← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 103

Sashe 39

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar yini na yi zuciyata ba daÉ—i da wuri suka gama suya suka É—ibar mini nawa. Sai na su na can Gwammaja. Na saka su Ya Aina suka É—iba na su har da y'an can gandun albasa. Nima na É—ibar ma su Hauwa a ka raba da yaji kafin yamma gida ya watse har su Laila suna koma ÆŠorayi za su kwana washegari su É—au hanya. Ina ta musu godiya na su Samira Rahila na ba mawa na ce ta aika ma Maijidda za ta kai ma su Samira. An yi taron suna an ta shi lafiya gyaran gidan washegari Saude da Marwa da Mubeena suka gyara mini tun da sai ranar da Yamma Kawu ya zo ya É—auke ta suka koma rano.

Tun da a ka yi suna a ka gama na mai da hankalina wajen renon Yumna. Ta tsiri rigiman dare ba ta barina na yi barci ɗan kumarin da na yi duk na fara sakewa. Ga shi Yallaɓai can gidan Gimbiya yake kwana nan ya gama cika mini baki shi bai amince ya koma can ba amma sai ga shi an gama taron suna gida ya watse amma bai dawo ba ni kuma ban yi masa magana ba daman na san can munafumcin ne irin na su na maza. Sai dai ya zo duba mu safe da yamma.
Daga ni sai yara suma suna zuwa makaranta sai yamma asabar da lahadi kuma Tahfez Jidda har ta kusa sauka izifinta hamsin da biyar Baby kuma ta na cikin izifinta na ashirin. Ni kaÉ—ai a gida ga fama da aiki ga fama da Yumna wacce ta cika rigima ga tsotso mintina kaÉ—an ta fara rigiman nono shi ya sa ta zama wata burkuta da ita.

Muna da kwana goma sha biyar da haihuwa na ga Yallaɓai ya dawo kwana a gida na kamar zan yi masa magana sai dai ban yi ba. Kwana biyu tsakani kuma sai ya ɗauke kafa ya koma can ni sai na koma kawai na zura masa ido saboda na ga jeka ka dawon da ya ke yi, na kasa gane nufin sa.

Sai a tsakanin Munnira ta sake leko ni a bakinta nake jin rigima ce suka yi shi da Gimbiyar ta sa har sai da Nene ta shiga ciki. A kan dai maganar kuɗin da ta ce ya ara mata na shipping ɗin kayanta ya ce ba shi da kuɗi amma ni ya ba ni kuɗi na yi suna har ina kiran mai hoto. Ita ko abin ya tsaya mata a rai ta ce mini ranar ta na gidan a ka yi har da su Maman farko a shigar maganar shi kuma ya rantse ba shi ya ba ni kuɗin wasu abubuwan ba da kuɗina na yi, amma ba ta yarda ba ita a dole ya yi rashin adalci. Wato dalilin dawowan shi gidana kenan sannan kuma ya koma bayan sun shirya. Ni dai na ce ma Munnira Allah ya kyauta can su ƙarata.

Sai da ma muka yi maganar hotuna da Munnira sannan na tuna na tura ma mai hoto ragowan kuÉ—in sa ya turo mini hotuna. Washegari ko carbi na yi a status É—ina hotuna ne ba adadi na saka.
Na farko nawa da Yallaɓai na saka da yara wanda Amina ta ɗauke mu ranar suna da safe.
Na yi caption da cewa" Shekaru ashirin da albarka Æ´aÆ´a uku. Alhamdulillah."
Sai na saka wanda muke mu uku ni da shi da Yumna. Shi ke riƙe da ita ni kuma sai na shafa sajen sa. A ƙasan hoton na saka sticker ɗaga hannu na za a saman kai sannan na ce" Jama'a na ba ni Yallaɓai na ne na ga ya fara furfura"
Ai ko na sha comments har Ya Hamza sai da ya yi mini mgana da cewa. Ke kina nufin ya dauwama a saurayin da kika aura ne? Sorry yarinya."

Maijidda Bala ta yi dariya ta ce" Sadiya rayuwar auranki da Yallaɓai a bar sha'awa ce Allah ya bar ku tare."
Na amsa mata da Amin ba ta san tarin ƙalubalen da na fuskanta ba ne. Ba su san ma an yi mini kishiya ba sai a sunan Yumna na faɗa musu suna ta mamaki ai ni yanzu na yi hankali na kama jama'a. Ni dai ban ɗora hoton Gimbiya ba amma ma tura mata wanda ta ke ciki haka ma su Anty Bahijjs. Yan gidanmu duk na tura musu sun ɗora mu. A gidan su Yallaɓai da ga Mimisco sai su Suwaiba su Munnira daman nawa ne, mazan kuma daman Musbahu da Adnan suka yi ta ɗora mu suna addu'a. Yallaɓai ma turamai na yi wajen guda hamsin sai turo mini emojin mamaki ya yi ni kuma na ce masa miye? Da alaman tambaya sai ce mini ya yi wai wa ya ba ni kuɗin waɗanan hotunan? Na ce tun da bai bai ba ina ruwan shi sai ya turamin na emojin baki da zip kuma ina tunanin bai buɗe hotunan ba, shi ya sa ko a status bai saka ba. Ban damu ba sanin halin Yallaɓai wani lokacin ba ya yin abin da a ke zaton shi da shi sai saɓanin haka

