Sashe 100
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yallaɓai har gobe bai dai na faɗin bai cire rai ba bai kuma haƙura ba yana fatan bayan Yumna na sake haihuwa ni kuma na kan ce masa na gama. Ga su Gimbiya nan dai su yi ta cika mana gida da yara Alhmdulillah. A tsawon zamana da Yallaɓai ya yi mini tarin alhern da suka goge sharrinsa a wajena amma babban abin da ya yi mini da ya ƙara samun daraja a cikin zuciyata shine ya biya mini kujeran makka a wannan shekaran na je na sauke farali sannan ina dawowa na yi cukun_cukun buɗe shagon Saloon ɗin da na ke buri, domin na fahimci Yallaɓai ba zai iya cika mini alƙawari ba, Musbahu na saka a jagoranci sai dai Yallaɓai ya ji labarin an kama shago a wajen ƙaninsa domin ni ban faɗa masa ba, sai ga shi ya zo yana borin kunya shi da man yana da niyyar da na dawowa daga Saudiya ya buɗe mini shago shi ne target ɗin shi, har yana faɗan me ya sa na yi masa haka? Ni ko na ce kar ya damu ba komai ai na san abubuwa ne suka yi masa yawa, ba na ce ban gode masa ba ne na gode tun da ya yi sanadin da na je ɗakin Allah, amma mganar buɗe shago bana son tunawa saboda tsabar renin wayau da renin hankali Yallaɓai ya yi mini shi, tun yaushe? Mgana ce tun auran mu, yana da shi ba wai ba shi da shi ba ne, kawai bai yi ra'ayin cika alƙawari ba ne shi ya sa na kuɗiri niyyar sai dai ya ga ana yi, da jarin hijabaina da kudaɗen hannuna na haɗa na kama shago na yi siyayyan wasu kayan shi kuma Gogan sai ya ji kunya ya dunkule 800k ya bani da na ce ma ba zan karɓa ba wajen Alhajinmu ya kai ni kara shi ya tursasani na karɓa sannan a ɓoye ya saka aka yo mini oder ɗin kujeru da sauran kayan injinan shagon sai dai na ga an kawo sannan ya shiga ya fita sai da aka gyara shagon nan ya ga komai ya kamallah, har yana yi mini mganar ko zai kama mini wani babba ne! Ya ga kamar wannan ya yi ƙarami na ce na gode ƙaramin ma ya ishe ni.
Gabaɗaya dai kunya ta hana shi suƙuni ni kuma ko a fuska ban nuna masa ba, shi ne dai ya san bai kyauta ba yana ta kame kame na yi banza da shi. To ni Yallaɓai ai ya daina damuna, na tattarashi da sha'aninsa na watsar tun a baya.
Da shago na ya kamallah mai suna S.S YASHE BEAUTY SALOON.
Na yi Farinciki da ban san iyaka ba da man ina cikin farimcikin ne na je na ga ɗakin Allah A shekaran tare muka je da Alhajinmu Hajji da Ya Hamza da Ya Auwal suka haɗa kudi suka kai shi sai Ya Usman da Anty Zabba Allah ya taimaka a masauƙi ɗaya muka sauka. Yallabai ya girmama ni tun da ya ce ni ce uwargidan shi ni zan fara zuwa amma daga baya ɗaya bayan ɗaya zai kai su Gimbiya. Suma ɗin ba su nuna damuwar su ba sun yi fatan Allah ya sa suna da rabon zuwa ita Gimbiya ma ta taɓa zuwa Umra tsohon mijinta ya taɓa kai ta, Yallaɓai ma a shekarslan da ya biya mini ya je Umra ya dawo.
Kamfanin Yallaɓai ya shahara fiye da tunanin mai tunani yanzu haka yana ma shirye-shiryen buɗe reshe ne a jihar Kaduna. Yanzu in dai kamfani ne na gine-gine da zane-zane in sunan kamfanin Yallabai bai shiga gaba to zai jera a na biyu. Dukiya kam ya nema da aiki tuƙuri kuma ya sa mu, yanzu haka dukkan mu ya siya mana sabbin motoci, ni da Gimbiya da Rabi'atu ni tawa Ta kamfanin toyota ne, tawa kuma ta fi tasu tsada ni fara ya siya mini.
Na su kuma na kamfanin camry ne, duka kalan ruwan toka.
Sannan can Gwammaja an sake gyara gidan an ƙawata shi ya siya ma Nene mota har da direban da zai riƙa zirga-zirga da su ya ɗaukan musu. Ba abin da suka nema suka rasa sai godiya.
