← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 103

Sashe 37

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yumna ma an sauya mata kaya ta yi kyau daman ta sha kunshi a hannu da kafa da Ya Murja ta sake kun sa mata yau da safe yau ma mun so komawa asibiti amma sai Yallaɓai ya ce mu bari gobe da safe kar mu je a yi mata allura ta dawo da rigima amma dai tun kwana uku da haihuwanta wanzami ya zo ya cire mata belu sannan ya yi mata askin gashin kanta kamar yadda ya zo a cikin sunna. Zuwa biyu da rabi shagalin suna ya kamkama, baki suna ta zuwa ban yi tunanin zan tara mutane haka ba ni da ban damu da zuwa suna ba, duk sun saka ankon su sai suka yi kyau sosai. Maijidda Bala daman ta zo garin lokacin da na haihu da ya ke mijinta ya samu aiki a Dutse sun koma can da zama ita ce ta yo mini gayyar su Samira da Hauwa jamilu sai da na yi ƙwalla da suka kawo min pampers da mayukan jiki da hoda na jarirai sai safa da huluna suka ce kuɗin da a ka haɗa mini ne suka siya mini da shi, duk da ina ba da wa in na gani amma ba kowanne na ke yi ba, amma dai tabbas na ji daɗi na kuma martaba wannan karan da suka yi mini, sun kuma saka ankon su gwanin ban sha'awa.
Muna cikin bedroom ɗina tare da su muna hiran yaushe gamo. A nan Rahila ta kawo musu abinci sinasir da waina sai alale da ruwa da drinks can cikin gida kuma su Munnira na ta ji da baƙi.

Suwaiba da Jamila sun zo mini suna da wuri amma ko Gimbiya sai wajen uku na rana ta zo tare da Halima da Naja. Mimisco daman ta ce mini tana Abuja amma yaranta ƙananun suna nan, Anty Maimuna ba ta zo ba sai can wajen la'asar suka zo ita da Anty Bahijja. Su Nasara da suke kusa duk sun zo mini suna kuma an ba su abinci kamar na kowa ba nuna bambamci ko da suka zo na sauya kaya na saka anko da suka shigo suka ganni sai da mamakinsu ya nuna tun ballantana da suka ga gefen gado na cike da kayan arziƙin da a ke kawo mini. Gimbiya ta ta ba ni saƙo a leda Anty Bahijja ma ta ba ni leda Babba cike ta ce na su ne gabaɗaya daman haka suke yi bai ɗaya suke mini hidima in har na haihu. Naja ce kawai ta ɗauki Yunma amma bayan ita haka suka fita ba su ɗauke ta ba sun fita fuska ba daɗi domin ba haka suka so su ganni ba. Ga shi sun tarar da ɗaki cike da mutane su da ba su yi anko ba sai suka ga su ne ma dabam a wajen domin kowa ya yi ban da su.

Ba abin da zan ce ma mutane sai godiya domin sun yi mini karam kaya sai da na koma jefa su a ƙasa saboda gadon nawa ya cika kowa ba ya zuwa hannu rabbana in ba a bani saƙo a leda ba za a ba ni kuɗi hatta Ya Abubakar da Ya Muntari sun tura mini kuɗi sannan matan su ma sun zo sun kawo mini turame, sai da a ka yi sallar la'asar sannan mai hoto ya zo a haraban gidan shi da yaran shi suka yi decration na ɗaukan hoton. Mamaki kawai na ke ba ma su Anty Bahijja sun kasa magana na fito da tawagata mun sha hotuna zafafa na shiga na fita da kaya sama da kala biyar ni da Yumna, na kuma gayyaci su Anty Bahijja zuwa hoton sun shiga amma a cunkushe Gimbiya ma mun yi ni da ita sannan mun yi da yara. Muna cikin hoton ne sai ga ƴa'ƴan su Anty Bahijja da na Anty Maimuna waɗanda ke gida wasu sun yi aure wasu kuma suna makaranta. Ana gamawa da hoto suka saka kiɗa a speaker suka yi connecting da waya daman Munnira na da home thearter ita ta zo da su daga gida saboda ta ce chasu za su yi ni dai na sulale na koma cikin gida na kira Musbahu na tambaye shi Yallabai ya ce yana office tare da Kawu sai na ce ya zo gida ya karban musu abinci ba daɗewa sai ga shi ya zo na saka Mubeena ta je ta kai mishi har da na shi gabaɗaya.

