Sashe 80
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na faÉ—a ta amsa da Amin sannan muka katse wayar.
Su Jidda sai wajejen goman dare Adanan ya dawo da su ina ta ma kiran wayarta ba ta É—auka ba suna shigowa na fara masifa sun barni ni kaÉ—ai a gida ta je sun yi zaman su.
"Ki yi hakuri Umma. Ba mu samu me dawo da mu ba ne. Uncle Musbabu ne kuma Anty Mubeena ba lafiya ya tafi gida. Sai Uncle Adnan ne shima bai daÉ—e da dawowa ba."
"Ba sai ki fito ki jagoranci ƙannen ki ku samu adaidaitasahu ku dawo gida ba? Sannan ina kika saka wayarki ina ta kira ba ki ɗauka ba?
"Ban ji kiran ba Umma tana jaka "
Hararanta na yi ta wuce tana dariya. Adnan da man bai shigo ba yana ajiye su ya juya. Baby ce ta fara mini surutu wai Amaryan Abba an kawo ta Gwammaja, kaf labarin abin da ya faru sai da ta ba ni Yumna saboda Gajiya a can ta fara barci ko da suka shigo tana saɓe a kafaɗan Jidda. Sai na ce ta shigar mini da ita ciki.
Sai da duk ta gama surutunta sannan ta ce mini wai yunwa take ji.
"To ni ce zan ta shi na dafa miki abin da za ki ci kenan uwata Maimuna?
Na faɗa ina hararanta sai ta miƙe tana dariya ta wuce na rakata da tsaki. Kayan da man su Munnira suka kama mini na kai shi ɗayan bedroom ɗin da niyyar sai Yallabai ya gani sannan zan yi kasafin shi. Na ɗauka zai shigo yi mini sallama ne amma tun da na ga sha ɗaya ta yi na cire rai. Ni kaɗai a falo su Jidda sun gama duduman su sun shige ciki.
Nima dole na tashi na kashe komai na shiga ciki. Tiolet na shiga na kama ruwa ina fitowa na ga wayata na haske kafin na ƙarisa wayar ta katse.
Yallabai ne, ina shirin bin bayan kiran shi sai ga saƙon shi ya shigo.
"Ku kwanta sai da Safe Sadiya ta. Tariq ya rako ni yanzu haka ma muna ƙofar gidan."
Sai na ji jim ina sake bin saƙon sa da kallo, to mi ye na sai ya wani faɗa mini za a raka shi ɗakin Amarya. Duk da na so kar na ji zuciyata ta motsa sai da kishi ya taso mini. Shi ya hana ni mayar masa da amsa, ganin kamar zuciyata ta ɓaçi sai na juya na koma tiolet na ɗauro alwala na zo na yi shafa'i da wuturi na yi addu''o'ina da Allah ya cire mini damuwa a wannan daran ya sanyaya mini zuciya.
Na yi ta maimaita LA'ILAHAILLAH ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN.
Sau arba'in har sai da na ji zuciyata ta yi sanyi.
Ina idarwa na yi shirin barci Yumna da man tuni ta kai england. Gefenta na kwanta bayan na yi mana addu'an barci na shafe mu gabaɗaya wutar ɗakin na rage sannan na kunna suratul Maryam a wayana na ɗan rage ƙara na saka shi gefena na rumgume y'ata muka shige bargo.
Da farko sheɗan ya fara hasko mini abubuwan da ba su kamata ba na yi ta ta'awizi a cikin zuciyata cikin ikon Allah sai barci ya fara fizgata ban daɗe ba barci ya sace ni, ba ni na farka ba sai asuba na kuma ta shi wasai kamar ba ni ba. Na ɗauka zan ga Yallaɓai a ranar shima haka aka yi har dare ba shi ba wayarsa da Amina ta zo yi mini sallama ma nuna mata kayan sannan na diɓa mata kayan fulawan da kayan kwalliya na ce ta kai ma su Afra sai filet da kula guda ɗaya. Tun da gogan yana can yana cin amarci bai samu fitowa ba, aka sake kwana ba Yallaɓai ba wayarsa ni kuma ban neme sa ba na riƙe mutumcina amma in na ce zuciyata ba ta motsa ba wallahi na yi ƙarya daurewa kawai na ke yi. Amma ni kaina na san Yallaɓai ya samu chajiin Lambu ba zai yi wasa da ban ruwa ba.
 Da na ga ba shi da niyyar zuwa ranar laraba da yamma Rahila da Ma'u da ke da tsohon ciki suka sake leƙoni da man ina da niyar kiran Hauwa ko Munnira ne su taya ni na raba kayan sai ga su Rahila. Su suka taya ni muka zauna na kasa shi, har Gwaggo sai da na dibar ma turaren wuta da kayan fulawa haka su Ya Aina. Hauwa da Munnira ma daidai da nawa na ɗibar mana saboda a sha'anina ko ya'nuwana albarka yadda suke tsaya mini. Kayan kwalliyan kuma suka ce na bar ma yara tunda ƴaran mata gare ni, Alhajinmu ma zaɓa masa yar kula mai kyau na ce zan kai masa Atamfar kuma suka ce na ɗinka tunda ni suka ba mawa. Su suka tafi da y'an gidanmu har na Gwaggo da Alhajinmu tun da Dorayi suka ce za su fara sauka kafin su wuce gidajen su, jin haka yasa na diɓi kayan fulawan da turare na ce Ma'u ta kai ma Baaba, duk da ta daɗe a can Yashe sai a satin nan ta dawo Kano.