Har Shemau Ma'un ta kirani ta mini barka saboda ma yafe ma Ma'u shi ya sa itama na ji na yafe mata. Ta ce mini in ta shigo garin za ta shigo ta ga Baby na ce sai ta zo so. Kara an yi mini shi sosai kuma na gode ni ce na tara turamen atamfa kaɗan ne babu a hamsin bayan kayan jarirai da sabulai da sauran su da masu tura mini kuɗi. Da na nuna ma Yallaɓai sai da ya jinjina kai kafin ya ce wai ni da kaya sai nan da shekaru biyar na ce bai isa ba. Ya saka albarka yana dariya a ciki na nemi shawaran shi na ce zan ba ma Gwaggo ɗaya Nene ɗaya sabulai kuma na ba su Maman farko da su Inna Mariya ya ce duk yadda na yi dai-dai ne tun da kayana ne. Ban damu ba sanin halin shi, shi ya sa na yi gaban kaina na ware musu da niyyar in na yi arba'in in na je gaishe su na kai musu.

Mun shigo watan december ƙarshen shekara. Ina ta jego na ina kula da kaina gefe ɗaya bikin Alhaji Mustapha na ta ƙaratowa. Ma'u duk ta damu ni ce ma ƙarfin gwiwanta. Sai ma Allah ya sa a ka ɗaga bikin sai Jan ƙarshe.
27 ga watan december na yi arba'In a ranar da na yi arba'in Gwammaja na yini na kai ma su Nene saƙon su suna ta godiya tun da na je Yumna na tsakanin ɗakunan su Maman farko da Hajiya iya sai da zamu fita. Washegari kuma na yini a ɗorayi na kai ma Alhajinmu matarsa nan da nan ya ce shi kan ya saki jidda ya samu sabuwa Gwaggo na dariya ta ce da tsohuwar zuma dai a ke mgani. Ranar ma a wajen Alhajinmu ta yini kuma ikon Allah ba ta yi rigima ba, a jere na haɗa fitan na je gidajen su Ya Aina na je har can gandun albasa wajen su Inna Mariya. Na je gidan Munnira da Hauwa na yi musu yini da ban gajiya wajen kwana goma har Yallaɓai ya ce ba zan sake fita ba duk gari an gama gani na kullum sai na fita sannan na samu natsuwa a gida na fara gyara kaina.

Surayya dee ce mai kayan ɗa'a ta gyara ni da haɗin kazar sababi na masu jego. Daman kuma bayan haihuwata na dage da cin kayan marmari da ganye da kuma kifi domin ƙarin ni'ima. Sannan Amina ma ta aiko mini da Gumba na sha da madara Yallaɓai na ta rara gefe na hana shi sai da na ji na yi tsab sannan na gayyace shi. Ranar na sha sambatu amma na gane ba ni da wayau, domin Yallaɓai kaca kaca ya yi wajen ɓarnan ruwa sai da ya famshe kwanakinsa har yana haɗa wanka ma.

*Janafty**TKGB3J010*

Washegari ma bai bar ni na huta ba, ko falo bai bar ni na fita ba sai wajen sha ɗaya na safe su Jidda ma shi dai ya fita suka gan shi suka gaishe shi. Daman ba sa jira na yanzu sun girma komai na buƙatunsu, su suke yi ma kan su. Sai alokacin na samu damar yi ma Yumna wanka sannan nima na shiga wankan kuma na bar mishi Yunma kwance a gefen shi shi kuma yana duba abu a cikin laptop ɗin shi.

Ina fitowa ɗaure da Towel a ƙuguna na iske sa har ya gama abin da yake yi ya ture laptop ɗin gefe. Tambayarsa nake yi Yumna ta yi barci ne? Sai ya leƙata yana faɗin ta soma barci.

"Ai gwara ta yi barcin nan kowa ya huta."

Na faÉ—a ina mai zama saman stool É—in madubin dake bedroom É—in namu.
Ban san tahowar shi ba sai kawai jin sa na yi yana shafa min wuya a lokacin ne na ci karo da fuskarsa ta jikin madubin dake gabana.

"Me ya faru Yallaɓai?

Na faɗa ina mai kallon shi ta madubin, bai amsa ba sai ma sunkuyowa da ya yi ya na mai sumbatar wuyana. Tun da na ga haka na sha jikin jikina da sauri na ture shi ina faɗin" Na yi wanka fa Yallaɓai."
"Me ya sa kika yi wankan?
Mamaki ya sa sai da na É—ago ina kallon shi.
"E. Ai ban sallameki ba hajiya."
Ya faɗa har yana wani ƙara tsumewa irin shi fa da gaske yake yi.

"Yallaɓai tun daran jiya kake abu ɗaya. Yau da safe ma don Allah kai baka gajiya ne?

Na faÉ—a ina cigaba da shafa ma jikina man shafawar da na lakuto a hannuna.

"To ni ban gaji ba."

"Ba ka gaji ba?

"E"
Chapter 39 · 0% Book details