Sun ta saka kiɗa su suna ruwa ni dai ban shiga ba, ina da ɗinki a ƙasana duk da ya kusa warkewa amma gwara na kiyaye amma da Munnira da Hauwa da Amina suna rawa na shiga na yi musu manni, Yumna ta na hannun Sameena itama ta shiga tana juyawa, har su Suwaiba duk sun shige daman su ai ba ruwan su ana cikin shagali ana ta farinciki suma Gimbiya da tawagarta suna wajen Anty Maimuna dai da Anty Bahijja sun yi mini sallama za su tafi na saka Munnira ta salleme su da ledan su ta ce mini sai da Anty Bahijja ta taɓe baki kafin ta ce"Lalle Tafida ya riƙe ma Sadiya kan macijin har da wani leda ne in mutum zai tafi? Duk abincin da aka ci bai isa ba? Ni dai a yadda ta faɗa mini ta ce ba ta tanka ba amma ni na san ƙarya take yi sai ta ba ta amsa. Sun tafi sun bar su Gimbiya da yaran su ina ga sai daga baya suma za su tafi.

Ana cikin shan wakar ado gwanja na kujeran tsarkar gida, Munnira ta sauya zuwa kirarin uwargida. Kirari ne da wani mawaƙi ya yi ga uwargida je, kuma tabbas kirarin ya yi sosai ni dai ina ta dariya da farinciki su ka ja ni cikin fili suna kuma bin kirarim suna nuna ni.

"Uwar gida ran gida in babu ke gida ya ɓaci. Haka zalika kowa ya zo ke ya tarar. Ke ce Amarya kuma ke ce uwargida, ke kika fara kafa gida saboda haka kowa ya zo ke ya tarar. Ke ɗin dai ce Uwargida haka za su gan ki kuma haka za su bar ki, hassadansu sai dai ta koma kansu. Allah Ya barki da Alhaji Tafida ya kuma kashe ki a ɗakin Tafida.
Takalmin kaza mutu ka raba."

Ina ta dariya saboda duk in da a ka ce Megida sai su sauya suna su kira sunan Yallaɓai. Jin daɗin kirarin ya saka na fiddo kuɗi a jaka ta sabbin yan ɗari bibbiyu da Khaleesat ta ba ni na riƙa manna musu. Daga baya ma Jamila kashe speaker ɗin ta yi ta ɗaga muryanta ta na rausayawa a gabana ta fara faɗin.

"Yau taken naki ne Uwargida a gidan Tafida. Uwar gida ran gida shalele a wajen Tafida. Kowa ya zo ke za ya tarar. A buga a bar ki sai ta Allah ta yi Uwargida sai gaban ki in da kike so. Wallahi ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya. Mun sani mun kuma tabbata da tsohuwar zuma ake mgani. In ka ji ana a wasa a wasa ba kaifi, ke ce wakiliyar Tafida kowa ya zo arziƙin ki ya ke ci, kin zama Tafida Tafida ya zama ke, maganarki a ke yi wa ke batun yan karere. A matsa a matsa ga Uwargida Sadiya a gidan Tafida ta hallara na ce a matsa a matsa."

Kaina na ji ya fashe,na ji na yi girim girim nan da nan na zazzage musu kuɗaɗen dake jakata sai shewa da ihu ya ta shi Amina da Munnira suka ɗora da guɗa. Har da Sameena a wajen ni ban ma lura da Gimbiya ba, ballantana na ji cewa ina yi da gayya ne sai bayan mun baro haraba zuwa cikin gida Hauwa ke tsegunta min ga Sameena can naja na yi mata faɗa wai ba ta kishin ƴar'uwanta ta biye mana a na yi ma yaruwanta habaici. Na riƙe haba cikin mamaki ina faɗin habaici kuma? Hauwa ta ce wallahi su haka suka ɗauka sai kawai na ce to Allah ya kyauta ni dai fata na mu rabu da kowa lafiya.

Ai ko na gan su da Sameena a can haraba bayan mangariba lokacin da na fito zan raka su Samira. Su ko salla ma ba su yi ba suna nan suna mganganu har da Halima a wajen, suna ganina suka yi shuru Sameena ko daga gani ranta ya gama ɓaci domin juyawa ta yi ta shige ciki a fusace kamar za ta tashi sama ni dai ban ce komai ba iyaka dai na ce musu ya kuka tsaya a nan? Sai Halima ta ce minI wai tafiya za su yi sai na ce su je su karbi saƙo a wajen Munnira sai ta amsa mini da to.

Ni na dawo cikin gida ban san me ya faru ba Sameena ɗayan ɗakin ta shige nima ban neme ta ba kawai muna cikin ɗaki ni da su Ya Aina suna ta ƙwashe min kayan da na samu nawa da na Yumna sai ga Khaleesat ta shigo tana faɗin wai ga Amina can suna hayaniya da ƙanwar mijina mamaki ya kamani ina tambayan kaina me ya haɗa su? Gabaɗayan mu muka fita can falon Yallaɓai muka iske Amina da Halima suna cacan baki ga su Gimbiya zaune Munnira ce me ke jan Amina da cewa ta yi shuru amma Halima da rashin kunya ina falon ta ce ma Amina.

"An zo an samu banza an tattare, za a kai gida. Saboda babu a house É—in tsoho sannan a house É—in miji ma babu."

"Ke Amina me ke faruwa! Me ya haÉ—a ki da ita?
Chapter 37 · 0% Book details