Sun fita ba daɗewa aka kira mangariba ina cikin yin salla na ji ana ta kiran wayata sai da na idar na duba na ga Yallaɓai ne sai bayan kwana biyu ya tuna damu. Jidda ma sai jiran shi take yi tana so ta komawa makaranta ranar lahadi. Ta ce mini ta kira shi bai ɗauka ba, na ce kar ta sake kiran shi ai ya san da komawar na ta.
Sau biyu yana kirana ina salla sai da na idar ya sake kira wayar na hannuna na ƙi ɗauka haka kurum na ji ina jin haushin shi. Har kwana biyu muna gari ɗaya amma Yallaɓai bai neme ni ba! Gwara Gimbiya suna gida ɗaya na tabbata ba zai kwana su tashi ba ta gan shi ba.
Sai da ya kara kira na huÉ—u sannan na É—aga tana ma gabda katsewa.
"Umma Sadiya."
Ya faɗa yana ɗariya. Sai na ji zuciyata ta ƙuntata, wai Umma Sadiya sai yau na ji kamar da gayya ya faɗi sunan e mana na zama Umma shi ko yanzu ai sabuwa gare shi.
"Uhm Ango."
Na faɗa ina ƙoƙarin daidaita yanayina.
"Uwargidata."
Yallaɓai ya iya bariki da ban sani ba sai da ya auri Gimbiya na san ko lauya ya karanta sai haka in dai wajem lauya zence ne.
"Ina yini? Ya amarci?
Na faɗa ina ƙoƙarin sakin fuska kamar yana gabana.
"Lafiya lau. Ya yarana ya gidan? Sai kuma kika manta da ni Abar ƙaunata?
Kamar na yi masa ashar sai kuma na fasa.
Cije baki na yi kafin na ce" Ah na bar ka ne ka ci amarcinka. Ina Amarya?
"Ga ta nan tana jin ki."
Ya faÉ—a yana yar dariya.
"Ayya ka gaisheta. Ina fatan ba ta yi baƙunta ba?
"Ta yi fa, ta na ma kan yi, ga ta nan ma kwance sai rakin tsiya."
Kasa magana na yi saboda na ma rasa me zan ce. Hakan bai sa Yallabai ya yi shuru ba ina jin sa yana dariya yana mata magana a ƙasa ƙasa wai ga ni ina son magana da ita ni yaushe muka yi haka da shi? Ina hamgame da baki ban rufe ba na ji muryanta tana yi mini Sallama.
"Umma ina yini"
Shike nan daga Anty na koma Umma, Yallaɓai ya gama da ni.
Sai na danne na saki fuska kamar tana ganina na amsa mata gaisuwar ina tambayanta baƙunta ta yi mirmishi.
"Ki saki jikin ki kin ji ko? Ai gidan ki ne"
"Yaushe su Jidda za su zo mini?
Ina riƙe baki na ce" Ba yanzu ba. Sau nan gaba Jidda ma ranar lahadi za ta koma makaranta in sha Allahu."
Sai ta ce Allah ya nuna mana, sai ya karɓi wayar yana ce mini gwara dai na yi mata faɗa taki sakin jiki.
"Ka yi haƙuri za ta saki na ɗan lokaci ne. Kuma ka san haka ke faruwa da kowacce amarya."
"Wallahi na tuna kema haka kika yi ta mini. Da na matso kusa dake ki fara mini kuka kina faɗin don Allah kar ka taɓa ni ba na so."
Ya ƙarishe faɗa yana kwaikwayin muryata wai, baƙinciki da takaici suka yi mini rufdugu kamar Yallaɓai ya ruɗe, ni na ma kasa mgana ina shirin ma na kashe wayata ne na ji yana faɗin" To itama haka take yi mini, in na kalleta ke kawai na ke tunawa a wancan zamanin Sadiya ta."
"Uhm"
To me zan ce? Ko na ce wani abu ba zai gane ba giyar amarci ne ke É—iban sa.
"Maganar komawar Jidda makaranta ranar lahadi ne."
Na faɗa da ƙoƙarin na kaudar da maganarsa.
"E wallahi na sha'afa sai da na ga kiranta jiya. Zan tura mata kudi ta yi siyayya kafin na shigo gidan.'
Wato ba ma yanzu ba? Duniya sabuwa a wajen Yallaɓai.
Ban ce masa yaushe zai zo ba? Na ce Allah ya kaimu. Yumna ya tambaya na ce masa tana falo na É—auka ya kirani ne mu gaisa amma sai na ji yana faÉ—a mini kwana daya daga gidan Mimisco aka kawo musu abinci jiya ko da yau ma duk takeway ya yi musu.
"Gaskiya. Ga Gimbiya a kusa ai ita ya kamata ta baku abinci har sai Rabi'atu ta yi bakwai."
Sai ya yi shuru maimakon ya amsa maganata sai kawai ya ce" Ina neman alfarman daga gobe ki dan riƙa dafawa damu, sabon direba zai riƙa zuwa yana ɗauka."
Na buÉ—e baki kamar yana ganina kafin na ce" Har sai an zo nan? Miye amfanin matarka dake gidan?
"Ai na san da ita na kira ki Sadiya."
"To me ya sa sai ni? Kana da tabbacin zan amsa alfarman taka ne?
Sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Nima ban san me ya sa a komai nawa in ya taso ke nake son kira ba. In wata bujata ce wajen ki nake son fara zuwa. Ina da yaƙinin ko ba ki yi mini abin da na ke so ba in na faɗa miki kina bani mafita."
Kalamansa suka kashe mini jiki da na kasa mgana.