← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 103

Sashe 23

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dirowan gado na jawo na ɗauko na fara sha fa masa kafaɗunsa zuwa bayansa ya na tambayana in da na samu man zafi na ce Gwaggo ta ba ni ta ce na riƙa shafawa a kafafuna da suke kumbura.

"Ba kumburi ba ne tsabar cin abinci ne ko?

Ya faɗa yana dariya sai na lakato na shafa masa a fuska ya ji zafinn yajin  ya sa ya kare fuskarsa yana faɗin" Makanta ni kike son yi Sadiya?
Ni kuma ina ta dariya ina faÉ—in" Ka kara cewa ina da cin abinci. Wai ba É—anka ba ne ke saka ni cin ba?

"Shi ne."

Ya faɗa yana danne dariyan shi. Haka na gama shafa masa muna hira nima har sha fa mini ya yi a ƙafafun nawa sannan ya saka kaya. Yau a bedroon na kawo masa abin ƙarin bayan ya gama na kwashe na mai da kitchen su Jidda ma sai da suka biyo sa suka gaishe shi a ciki.

Nan na bar shi na je falo muna duba hijabai ni da Jidda. Jiya suka iso na ce ta ɗauko list mu cire ma waɗanda suka saka oder. Can na ɓata lokaci ko da na koma ɗaki na ɗauka zan gan shi ya na barci amma sai na iske shi zaune yana waya ina shigowa ma ya gama wayar.

"Yallaɓai ba ka kwanta ba?

"Yanzu waya ta tashe ni."

Sai na zauna kusa da shi ina matsa masa kafaÉ—anshi.

"Sun daina ciwo?

"Sun yi sauƙi."

Ya faɗa yana kallona. Sai na sake shi ina faɗin" Yallaɓai ni fa ina son ka fara koya mini mota."

Daga maganar arziƙi sai kawai na ga Yallaɓai ya kalleni ya wani kwashe dariya.

"Mota? A hakan ne za ki koyi mota?

Ya faÉ—a ya na kallon cikina. Sai na fusata a kuma fusacen na ce" E a hakan ko ba za ka koya mini ba ne?
Na fada ina haÉ—e fuskata ganin yana ta mini dariya sai ka ce na faÉ—in abin dariya.

"Ko ba za ka koya mini ba ne. Na je wajen da ake biya na koya?

"E to gaskiya domin ni ina na ga lokacin koya miki mota fisabilillahi Sadiya? Wai ma to ke kina da motar ne da kike son koya?

"Ba ni da shi amma ina da niyar siya ne"

"Da wani kuÉ—in?

Yallaɓai ya faɗa har yana tagumi.

"Da kuÉ—ina mana"

"Kina da kuÉ—i ne da man?

Tambayoyinsa sun fara ƙular da ni ya sa a ɗan tsume na ce.

"Ai ba zaman banza nake yi ba kasan ina da sana'ata."

"Wai da riban hijaban ne za ki siya mota da man?

Sai kawai na kalle shi na kasa mgana. Me Yallaɓai zai yi in ba dariya ba har ya na duƙawa rike da ciki.

"Ke yanzu daman kin san riba ake samu haka tsagwa gwa shi ne ba ki faÉ—a mini na saka hannun jarina ba? To wai kamar nawa yanzu kika tara na siyan motan?

"Ban sani ba."

Na faɗa a fusace ina mikewa da cikina gaba. Har na bar ɗakin Yallaɓai na tintsira mini dariya abin ya yi mini ciwo. Kuma wallahi zan bashi mamaki da ni yake zencen.

*Janafty**TKG0B3F06*

Duk da na bar ma Yallaɓai ɗakin sai da ya ƙara biyo ni falon. Ina zaune ina cin dankalin hausa ɗanye kitchen na shiga na ga Jidda na ferewa wai shi ta ke sha'awa za ta soya ta ci nima nan take na ji ya shiga raina sai na ce kawai ta fere da ɗan yawa sai mu ci gabaɗaya. Shi ne kafin na taho na ɗauki wanda ta feren ƙarami na wanke na taho da shi falon Yallaɓai na zauna ina gutsira a hankali ina jin daɗin sa a bakina da cikina gabaɗaya.

"Aa Hajiyar mota nan kuma a ka dawo?

Wani kallo na yi masa amma ban yi magana ba. Yana dariya ya zagayo ya zauna a gefena yana faÉ—in.

"San mini dankalin"

Ya faɗa ya na kamo hannuna na yi saurin fizgewa ina ƙara haɗe rai.

"Ba za ki ba ni ba?

Nan ma na yi masa shuru. Saboda ganin har lokacin bai dai na yi mini dariya ba. Maganata ta zama a bar dariya a wajen shi shi ya fi ƙular da ni kuma ni har a cikin zuciyata da gaske nake yi zan koyi mota saboda nima ina son wata rana na ganni ina tuƙa mota da sunan tawa ce.

"To fushin duk na mene ne Madam?

"Ko duk  fushin na ce ba ni da lokacin koya miki mota ne?

Sai a lokacin na kalle shi ta gefen ido kafin na ce" Na me! Abu na kuÉ—i zan je na biya a koya mini kasha zaman ka."

"To ni me ya sa zan bari wani ƙaton banza ya koya ma matata mota?

"Haka ka so."

