Sashe 24
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin haka ya sa na yi shuru ban ƙara masa mgana ba. Zuwa can sai na ga kamar da gasken barcin ne ke fizgan sa, sai na rage ƙaran talabijin ɗin domin kamar ya dame shi. Daga baya ma da na ya fara barcin hani'an sai na kashe kallon a nan falo na koma falon su Jidda na kunna na cigaba. Har ta gama soya dankalin mu ka ci ni da ita. Baby na ɗakin su daga wasa ta bingire da barci sai la'asar na saka Jidda ta tashe su. Yallaɓai ma sai da na tashe shi sannan ya iya tashi da gaske yake yi yana da gajiya a jikinsa. Duk sai ya ba ni tausayi yana da ƙoƙari sannan ni kaina zan iya ba da shaidar mijina jajirtattace ne. Sai na ce masa ya bari da daddare ya sake wanka da ruwan zafi na ƙara shafe masa jikinsa da man zafi in sha Allahu zuwa gobe ƙasusuwan na shi da suka rirriƙe za su sake shi ya ce da ko ya yi ta saka mini albarka.
Haka ko na yi masa zuwa washe gari tun asuba da muka tashi salla ya ce minI ya ji daɗin jikinsa. Ni kuma sai na mayar masa da martanin ya riƙa siyan man zafi ko ya na can gidan Gimbiya ne in ya ji kasusuwansa sun riƙe sai ya gasa jikinsa ta shafa masa. Nan ta ke ya ce ai tun da ya ji daɗin sa shi zai riƙa siya.
Haka rayuwar dai ta cigaba da gangarawa yau a ji daɗi gobe a damu akasin sa. Gefe ɗaya ina cigaba da renon cikina da ya yi wani irin girma na ban mamaki ni ma ya mai da ni wata ƙatuwa. Shi ya sa ba na son fita sai ya zama dole. Daga asibiti sai gida ko Ɗorayi na daɗe ban je ba. Tun wani zuwa da na yi daga asibiti na biya na gai da su Gwaggo ban koma ba amma dai ina mgana da su Ya Aina ta waya muna gaisawa.
Siyayya kayan haihuwa kuɗi Yallaɓai ya ba ni muka je kasuwa ni da Jidda muka siyo komai da komai sai abin da ba a rasa ba. Da ya ke tun scan ɗin da na yi ya nuna mace zan haifa kuma ko Yallaɓai ban faɗa mawa ba. A raina na ji ko da macen na samu tabbas zan yi ma Allah godiya. Tun da ya yi min ni',ima a farko a yanzu ma ya sake zaɓo ni cikin dubu ya sake ba ni wannan ni'imar. Itama Jidda zencen ta kenan Umma ki hai fa mana baby mai kyau mu yi ta renon ta ni da Baby. Itama Babyn macen ta ke so Yallaɓai kuma daman bai da zaɓi duk abin da na haifa ya na maraba dashi.
Cikina na shiga wata na bakwai sai ya fara yin ƙasa. Mutane da dama sai su yi ta cewa namiji zan haifa saboda yanayin girma cikin. Ni kaina ina mamakin girman shi, ban taɓa yin ciki mai girman shi ba, ko na Jidda da ya ke na farko ne, jikina ya bi gwara ma na Baby ya ɗan yi girma. Amma shi wannan girman shi na dabam ne. Ban taɓa saka ma zuciyata ina son sai na haifi namiji ba. Abin da nake addu'a a duka khamsul salawati ɗina shi ne Allah ya sauke ni lafiya. Jinsin namiji ko macen duk wanda Allah ya ba ni, ni mai gode ma ni'imarsa ne.
Kuma ni ban taɓa lura da cikin nan muni ya saka ni ba. Ban cika kallon madubi ba ta kaina na ke yi. Sai da za mu je gai da Mimisco ta yi fama da zazzabi ni da Yallaɓai da yara. Su sun rigani fita ni kuma na tsaya ɗauko makullin gida da hijabina har ƙasa na tsaya rufe gida tuni na ce ma Yallaɓai ya samo mana megadi ya ƙi. Wai a wannan a kurkin gidan ne sai ya wani saka megadi? Na bari in ya gina wancan babban gida sai ya ɗauki megadi amma ba a nan ba.
Na fara takawa sannu a hankali zuwa wajen mota. Sai da na ƙariso na ji Yallaɓai na dariya shi da ƴa'ƴan shi. Ban ɗauka da ni suke ba na ɗauka labari ya ke ba su na abin dariya shi ya sa ban damu ba na buɗe mota da ƙyar na shiga na zauna a bangaren mai zaman banza na gidan gaba sai da na gyara zama sannan na ce.
"Na ce motar na kama da za a hau foo ka ji haushina Yallaɓai. Yanzu don Allah ga irin mu masu lalura ai sai yaro ya jirgice a ciki saboda wannan motar ta ka."
Sai na ji sun ƙara kwashe minI da dariya har da Jidda da nake gani saliha ba ruwanta. Sai na waiwaya ina kallon su nima ina ta ya su dariyan. A tunanina maganar da na yi ta saka su dariya ashe ni ce suke yi ma dariya kamar sun samu cortoon.
"Yallaɓai."
Na kira sunan shi cikin mamaki ganin yadda yake dariya har ya na kwantar da kan shi saman sitiyari. Na fara zargin da ni yake saboda na ga sai ya kalle ni sai ya ƙara tsintsirewa da dariya.
