← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 103

Sashe 31

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ƙarshen watan aktober a ka ba da sanarwa lafawar cutar corona. Farkon watan November kuma a ka buɗe gari har da makarantu gabaɗaya. Su Jidda a na ta murna an koma makaranta ta ɗauka da sun koma za su fara jarabawa ne amma sai a ka ce sai sabuwar shekara saboda calander ya birkice Jamb sai sun sake rigister. Wato abubuwa da dama a hutun nan na corona ya dagula shi, komai ya koma baya sai dai kuma a hankali komai zai dai- dai ta ni dai ban yi maganar komawa makaranta ba, in ma na yi Yallaɓai dariya kawai zai yi mini na ji ma kamar ba ni da rabon karatun ne daman haka Yallaɓai yake so. Ko da na koma bayan na haihu renon fa ai aiki ne mai zaman kan shi kafin sai kawai na cire karatun a raina na ce wata ƙila ba alheri ba ne. Na mai da hankalina kan sana'ata na hijabai da inears. Kuma Alhamdulillah ina samun alheri matuƙa.

Ga shi cikina ya yi ƙasa na shiga watan haihuwana. EDD dina 17 November ne. Har ina ce ma Yallaɓai in na haihu zan haɗa mana da Wedding Annivesary na cikar auren mu shekara 20 wanda tun June muka cika shekarun lokacin ina ta kaina laulayi ya saka ni gaba ya sa ko maganar ma ban yi ba Yallaɓai daman ni nake tuna masa tun a baya ballantana yanzu da harkokinsa suka yi yawa.

*****

10. November 2020.
Tuesday. Talata.

Lafiya lau na tashi ko ciwon bayan da kwana biyu na kan tashi dashi yau ban ji sa ba. Yara duk sun tafi makaranta daga ni sai Yallaɓai a gida kwanan su uku a Abuja sai jiya ya dawo da daddare ya sauka a gidana daman daga can gidan Gimbiya tafiyar ta kama shi.

Lafiya lau muka karya, ya ce ba da wuri zai fita ba sai bayan azahar muna cikin bedroom Yallaɓai na kwance ni kuma ina zaune a gefen gado ina ware kayana da na yara sai na Yallabai da safen mai wanki ya kawo su. hira muke yi sama sama sai na ji shuru ashe barci ne ya ɗauke shi.
Sai na cigaba da aikina. Na kwashe kayana na jere cikin kwaba haka ma na Yallabai na su Jidda ne na ce bari na kai musu ɗakin su, sai dai ina in mikewa ne ya gagara. Ƙafafuwana sun riƙe, bayana ya ƙage, daman kafafun sun kumbura cikin ya sunkunya ya yi kasa ba ni ma da riga a jikina da ga ni sai zani zafi kawai na ji ina yawan ji tun da cikina ya shiga watan haihuwan shi.

Na yi ƙoƙarin dafa jikin gado na miƙe ai ban san lokacin na saki ƙara ba, wanda ya ta da Yallaɓai a firgce. Tuni har na duƙe a kasa ina riƙe bayana da na ji kamar ya tsage.

"Me ya faru?

Yallaɓai ya faɗa yana dirowa gabana.

"Baya na. Wayyo Yallaɓai bayana ya tsage."

Na faɗa cikin tsananin azaba har ina cije bakina. Yallaɓai na duba bayan nawa ne ni kuma ina ta wash wash kawai na ji ruwa na bin kafafuna ina dubawa sai na ga har faya ta fashe ai sai na zaro ido cikin ƙaraji nake faɗin.

"Haihuwa ce Yallaɓai. Haihuwa ce faya ta fashe."

Na faɗa ina makarƙyata jin yadda marata ke wani irin juyawa. Kusan fa na manta yadda haihuwa take shekaru goma ba wasa ba. Ji nake yi kamar ban taɓa haihuwa ba azaban da nake ji kamar ban taɓa jin irin shi ba.

"Innaliillahi haihuwa? To mu tafi asibiti ko?

Ya faÉ—a cikin É—imuwa shi ma ya ruÉ—e kamar ni. Kawai sai na yi zaune kawai tuni zanin da ke jikina ya yi ta kanshi nima ina ta kaina na fahimci gajeruwar naguda zan yi. Haihuwa ce gadan gadan ta taho mini ban shirya ba.

"Ba lokaci Yallaɓai. Ba lokaci ka zo ka zoo.."

Na faɗa da ƙaraji jin abu na turowa ta gaba na. Kan ɗa ne ya turo, Yallaɓai ya ruɗe bai taɓa ganin haihuwa ba sai ranar shima da ya matso kusa na riƙe shi gam ina nishi amma bakina bai mutu ba.

"Zai fito. Zai fiiiiii.. too.."

Na faɗa ina karta kumbuna na a jikin fatar hannun Yallaɓai saboda nishin da nake yi, ga kan ɗa na ƙoƙarin fitowa da Yallaɓai ya leƙa ya gani sai ya ruɗe faɗi yake yi" Ga shi nan fa zai fito na shiga uku.".
Ya faÉ—a cikin fitan hayyaci..
Ni dai bam san yadda a ka yi ba domin kamar na shiɗe ne da na yi wani irin ƙarfafan nishi ina ƙara damke hannun Yallaɓai ihun har sai da muryata ta dishe. Sama sama na ji abu sulumf sulumf har sau biyu ya faɗo lokaci ɗaya da kukan jaririya

"Inyainya. Inya."

