← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 103

Sashe 77

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Auwal ya ce na saka karikitai mana, ina laifi Ya Hamza kuma ya ce ni na ma samu duniya tun da har falo  huɗu Yallaɓai ya yi mini. To ya cika ladan shi ya yi kayan ɗakin mana ni dai na yi dariya ban yi magana ba. Na san ba domin hidiman auren da ya ɗauko ba Yallabai zai iya yi mini abin da ma ya fi haka in dai bai fi ƙarfin shi ba. Amma dai yanzu kan bam ma saka rai ba shi ya sa nake ta fafutakana na samu na rufa ma kaina asiri.  Har a raina ban saka rai da samun wasu kuɗi daga Yallaɓai ba, sai ga shi ya ba ni 200k ya ce ba yawa yara kuma 100k  na yi musu siyayyan kayan fitar biki na yi ta godiya domin ban yi tsammani ba. Atamfa kawai na siya mana sai leshi sauran kuɗin na adana, da gayya da Munnira ta yi mini maganar Anko na ce a fitar mana da shi, nan take ta fitar mana da kamfala mai ja da ruwan madara mai kyau, kuma ni na tura ta a group ɗin gidan su Yallaɓai na ce ankon bikin Yallaɓai, kalilan ne suka fito suka yi magana amma su Anty Bahijja gum, na san kuma na sha zagi da man kuma ina kan sha ne.

Ai wannan ankon da na fidda kamar za su saka ni a cikin wuta. Yallaɓai ko da ya ji labari daɗi ya ji nan take ya sake tura mini 50k namu ni da yara har da Gimbiya da aka kawo na aiki Jidda ta kai mata sai ta dawo mini da shi da cewa Allah ya kyauta ita ba ta so, da ya dawo na faɗa masa tsaki kawai ya yi kawai ya ce na yi kyauta da shi. Ho ho ina shan zagi, Mimisco ta ce abin da na yi ya yi dai dai, hankalinta ya ɗauke ba ta yi tunanin haka ba, ba takura wanda ya ga dama ya yi wanda ba zai yi ba, ba takura. Su a cewarsu miye na fidda anko? Ai sai a jira a fidda a bikin Adnan na ce kowa da ranar auran shi saboda haka mu dai mun fidda wanda ya ga dama ya yi, wanda bai ga dama ba ya bar shi.

Su Suwaiba ce kawai suka siya sai su Jawahir, Halima kuma Jamila ta kirani a waya tana faÉ—a mini irin zagin da ta zo gidanta tana yi mini wai ba na kishi ina ta murna har ina fidda anko. Kamar zan kirata na ja mata kunne sai na fasa na ce bari na jira bikin na ga ni in ta isa ta hana abin da Allah ya tsara. Ni dai da tawagata muna gefe muna shirin mu Ankon Gimbiya kuma Rahila na ba ma ta É—inka har Amina ta siya za ta zo mini biki. Gimbiya ba ta gayyace ni tariya ba, ban kuma san za ta tare ba sai a bakin Hauwa na ke ji ta tare a sabon gida a ranar 31 ga watan December, na ce Allah ya sa rai ya mora, ba ta gaya mini ba ban kuma je ba shima uban gayyar bai sanar da ni ba.

Hauwa dai ta je amma Munnira ba ta je ba, ita ta zo mini da labarin ina shan zagi wajen su Anty Bahijja na ce sai su yi ta yi, ni kam ba sa gabana. Sun ce wai tarewaar ma saboda ina da mugun nufi na ce sai daga baya to tun da na nuna haka shike nan sai mu zuba su gani. Na rasa me na tare musu suka ɗora mini karan tsana, ga Ɗan uwan su da zai yi aure ba su yi masa haka ba sai ni? Miye nawa saboda nima ban yi haukar da Gimbiya ke yi ba? To in dai haka ne sai dai su yi ta tsana ta amma ni ba zan yi wannan haukar ba a baya ma ban yi ba, ballatana yanzu da girma ya kamani ba ruwana. Su je su yi faɗa da Yallaɓai shi da ya ɗauko auren ni dai ba ruwana shirin auren sa baya gabana, a gefe ɗaya ina ta shirin tariyata da zan yi bayan auren Yallaɓai amma na ce sai ya gama cin amarcinsa sannan zan koma, ba zan iya juran ganin shi yana rawan ƙafa kan wata mace ce. Ita Gimbiya da ba ta gane ba ta kai kanta. Hausawa suka ce ai ƙazantar da baka gani ba sunanta tsabta amma ita kazantar ta je gani Allah kuma ya ba ta sa'a ina nan ina zaman zamana na san za ta yi nadaman abin da ta yi.

*****

Biki ya ƙarato tun da mun shiga sabuwar shekaran 2023. Jidda na shirin komawa makaranta amma za ta je ta biya kuɗin makaranta da na hostel,  sai ta dawo tun da karatu bai kamkama ba sai bayan bikin babanta za ta koma, amma ko a yanzu ba zaman banza take yi ba kullum cikin cin kayan fulawa muke yi a gidan nan Cake kam har kyauta nake yi da shi. Donut kuma sai ya yi sati tun da shi ba ya lalacewa da wuri.

