← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 103

Sashe 79

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba wani cika baki. Ba ke kika hana shi ya ƙara ba."

In ji Yallabai.

"Kuma wallahi tsoron ta yake ji."

In ji Kawu nan suka haɗe mata kai suna ta caccankanta da cewa kamar fitilar besfa Tariq dai ya ƙi kara aure sai ita kaɗai haba ai gwara dai ya ƙara ko ɗaya ne. Shi dai Tariq na gefe yana dariya.

"To ku ba shi matar ya ƙara mana? Wallahi ko a jikina tun da ba kaina za ta zauna ba amma gaskiyan mgana ba zan iya abin da Sadiya ta yi ba wallahi."

"Ka ji ba "

Kawu ya faÉ—a yana dariya kafin ya cigaba da faÉ—in" Za ko mu ba shi mata mu ga karyan cika baki. Kai ka zo Rano na duba maka cikin dangi."

"An gama Kawun mu."

Tariq ya faÉ—a yana dariya.

"Amma tare da shi za ku ƙara ko?

Yallabai ya tare shi.

"Me?

"Auran mana."

"Ah ni kam ai na tsufa, na fara furfurta matata Marwatu ta ishe ni."

"Kai ma tsoron matar taka kake yi kenan?

Farida ta faÉ—a, sai ya sosa keya kafin ya ce" Ki fahimta mana "
Tariq ya shuri kafar Kawu yana faɗin"Ka iya addabata da maganar aure kai ma fa? Me ya hana ka ƙarawan?
Ga tafida har ya yi ta uku?

"Na ce muku matata ta isheni kar ku tsananta bincike"

"Sai mun tsananta."

In Tariq.

"Ko ba ka da lafiya ne?

Yallaɓai ya kwaɓo magana ni da Farida muka tafa muna sunne kai.

"Ba shi da lafiya ya haifi su Abdallah munafuki lafiyan sa ƙalau"

Tariq ya faÉ—a yana dariya da Kawu ya ga sun dame shi kawai sai ya kalle su kafin ya ce" Ba ni da karfin mazukutan da zan tara mata shike nan kuke son ji?
Sai suka yi shuru suna kallon shi, ni da Farida saboda kunya sai muka kama hanyar barin falon saboda kunya.

"Matata ma haƙuri take yi da ni. Ta ina zan jajiɓo wata?

Kawu ya faÉ—a a maganarsa ba alamun wasa.

"Wallahi ƙarya kake yi munafuki."

Tariq da Yallabai suka haÉ—a baki wajen faÉ—a ni da Farida muka bar falon muna dariya in dai su ne in suka fara to sai kowa ya yi shuru ya bar su.
Marwa na ce ma ta je mijinta na kira ta ce to da man ta tsaya yi ma su Abdallah wanka ne.
Jidda na tura da kayan kari falon iyayenta sai ma ta dawo da shi ta ce sun ce a sun yi beakfast daga hotel ɗin da suka kwana, sun jima a gidan sama da awa sannan suka fita. Tariq da Kawu duk a ranar za su koma. Sun ce ma matan su su shirya kafin su dawo. Marwa ke son zuwa gida sai na ce ta yi sauri ta je ta dawo kafin su dawo. Amma ba ta tafi ba sai da suka ta ya ni muka gyara gidan sannan muka yi abincin rana Allah ya sa ba mu dafa da yawa ba tun da sai da na kira Yallaɓai a waya na yi masa maganar bangaren Amarya da danginta ya ce kar na damu Mimisco ta kira shi ta ce za ta yi direba zai kai sai na ce shike nan ta hutattashe ni.

Farida na ta mamaki wai kuma sai na dafa na kai! Na ce me ye a ciki? Ita kam ta ce ba za ta iya ba.
"Ba zan ta yar da hankalina balle na zama abin tattaunawa a dangi ba amma wallahi ba zan yi ba."
Ina ta dariya ita ko tana shan wallahi. Shi ne har muka gangaro maganar Gimbiya ina ba ta labarin duk abubuwan da suka faru kafin auran nan.

"Ba irin shawaran da ban ba ma Gimbiya ba ta ƙi jin maganata. Ni yanzu haka makiyayarta ce. Su Anty Bahijja ne masoyanta su ta rike suna zugata tana yi ma mijinta rashin kunya. Jiya fa a gaban dangin Rabi'a ta kunyata ni da Mimisco abin ba daɗi wallahi."

"Ai ga shi nan ta bar ma kanta abun faɗa. Sai yi da ita ake da cewa mijinta zai ƙara aure tana ta hauka. Gaskiya abin da ta yi ba aji ba ne, ni kaina ba ta wani yi da ni tun ma kafin auranta da Tafida. Bayan auran su kuma ganin muna tare ba ta shigo ni ba."

Ina dariya na ce" Ko yau kika je Allah ya sa ma ta kalle ki. Za ta ce kina murna tun da kika zo biki kika kwana a gidana."

Farida ta ce to sai dai ta ce amma ita ina ruwanta? Tun kafin auran ta da Tafida ya ke aminin mijinta kuma ko shi yayan nata ai ya je É—aurin auran

"Allah na tuba su maza ina ruwan su?

"Ai shi kan shi ya yi ta faÉ—a da ya ji labari kin san Tafidan bai sanar da shi ba sai Hajiya ce ta kira shi tana faÉ—a mai akan na gida ne ma. Kai tsaye ya kira shi ya ce in ta sake yi masa gaddama ya kora ta gida."