"Me kika gani?
Ya faɗa ya na kuma cigaba da dariyan. Sai na ɗan tsume kawai na juya ina kallon gefen window ni kam ai na daina biye ma Yallaɓai tun da ya ce mini wai nishaɗi na ke bashi. Haka kurum zai ta sa ni yana mini dariya ko ya yi ta ja na da mgana ko faɗa sai na fara masifa sai ya koma gefe yana mini dariya. Tun da na fahimci mahaukaciya ya ke son mai da ni na fita sha'anin sa. In ya na dariyan shi ba na bi ta kansa.
"Wai uban wa kuke yi ma dariya?
Na faɗa cikin ƙufula. Ganin har su Jidda ban daina jin tashin dariyan su ƙasa ƙasa ba.
Sai suka yi tsit kamar ruwa ya ci su. Yallaɓai kuma ba ni da yadda zan yi dashi shi ya sa na kallon shi a ɗage sannan na ɗauke kaina sama ina hura hanci.
"Me suka yi miki? Ba su suka kai zomon ba."
"To dariyan me kuke yi? Haka kurum ku ta sani kuna yi mini dariya?
Na faɗa har ina yarfa hannu. Zaune kawai na yi ina kallon Yallaɓai na kallona ya na cigaba da dariyan sa. Tuni na harzuƙa na cika saura kiris na fashe.
"Me ye abin dariya a jikina?
Na faɗa ina kallon shi ganin da ya yi a fusace na yi maganar ya san yanzu nan zan birkice musu. Ya kuma san halina ba ni da sauƙi.
"Wai. Sannu Hajiya Dubu."
Ya faɗa ya na kallona har ya na ƙwarewa saboda dariya. A raina na ce Allah ya ƙara. Saboda ai dariyan ta mugunta ce.
"Ban taɓa tunanin sunan da Alhaji ke kiran ki dashi ya dace da ke ba sai yau."
Sai kawai na koma ina bin kaina da kallo. Rarrashin kaina na ke kar na kai ma Yallaɓai duka. Sunan nan ban da Alhajinmu da Gwaggo na haramta ma kowa ya kira ni da sunan nan saboda ba na so. In wanda na ke jin kunya ne ba na mgana amma in har ba na jin kunyar nan ta ke zan maka in karin da cewa ni ba sunana Dubu ba. Yallaɓai bai cika tsokana da sunan ba sabo da ya san yadda na fi tsanar sunan gwara ma a kira ni da Sadiya ƴar laushi. Amma yau
Saboda cin mutumci yana kirana da shi a gaban ƴa'ƴa na bayan ya tara su suna yi mini dariya.
Da dai na fahimci yadda ciki ya mai da ni suke yi ma dariya sai ban ƙara magana ba. Ya gama dariyan shi ya na tsokanata da mgana na yi masa banza. Su jidda kan sun yi tsit sun san halina wallahi yarinya ta ƙara mgana sai na yi mata bugun tsiya. Tun da uban su ba zai dakun mini ba to ai su ni na haife su zan yi iya hawa ruwan cikin yarinya na yi mata lilis ba mai ce mini me ya sa? Baby ta fi shan dukana domin da cikin nan ban san a dadin dundu da rankwashi nawa ta sha ba. Ita Jidda ba ta cika laifi ba ina son yarinyar ta na da gudun zuciyar iyayenta.
Bar muka isa gidan Mimisco a tsume nake. Ita kanta sai da ta yi maganar ta ga raina a ɓace me aka yi mini. Cikin jin haushi na ce" Wai Yallaɓai ke mini dariya saboda ciki ya sa duk na zama cus. Har yana tara su Jidda suna kallona suna mini dariya.
Tsabar yadda abin ya tsaya min a rai sai da na ji hawaye sun kawo minI. Ita ko da yake ta san irin yanayin nan da nan ta fara masa faÉ—a.
"Kai shike nan haka ake yi? Sai ka yi ta mata dariya? Waye silan da ta koma haka in ba kai ba? Ka daina tun da ta ce ba ta so don Allah Tafida ka daina. Ka san yanayin masu ciki sai a hankali in suka ce ba su so abu gwara a bar shi zai fi alheri."
"To na bari shi kenan?
Ya faɗa ya na kallona kuma ya na ƙara mini dariyan yadda zuciyata ta kawo a lokacin duk da a gaban yayarsa ne sai da na shammace sa na kai masa bugu a gadon bayan sa lokaci ɗaya kuma na fashe da kuka domin ji na yi in ban yi kuka ba kamar zan mutu saboda haushi.
"Kin gan ta ko Mimisco? To kuma ta dake ni, ni ban yi kuka ba sai ita?
"Tashi ka fita ka ba mu wuri."
Da haka ta fattake shi,ya fita can falon mijinta ni kuma sai ta koma ta ba ni haƙuri.
"Ki yi haƙuri Sadiya. Kin ji ko?
"Mimisco na gaji da abin da Yallaɓai ya ke yi mini a cikin gidan nan. Abu kaɗan sai ya ta sa ni a gaba ya na mini dariya."
Na gama faɗa bilhaƙki da gaskiya ina sharen ƙwalla sai ta taso ta zo gefena ta zauna ta na bubbuga bayana alamun lallashi.