Sashe 17
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar da Nene ta zo ita da Hajiya iya da Maman farko a raina na ce duk abin dake cikina ɗan gata ne. Tun da har su Nene suka zo duniya. Nene ko faɗi ta ke yi Allah ya raba lafiya. Amma ko su kan su sun yi ta ƙorafin rama ta da rashin cin abinci na ce komai na ci sai na yi amai kuni kawai ke zama a cikina shima mai zafi. Ruwa ko rabon da in sha har na manta. Yallaɓai tsausayina ya ke yi sai ya ce ya za a yi ɗan adam ya rayu ba ruwa na ce to ga shi dai ka gani. Gimbiya sau ɗaya ta dawo shima ba ta daɗe ba ta tafi sai na ga kamar ba ta murna da samun cikina. Amma sai na yi saurin cire tunanin haka a raina sai na yi mata uzuri na kuma saka mata kyakyawan yaƙini. Inna Mariya ni da kaina na kira ta na faɗa mata ta yi ta murna ta kuma zo har gida ta duba ni.
Ko da nake kwance in ana son Hijabai ko kaya Jidda ke mgana da mai ɗinka min daga Zaria a kawo kuma ta zauna duk ta saka musu sticker ta kuma saka su a ledojinsu shi ya sa ba ni da damuwa. Na shafe wata ɗaya da wani abu ina wannan zazzafan laulayi sannan na ɗan fara samuwa. Na fara cin abinci tuwo haka sai ɗanwake sai awara sai dambu, amma ban da su shinkafa da taliya. Duk sona da fura da kayan marmari na daina son su yanzu, ruwa kuma na fara sha amma sai mai sanyi ko na ce mai ƙanƙara ya na narkewa ina sha. Yallabai ya yi ta faɗa wai sanyi zai kamani amma shi kan shi da ya ga shi ne ruwan da na ke sha sai ya ƙyale ni. Na ɗan fara samuwa tun da na daina kwanciya kasalar sai dare ya yi yanzu ta ke nika min jiki, sannan tun da na fara laulayin nan ban yadda mun yi ɓarnan ruwa da Yallaɓai ba to ina ta kaina. Shima kuma bai matsa mini ba, kuma bai sani ba kwata kwata abin ne na ji ba na ma son shi. Na ɗan fara dan kiɓan kumatu amma fa kaya na duk sun yi mini yawa. Na faɗa a raina na faɗa asarari da cewa wannan cikin ɗan gata ne shi ya sa ya ke wahalar da ni. Amma dai na ji sauƙi sosai ba kamar kwanakin baya ba.
Cikina na wata uku cikin na huɗu aka fara hidiman bikin Sulaihat ɗin Anty Bahijja. Matar nan ba ta zo ta duba ni ba duk da ta san ba ni da lafiya. Amma dai Anty Maimuna ranar ta biyo Nasara sun taho tare. Da Anty Bahijja da Halima ba su zo ba daman ita Halima tuni ta koma bangaren Gimbiya. Yarinyar nan mun sha haɗuwa a Gwammaja ko sha'anin su ta yi kamar ba ta ganni ba. Wai ni ce Halima ta ke gani ta wulaƙanta, lalle na yarda rayuwa ta na cike da mutane masu abin mamaki. Yadda ba a saka ni a shirye shirye ba, ban tusa kaina ba an dai fidda ankon mother eve da na yinin biki. Yallaɓai ya siya mini tun da matarsa ce ta ɗauko Gimbiya. Jidda kuma Anty Zuwaira ta yi mata tare da sauran sa'aninta su Farhan Anty Maimuna Baby ma su suka yi mata, ni ina fama da kaina ba ma ta kan bikin na ke yi ba, bikin zai kama babbar salla saura kwana tara ne.
Na dai san Kaduna za a kai ta. Bikin kuma zai yi jama'a tun da har Anty Zabba da muka yi waya ta ce za su zo gabaɗaya har da yara tun da ba makaranta. Sannan kaf su mazan gidan da ke zaune ne sa za su taho da matan su. Matar Jafar ce kawai ba za ta zo ba ita za ta tarbi bakin nan in ji Anty Bahijja, nima duk a bakin Munnira na ke jin wasu labaran a bakin ta na ji su Gimbiya su ne ƙirjin biki sannan har list an yi na mutanen da za a tafi da su a kaduna. A dalilin ina fama da kaina ban ji a raina zan je kai Amarya kaduna ba, ko da ma ina lafiya ba zan tusa kaina ba.
Ban je gidan bikin ba ma sai ranar laraba da a ka yi mothers eve ɗin. Yallaɓai ma cewa ya yi in ba zan iya ba na yi zama na su Jidda su tafi sai na ce zan iya. Tare da su Hauwa muka tafi can muka iske matar Muhammad Kabir Nafisa har Faridan Tariq ta zo Marwa ma ta zo muna tare da ita tun da gidana ta sauka. Anty Bahijja ta sha gayu ka ce ita ma Amarya ce da ƙawayenta suma yan gayu su Gimbiya ana ta shiga da fita har makeup ta yi su Khalipa ma an sha gayu. Anwar ne ma na gan shi a hannun Baby ta na fama dashi,
Ni dai na je na gaishe da uwar biki na yi mata fatan alheri shi ne ta ke ce mini an ce ba ni da lafiya na warke kenan na ce mata Alhamdulillah.