Na riƙe baki ina faɗin" Lamarin har ya kai haka? To Allah ya kyauta."
"Ni in na je zan yi mata faÉ—a ruwanta ne ta ji ko kar ta ji ta gyara "
Ni dai da man ba komawa zan yi ba, zuwa la'asar suka barni ni kaɗai a gida har su Jidda sun tafi Gwammaja. Farida tun wajen biyun na rana ta wuce Gwammaja daga can za ta ƙarisa sabon gida. Amina da Marwa tare suka fita zuwa Ɗorayi, har Yumna da ita Baby suka tafi suka bar ni kaɗai.
Zuwa can Yallaɓai ya kira ni ya ce yan uwan Rabi'a za su kawo ta nan gidana na ce sai sun zo. Na tashi na ɗan ƙara gyara gidan na saka turaren ƙamshi
Ganin ba kowa a gidan har zan kira Munnira na ce ba za su dawo ba ne! Sai ga su ita da Hauwa sun shigo, na ce wayar dake hannuna su nake shirin kira na ce za a kawo mini amarya babu yan tawagata suna ta dariya.

Sai gabda mangariba suka zo. Musbahu ne ya kawo su a motar Yallaɓai, daga Gwamnaja suke an kai ta wajen Nene da su Maman Farko. A can kuma sun fara kai ta shashen Gimbiya. Hauwa ke faɗa mana Mimisco ce ta yi mata fata fata shine da aka kai mata Amaryan ta fito ta karɓa. Ni ma sun kawo min ita suka kuma damƙata amana a hannuna a matsayina na babba na kuma riƙe hannunta na ce na karɓa Allah ya zaunar damu lafiya.

Matar Baffan Rabi'atun na Kano da take zaune a gidan su ce ta kalle ni tana mai faɗin"Rabi'atu ƙarama ce a cikin ku don Allah a kula da ita. In ta kauce a karkato da ita, duk da ba kwa gida ɗaya tun da ke ce babba ki taya mu riƙe wannan Amanar don Allah"
"In sha Allahu. Da yake ba daÉ—ewa nima zan koma can ba matsala Allah ya ba mu zaman lafiya."
Aka amsa da Amin gabaɗaya sannan aka yi addu'o'i sun kawo mini kayan su fulawa har da su dakuwa da nakiya sai tarurukan kamshi na ɗaki da na kaya sai atamfa da kololi sai filantai da kofuna har da kayan kwalliya kaya fa himiɗi ni na ce ma su rage kayan sun yi yawa suka ce ina tuwon girma a miyan shi nama. Sun kai ma surukanta da ɗayar abokiyar zaman nata. Muka karɓa su Munnira suka taya ni godiya nan na tsayar da su suka yi salla sannan suka tafi bayan sun sake yi mini sallama tun da sun ce suna ma yar da ita gida suma za su wuce. Baƙin Maiduguri kuma asuban cin gobe za su ɗau hanya

A bakin Musbahu nake jin suma su Nene haka aka kai musu himilin kayan arziƙin nan ita da su Maman Farko, har da na yayyen miji.
Ina ta mamaki daga baya kuma sai na cire shakku suna da al'adu sannan daga gani suna da hali da rufin asiri. Sannan kamar yadda suka ce ne Tuwon girma miyan shi nama shima Yallaɓai ya yi harkan girma in sun yi masa kara babu laifi a ciki. Ban bari su Muniira sun tafi ba na ce su tsaya mu raba kayan nan suka ce bai kamata ba na bari in Yallaɓai ya zo ya gani sannan sai da suka faɗa na yi wannan tunanin. Dare ya yi sosai shi ya sa ban kai su gida ba tun da Yallaɓai ya hana ni tukin dare tun da na faɗa rami wata rana na dawo daga ɗorayi ni da Baby da Yumna mota ta maƙale na kira Yallaɓai a waya. Ƙarshen ta dai nan motar ta kwana sai washegari aka ciro ta daga ramin.

Mun yi waya da Marwa sun wuce. Farida ce ta ce mini tana Gwammaja can za ta kwana sai a safe za su É—au hanya. Ni da kaina na faÉ—a mata kayan da dangin Rabi'atu suka kawo mini sai itama take ce mini.
"Haka suka kai ma Gimbiya. Sannan nan ma bayan na su Nene har da na yayyen miji, har maza suna da kula. Waliyi kuma Baba Tafida na da shadda."
Na riƙe baki ina faɗin" Haka Musbahu ya ce. Ma sha Allah. Allah ya saka da alheri ya ba mu zaman lafiya."
Ta amsa da Amin ta cigaba da faÉ—in" Ai Gimbiyar da kyar ta fito fuskar nan ta kumbura saboda kuka na ce sakarya zauna ki kashe kanki saboda namiji. Shi kin ga bai fasa ba, ba kuma zai fasa ba ko da mutuwa za ki yi"

"Wallahi.."

Na faÉ—a ina jinjina kaina.

"Da zai fasa tun boren da ta yi a farko da ya fasa É—in."

"Ai ba zai fasa ba wallahi. Ko don ya ga karshenta ma sai ya ce sai ya yi. Ai an ce da safe Mimisco ta je ta yi mata faÉ—a akan abin da ta yi jiya. Nene ma an ce ta kira ta a waya shi ne har yau ta É—an saki jiki kaÉ—an."

"Allah ya kyauta "
Chapter 79 · 0% Book details