Na faÉ—a a tsume kuma cikin gatse sai ya gimtse dariyan sa lokaci É—aya yana faÉ—in" Ba za a yi haka ba. Yanzu dai ki bari in na samu dama zuwa ki haihu sai na koya miki."
Na yi masa shuru ban ƙara magana ba amma ina ta gutsiran dankali da ƙarfi yana ƙara saboda haushi.

"Kan lokacin ma ƙila abubuwa sun warware na sauya mota sai kawai na bar miki nawa Hajiya ta."

"Ba na son wannan motar."

Na faɗa da sauri ina kallon shi fuskata ba fara'a saboda ni fa gani na ke yi kawai Yallaɓai zama ya yi ya na ci mini fuska.

"Sabo da mene ne?

"Ba na sonta ne. Mota kamar za ka hau foo?

"Foo kuuma?

Yallaɓai ya maimaita cikin alamun tambaya.
Sai na gyaÉ—a masa kai kafin na ce" E. Ni zan siya mota ta mai kyau irin ta mata."
Yallaɓai sai dariya yake yi yana kallona.

"Wai miye? Na zama abin dariya ne?

Na faÉ—a a tsume fuskata a murtike ba ko fara'a.

"Ke yanzu motar tawa ce kamar za a hau foo? Lalle kin ma raina mini wayau. Motar nan ma a gan ki a ciki duniya ne hajiya amma tun da kin raina shi kenan. Zan siya miki ta mata ko irin ta Daughter satin da ya wuce ta sauya mota wata Vibe mai kyau ta mata kina son irin ta na siya miki?

Bai ba ni zarafin mgana ba na ga ya É—auko wayarsa ya latsa sai ga hoton motar yana nuna mini tana da kyau. Sai da na gama gani sannan na ture hannun shi ina faÉ—in" Ba na son irin ta. In ta shi siya ai ni na san irin wacce nake so"

Kawai sai ya riƙe baki cikin mamaki ni kuma sai na juya masa ƙeya ina faɗin" Kuma saura ka ce wai saboda matarka na da mota ne, nake son siya. Ni kawai ina so ne saboda nima na faso gari na dai na garari a cikin Adaidaita sahu."

"Yaushe ne kike garari a cikin adaidaita sahu Sadiya?

"Ba na yi ne?

Na juya a fusace ina tambayarsa.

"Fisabillahi fa Sadiya"

Gani na yi magana da shi ma ƙara ɓata minu rai yake yi ya sa kawai na tashi na sauya kujeran zama na bar shi yana mini dariya. Tunani nake yi wata ƙila shi da matarsa sun shirya ne can kwanaki bai ko zencen ta in ma zencen ya zama dole sunanta ya ke kira kai tsaye. Yau ko tun da ya kira ta da sunan da ya ke kiran ta dashi na san sun shirya. Saurin kauda tunanin na yi ina mai faɗin miji da mata sai Allah tuni zai lallasheta su shirya har yana wani ɗaukan hoton mota ya na nuna mini saboda iyayi.

Ina ta hararan shi ta gefen ido lokacin yana amsa waya ne. Bayan ya gama kawai sai ya ɗau remot ya chanza tasha. Daga MBCBOLLYWOOD suna haska wani indian film mai suna Khabi kushi kabhi gham. Tsohon film ne mun kalle shi tun muna da ɗan wayau ina son film ɗin kawai ina cikin kallo Yallaɓai ya sauya mini tasha ya kai can wani tashar turawa a na rawa.

"Haba Yallaɓai ya za ka sauya mini tasha?

Na faɗa a ƙufule sai kawai ya kalle ni bai yi magana ba ni kuma na mike a fusace na je na karɓe romot ɗin hannun shi na mayar tashar da nake sannan na koma na zauna ina girgiza ƙafafuwana saboda yadda na ke jin ɓacin raina nw hauhawa.

"Allah ya ba ki haƙuri ban san kallo kike yi ba."

"Kallo na ke yi mana. Ko da ka shigo ba shi ka iske ni ina yi ba?

Na faɗa ina mai ƙure sa da ido fahintar da ya yi a fusace nake da shi ya sa koma ya jingina a jikin kushin ɗin kujeran ya na mai dannne dariyan shi.

"To miye abin faɗa anan? Na ce ki yi haƙuri ban sani ba ne?

Ɗauke kai na yi na mai da hankalina wajen kallon. Shi kuma ina ganin shi yana ta dariya ƙasa ƙasa.

"Na gode Yallaɓai na zama abin dariya a wajen ka "

"Kai na shiga uku. Wai dariyan ma ba zan yi ba?

"E in dai a gaba na ne to zan ce ni kake yi ma dariya?

Na ƙarishe faɗa ina zaro masa ido sai kawai ya koma ya kwanta a saman kujeran har yana miƙe kafa kafin ya ce" Ke dai ke ce yanzu kin koma rigimmaniya abu kaɗan sai ki yi zuciya ki hau faɗa. Allah ya baki haƙuri ni kin ga ma barci na ke ji"

"Ka je É—aki mana. Nan ai ba wajen barci ba ne"

"Ni da gidana sai an zaɓa mini in da zan kwanta?

Ina ƙoƙarin mgana ya yi saurin dakatar da ni yana daga kwancen bai taso ba ya ce.

"Ki ƙyale ni na yi barci Sadiya. Ba zan iya da rigimar ki ba."
Chapter 23 · 0% Book details