Kowa ya ganni sai ya ce na rame amma fa na yi shar da ni. Suwaiba kam har sai da ta ishe ni wai ban ga kyan da na yi ba ne ko Tafida ya ganni kafin na fito na ce ban sani ba. Mun haɗu da Gimbiya amma ba ta minI mgana ba da cewa ita ta na fama da jama'a ba ta ganni ba ni ko na ce ba zan bi ta domin mu gaisa ba. Ita da Najan Anty Zuwaira ne akan komai kuma suma sun ui gayyar ƙawayen su irin su yan gayu kirari kawai suke yi mata tun da kusa damu suka zauna a haraban gidan in da aka saka kanofi da kujeru. Su Ma'u ana gefe ba karsashi to ta ga iyayenta a kinibibi dole ta koma baya.
Gimbiya suke ta raba takeaway da snack a ciki da naman kaza sai ruwa da lemu. Da ta zo wajen ƙawayen na su sai shewa ya hau ta shi ana yi mata kirari.
"Ka ga Saudatu sa'ar mata. Gimbiya kike sunan ki ne. Kuma kin cika Gimbiya a zuciyar Injiniya Yusuf Tafida. Takawarki lafiya giwar Tafida. Takawarki lafiya Amaryan Tafida. Takawarki lafiya uwar maza a gida ko da kika je an haihu amma ke da kika tashi sai kika yi irin haihuwan da ba a taɓa yi ba. Ka ga uwar maza a gidan Alhaji Yusuf Tafida. Ko gobe aka sake masa haihuwa ba za a kwantata irin ta ki ba"
Sai suka buga shewa ta miƙa hannu suka tafa ta jiya musu kugu kafin ta ce" Wallahi ko gobe aka sake masa haihuwa ba za ta kama kafar irin tawa haihuwar ba faɗi ki ƙara."
Ta faɗa ta na wani fari da ƙara juyawa.
"Takawar ki lafiya ki juyi dai Gimbiya a girman ki ne. Kin ci lokacin kuma za ki ci na wasu in sha Allahu kuma daga kanki ba ƙari kin cika duka gurbaben mata huɗun nan"
Sai kawai ta ɓalle jaka ta fara zazzaga ma mai yi mata wannan kirarin kudi suna ta ihu da shewa sai hankula duk ya koma kan su.
Duk da Maganar suke yi amma ko waye ya ji ya san magana ce mai harshe damo ko na ce habaici.
Hauwa ta kalleni ganin na yi shuru kawai ina zaune.
"Kamar fa da ke suke. Wai ko da ta zo an haihu amma ba a yi kamar irin ta ta ba"
"Kuma wai ko da an sake haihuwan ba za a sake irin ta ta ba"
Munnira ta amshe itama.
"Da Sadiya fa suke yi. Shi ya sa na tsani Gimbiyar nan munafuka ce baƙn ciki take yi kin samu ciki ta so ne ita ta yi ta haihuwa ke kuma ki zama yar kallo."
Hauwa ta saki tsski kafin ta ce" Wallahi haka ne ma. Sai kin ji mganganun da take zuwa gida ta na yi. Ta yi ma Tafidan da Dangin sa haihuwan da ba a taɓa yi masa ba. Tun da ta haifi maza har ji fa na yi wai ta ce yadda ya ke son su Khalipa ko su Jidda albarka."
"Ka ji sakarya. Ya fara samun su Jidda? Ai wallahi ƙarya ta ke yi.'
Baƙin ciki suka hana ni mgana amma na daure jin Munnira ta ce wallahi za ta tashi ta je ta yi musu mgana sai na riƙe ta ina faɗin" Rabu da su so suke a tanka a yi wani abu kuma ace ba mu da gaskiya ku ƙyaleta. In za ta je ta faɗa ma duniya cewa Yallabai ma ya fi son ta a kaina ni bai dame ni ba. Fatana na sauka lafiya."
"Allah ya sa ki haifi namiji na ga ta tsiya."
Sai na yi mirmishi ina tuna wayar da na yi da Dr. Aisha AKTH. da na faÉ—a mata ina da ciki ta yi murna karshe ta ce Allah ya kawo boy ni kuma na ce mata ko boy ko girl duk wanda ya Allah ya bani ina iso.
Yanzu É—in ma cewa na yi.
"Ko namiji ko mace duk wanda Allah ya ba ni iso."
Suna kallona sai na kaÉ—a kai kafin na ce" Ni ba ruwana da jinsi Ni ko duka mata zan tara ina so. Ita haihuwan maza ke gabanta."
Daga nan na kashe maganar. Amma har Suwaiba sai da ta zo wajen mu ta na zagin Gimbiya a cewarta ni ban yi kishi da ita ba ita da ta aure mini miji sai ita. Ant Zabba ba ta wajen da ya ke so sun iso har da Amaryan Usman É—in itama da tsohon ciki za ta yi haihuwa na uku kenan itama kamar Gimbiyar gwarne take yi. Da ta zo wajen mu ta ji ana mai da zence ta yi ta mini masifa ta na faÉ—in ina da sanyi na daina sanyi da kishiya za ta rika cin kasuwarta a kaina na yi dariya kawai ban ce komai ba.