Jidda ta gayyato kawarta Ummu Salma Hamza. Baby ce uwar gayya har da yan haddar su, su ba ruwansu murna kawai suke yi, a na saura sati biyu da wani abu biki Yallaɓai ya ce Rabi'atu a ranar ta koma Maiduguri na ce lalle za ta sha tafiya. Sai ya ke ce mini ai jirgi ta bi amma daga nan gida sati na sama za su tafi da  sauran kayan a mota. Ban ma tambaye shi ba shi da kan shi yake faɗa mini suma a jirgi za su je ɗaurin aure. A raina na ce ai kana da shi ko birnin sin ne za ka biya domin ku je, yana yi mini list ɗin da waɗanda za a je ɗaurin aure Alhajinmu na sahun gaba shi da Tafidan Rano. Sai shi da aminan shi, sai Ya Usman da a can za su haɗu sai Musbahu.

"Kuma duk kai za ka biya kuÉ—in jirgin?

Yana dariya ya ce" Kawun ki  ya ce zai ɗau nauyi"
Na jinjina kai zai iya tun da shima ya ta da kai. Har anko ya siya ma Marwa kuma da kan shi ya zo ya karɓan mata da ya shigo garin. Tariq ne da man bai kamo su ba amma shima yana da rufin asirin shi.
Yallaɓai bai faɗa mini ya yi kashe kashe kuɗi ba amma ni na san ya yi auran yar maiduguri ba wasa ba, ya faɗa mini an yi masa maganar kuɗin gyaran jiki na ce ai su can kamar al'ada ne.
Amma shi fa bai damu ba murna kawai yake yi ba ya damuwa da kashe kuÉ—in. Ni ce ma na gaji na tambaye shi gidan da Gimbiya ta tashi ya zai yi da shi? Ya ce mini bai yi tunani ba yanzu an rufe shi in ya yi shawara zuwa gaba zai san yadda zai yi da shi. Wallahi har raina nake son gidana ba na son tashi, amma tunda cigaba ne ya samu ba ni da mafita amma ina son gidan nan kuma ina da tarihi mai É—imbin yawa a cikin shi.

Yallaɓai ya tsara tun da ban riga na tare ba a gidana za a yi taron biki ba Gwamnaja ko sabon gida ba. Ni da man ban ce kowa ya zo ba iya ni da yan uwana da wanda ya ga zai zo. Gimbiya da man ta ce ita ba biki za ta yi ba gidan matar de za ta zo, saboda haka mukkarabanta can za su sameta a sabon gida. Ni kuma ina gidana da jama'ata.
Tun satin biki Yallaɓai ya fara ƙyallin amarci ni kuma sunan shi ya tashi daga Yallaɓai ya koma Ango da ko na ce Ango zai washe baki yana jin daɗi..komai na buƙata ba abin da Yallaɓai bai kawo ba. Ya ba ni kudin kunshi da gyaran kai ni da yara kuma mun yi, mai kunshi ta zo har gida ta yi mana na yi gayya domin kaf yan gidanmu ban ce na ɗauke ma kowa daga su har yaran su.

Ana jibi biki Amina ta diro daga Kaduna. Faridan Tariq tazo aamma ita sai ana gobe biki. A kuma ranar su Yallaɓai suka daga maiduguri tun da in an ɗaura aure kuma za su juyo da amarya amma akwai sauran kayan da wasu za a kawo su ta mota. Jere kuma a ranar jumma'an da man daga nan Kano dangin su suka zo suka yi, ni ce na yi musu abincin tarba domin Gimbiya ta ce ba za ta yi ba Yallaɓai ya kirani ya ce na dafa na aika akai musu. To ba ma ni na dafa ba su Mubeena ne su kuma suka kai musu abincin can gidan shinkafa da miya da pepe chicken, sai kunin aya da zoɓo. Suka dawo suna faɗa mana irin dukiyar da aka sanya ma Amarya a shashenta da tsaruwan sabon gida.

Da man Mubeena da Marwa ne suka je kai musu. Suka ce Gimbiya na bangarenta ana ta shewa ta shirya rashin mutumci na ce ya ƙare mata can ni ba ruwana da ita. Wannan abin da na yi haka Yallaɓai ya kirani yana ta yi mini godiya sai da na ji wani abu ya motsa a cikin tsokar ƙirjina. Me na yi masa? Komai shi ya kawo kawai nawa na ba da umarni an dafa kuma na aika da shi.
Washegari 30 Jan ranar asabar ƙarfe sha daya na safe aka ɗaura auran Yallabai da Rabi'atu kuma sha sha ɗaya da mintina ni ya fara kira ya sanar mawa.

"Alhamdulillah. Ma sha Allah Allah ya ba mu zaman lafiya ya kaÉ—e dukkan fitina."

"Amin na gode Sadiyata. Na gode ƙwarai da girmamawan ki."
Chapter 77 · 0% Book details