirana har Yallaɓan ma in yana jin nishaɗi Umma Sadiya ya ke kirana in kuma zai kirani har yau har gobe Sadiya ta ne ko abar ƙaunata nima ko shekara ɗari ya yi a duniya ba zan iya daina kiran shi da sunan Yallaɓai na ba, domin na riga na saba.
Matsalan da ke faruwa yanzu shi ne ita Rabi'atu tana ware ya'yanta tana nuna kamar dabam suke, shi kuma Yallaɓai ba zai aminta da haka ba ya yi mata faɗa ta ƙi dainawa ya faɗa mata ya'yan shi duk ɗaya ne kar ta zo ta nuna bambamci ta raba masa kan yara amma ba ta jin mgana. Ko a cikin satin nan sai da Baffanta ya zo kwana biyu ta hana yara fitowa a bangarenta take kulle su suna son fitowa su yi wasa da y'an uwan su ta ki barin su.
Tun ballanta sun saba da wassanin su a haraba har raga na ƙwallo Yallaɓai ya saka aka saka musu a haraba in yana gida Weekend zai ta wasa da su shi ne su yi ƙwallo wasan gudu, chinese wasan ɓuya to yaran sun saba da wassani ko baya gida za su fita haraba su yi ta yi. Yunma ma da ke mace in ta ware kafa ta kai duka kamar wata namiji Yallaɓai duk ya gama koya ma yara wasan banza ko a jikin shi, mu kan mu in za mu fito zai so haka tuni ya ce mu riƙa fitowa muna rage kitse na ce ni kam ya ƙyaleni da kitsena. Ni ban ma kai su Gimbiya kiba ba su ne sun zama wasu Hajiyoyi da su ni dai na san na yi kiba amma ba ta yi mini muni ba, ko don bana haihuwa ne su kuma suna haihuwa da wannan ta sauke wannan ta ɗauka sun ma yar da abin na su gasa.
*****
*RUFEWA.*
Lahadi
20 DECEMBER 2025.
A sati sau biyar na ke zuwa shago ina da mai ɗan taimaka mini Nana ce ɗiyar mai yi mini kitso Maman Nana ta gama sakandiri ba ta shiga makaranta ba. Yanzu haka muna stimin, saloon, wash and set, kitso gyara kafa na ke so mu fara tun da ina shiga clases ɗin online ina ƙarin sanin wasu abubuwa. Ba na zuwa asabar sai dai Nanan kaɗai ke zuwa duk na koya mata ba abin da ba ta iya ba. Sai Baby ta kan leka itama ranar asabar ko in ba ta shiga makaranta ba tun da itama ta yi sauka an yi musu walima a Tahfiz.
Jidda ma in ta dawo hutu tana zuwa, ita yanzu ta yi ƙarfi wajen yin snaks, in dai ta dawo hutu tana yin na biki da na birthday.
Ranar lahadi kuma muna gida ba ma buɗe shago. Haka itama Gimbiya dukkan mu muna gida muna kula da mijin mu da yaran mu. Yallaɓai ma ba ya fita ranar ta iyalai ce.
Ranar duk muna gida gabaÉ—aya har Jidda na gida ta zo hutun karshen shekara.
Da ni da su da yara tare da Gimbiya mun je min duba Hajiya Iya da hawan jini ya kwantar da ita mun ɗan jima a Gwammaja sai gabda mangariba muka dawo gidan Rabi'atu ba ta je ba, tana fushi da mu gabaɗaya daga mijinta ya yi mata faɗan in ba ta daina rufe su Ayush a ɗaki ba za su samu matsala ta bar su su fito su yi wasa da yan uwan su in ba haka ba ranta zai ɓaci shi ne ta yi ta kuka tana kumburi tun da ya yi mata faɗa a gaban mu shike nan ta daina ma fitowa shi kan shi mijin ƙamshi ake shakar masa sai dai ya bita cikin ɗakinta mu dai ba ma bin ta yara dai ta ji faɗa ta barsu yau ɗin ma tare muke je Gwammajan da su bayan mun dawo ma a shashena muka ya da zango. Yallaɓai dai ya ce yana ganin har da cikin da ke jikinta ke saka ta fushi, ga kishi ko mgana ce yanzu in ta ji mganar kishiya za ta sauya fuska ta fara kumbura. Ita a dole ba ta son wata ta shigo. Kuma duk abin ta in Allah ya so Yallaɓai zai cike ƙofa.
Can kwanaki ma har ma'aikatan shi ta riƙa zuwa lokacin da ya dauƙi wata sakatariya, tun da yanzu kamfanin ya na ɗaukan ma'aikata mata, ba ta yi sukuni ba sai da ya maye gurbinta da namiji sannan hankalin Rabi'atu ya kwanta.
Ko Gimbiya yanzu ta shafa ma kanta lafiya ba ta wani rawan ƙafa a kan Yallaɓai.
GabaÉ—aya ita ma ta tattara shi ta bar ma Rabi'atun.
Mun dawo mun iske Yallaɓai ba ya nan ya fita, ni ce ma na kira shi a waya sai ya ce mini ya ɗan fita ne zai dawo ba daɗewa ba. Da ya ke ni ke da shi a turaka shi ya sa muna dawowa na zage na shiga na share falon na gyara bedroom na wanke tiolet, na ɗauko sabon zanin gado na shimfiɗa wani ja mai love a saudiya na siye shi, sannan na koma bangarena na shiga kitchen na ɗora ruwan zafi a tukunya.