Sai na koma na kwanta a ƙasan tayels ɗin dake bedroom ɗin domin cafet ɗin yana da ga wajen ƙuguna ne, wajen kaina kuma tayels ne haka na ji jikina ya saki yaraf na kwanta kawai ina maida numfashi ina jin Yallaɓai cikin fitan hayyaci yana faɗin.

"Sadiya kin haihu. Wallahi kin haihu."

Muryansa cikin farinciki da wani irin É—imuwa mara misali.
Ni kuma ina ta sauke ajiyar zuciya a jere ga zufa da ya wanke minu jiki kamar an kwarara mini ruwa. Haihuwa na yi cikin abin da bai gaza da mintina goma ba. Allahu akbar Allah shi ne Ubangiji mai yin yadda ya so a lokacin da ya so.

"Alhamdulillah."
Alhamdulillah'

Na ke faɗa a zucci da sarari saboda Ubangiji ya yi mini sutura na haihu a cikin ɗakina tare da mijina cikin lafiya da ƙarfina. Allah ne abin godiya.

*Janafty**TKGB3H08*

*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*

Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732

Ganin da na yi Yallaɓai a ruɗe yake, ni kuma jikina duk ya saki ina kwance itama jaririyan na kwance cikin ƙazanta tana ta callara kuka, tun lokacin da ta faɗo ta callara kuka na san cewa da gaske ƴa mace na sake haifa.
Sai na kira sunan Yallaɓai ya taho wajena sai na ce ya kamani cikin rawan jiki ya kamani na tashi zaune. Sai a lokacin  na fahimci jaririyar tare da uwa mahaifa ta faɗo shi ya sa na ji fitowar abu sau biyu daga ƙasana.

Zanin da ke jikina da ya yi gefe na ce ya ɗauko jiki na rawa ya tashi ya ɗauko sannan na ce ya buɗe dirowan gadon mu ya ɗauko kit ɗin mu na magunguna akwai reza a ciki, bayan ya kawo mini na karɓa na rike jaririyan shi kuma na ce ya riƙe zanin na saka ta a cikin zanin tana hannun shi sannan na daidai ta na yanke cibiyar na ce ya matsa daga wajen tun da gabaɗaya mun yi dama dama daga ni har shi cikin kazantar haihuwa.

"Ya zan yi mata Sadiya?

Ya faɗa yana kallona ya na kuma riƙe da jaririyar.

"Ka naÉ—e ta a cikin zanin ka kwantar da ita a kan gado ka zo ka kama ni na tashi."

Haka ko a ka yi bayan ya kwantar da ita sai callara kukan jarirai take yi ya zo ya kamani na tashi tsaye. Na saka shi ya buɗe karamar akwatina in da na tara kayan haihuwa na ce ya ba ni na ɗaura. Bayan na ɗaura na ce ya je ya saka min ruwa a hiter tiolet da gudu ya fita ni kuma na tattaka ina ware ƙafa domin sai ina jin kamar na ƙaru ta ƙasana na isa in da yarinyar ke kwance na ƙura mata ido ina kallonta lalle dole ta ci sunan uwata. Domin a kammanni ma ni ta ɗauko.

Yallabai ya dawo É—akin ya ganni tsaye ina kallon ta yana zuwa na kalle shi da mirmishi kafin na ce.

"Alhamdulillah mace na haifa Yallaɓai. Mace Allah ya sake ba mu"

Sai kawai ya rumgumeni bai damu da yanayin da nake ciki ba. Cikin tsananin farinciki ya ke faÉ—in.

"Alhamdulillah. Allah na gode maka da ya sake nuna mini wannan ranar"

Wai a haka don ƙarfin hali Yallaɓai sai da ya sumbaci bakina na ture shi ina faɗin" Ko minti goma ban yi da haihuwa ba Yallaɓai?
Sai ya yi mini dariya kawai bai ce komai ba.

Shi na saka ya kwashe kayan su Jidda dake zube akan gado ya saka musu cikin wardrope kar su ɓaci. Ba ni da tsummokarai sai kawai na ce ya kwaso doguwayen rigunan da na ɗinka na yi amfani da su lokacin ina da ciki waɗanda shi da kan shi ya saka musu suna da buhu in naɗe kazantar da su kawai a kai su bola bayan an wanke tun da sun gama amfani.

Jaririyar kuma na goge mata jiki da dotel, tare muka goge kazantar ni da Yallaɓai ina cewa ya bar shi yana mini faɗa  wai na mayar da shi mara tausayi ta ya ina cikin wannan halin zan ce ya koma ya zauna yana kallona ai sai na yi shuru. Tas muka gyara wajen duk da ba sosai ba amma mun goge kazantar haihuwar. Ita kuma uwa mahaifa na ce ya je ya haƙa rami a haraba ya rufe. Ya ɗauka cikin wani zani ya fita dashi ya je ya rufe bayan ya dawo ya sake fita da cafet tun da a kan shi na haihu na ce ma Yallaɓai kawai a wurgar da shi ya ce  a'a sai an wanke in zan yi kyauta da shi ne sai na yi amma ba zai bari a wurgar da shi ba.

A baho babba da ya ɗauko muka tara kayan da muka yi gogen-gogen na ce ya fita dashi can ta ƙotar kitchen.
Chapter 31 · 0% Book details