Munnira Nasir ya samu aiki a Taraba ya koma can daga baya ya zo ya ɗauke mana Munnira suka koma can sai dai mu yi magana ta waya. Daga ni sai Hauwa da itama Alhamdulillah Mutaƙƙa ya samu buɗi da rufin asiri. Duk sun sake haihuwa har Marwa yanzu yayanta uku ta zama uwar mata. Datti ma matarsa ta haihu gidan mu na ɗorayi shashen farko su Ya Hamza sun rushe shi sun gina shashe mai kyau in da suke sauka da iyalansu in sun zo. Cikin gida ma komai ya sauya Gwaggo ta na nan kwance ta samu ciwon ɓarayin jiki Baaba ce ke kula da ita amma Alhajinmu har gobe yana nan da ƙarfinsa.
Ma'u ta sake haihuwa amma ta samu matsala har sai da aka cire mata mahaifa ta fi wata a asibiti tana jinya daga baya ta ji sauƙi ta koma gida. A yashe mun yi rashi shima Baba Aminu mun rasa shi mahaifin Ya Muntari rayuwa sai godiya. Bayan rasuwar Baba Aminu ko wata shidda ba a yi ba mahaifiyarsa ta saka shi ya auro ɗiyar kanwarsa tana nan gida ɗaya da Rahila. Auran da ya sha mganganu ita kanta Rahilan har cewa ta yi sai Muntari ya zaɓa ko ita ko amaryan da zai aura. Da nasihan Alhajinmu da shawarwarin irin mu Rahila ta haƙura domin na sha faɗa mata ta yi haƙuri wata rana za ta ci riba. Su Ya Aina kowa sai hamdala rayuwa ta yi kyau ana lallaɓawa. Amina ma ta sake haihuwa ƴaƴanta biyar kenan tana zaune cikin farinciki da mijinta. Ya Abubakar ma ya ƙara aure tun da shima ya kama babban aiki yanzu ba gida ɗaya suke da Amaryan ba tuni Zaituna ta shiga taitayinta ta gyara bayan lokaci ya kure mata.
A yanzu haka Jidda na Aji huɗu ne za ta je biyar a jami'a. Kuma tana da shekaru ashirin da huɗu ne, an sanya mata ranar aure shekara mai zuwa ita da Uncle ɗin kawarta Ummu Salma auta ne a ɗakin mamanta. Sun yi bikin yayar Ummu salman Jidda ta je musu biki anan ya ganta. Abdullahi pilot ne matukin jirgin sama ne. Kuma ba jira ya nemi soyayyar Jidda ta amince ganin duk abin na gida ne an zama ɗaya tun da har bikin na je ni da Baby sai ya gabatar da kansa a wajen Yallaɓai.
Sai ga shi Yallaɓai na zuwa da wata magana wai ba yanzu zai aurar da y'arsa ba sai ta gama makaranta. Ƙiri-ƙiri fa yana abu kamar wani ɗan fari ni ko ganin zai yi mana salalan tsiya ga Jidda na son abin ta na kai shi ƙara wajen Ya Usman kai tsaye ya ce na ba ma yaron lambarsa ya neme sa. Ai sai dai Yallabai ya ji labari daga baya Uban Jidda Alhaji Usman ya ba ma Abdullahi dama ya cigaba da neman Jidda. Ba shi da bakin mgana balle da Tariq da Kawu suka ji labari kamar su tsire shi, suka ce ya yi musu katsalanda ina ruwan shi ai sune ma su ba da auran yar su. Hakan ne ya sa ya koma gefe ko maganar auren da saka ranar Ya Usman ne da su Kawu anan Kano ya zo aka karɓi maganar a Gwamnaja aka saka rana wattani goma ma su zuwa. Baby da ta ke aji ɗaya a BABA AHMAD UNIVERSITY KANO tana da manemin ta. Shi kuma yaron ƙanwar mijin Mimisco ne likita ne an asibitin Aminu Kano. Shima Yallaɓai ya fara faɗa wai Babyn nawa ta ke? Ba ta isa fara samari ba shima sai da na yi masa ido da ido sannan ya bari Hafiz na zuwa duk Weekend suna ganawa da Baby tun da na gida ne amma fa ya sha sharuɗɗa kamar zai auri wata gold Yallaɓai fa ya ƙaro wulakanci wai shi nan haushi ya ke ji duk za a tattare mai ya'ya lokaci ɗaya. Ina dariya na ce wanzami ba ya son jarfa shi amma ya tattare ya'yan mutane a gidan shi?
Sai an yi mgana ya ce Æ´aÆ´an shi ba su isa aure ba sai sun gama karatu. Su Musbahu suna nan an zama magidanta Mubeena ya'yanta biyu. Ga Adnan ma yan baya baya matarsa ta haihu shima.