← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 103

Sashe 90

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faɗa yana haɗe rai sai na yi mirmishi kafin na ce"Allah ya baka haƙuri."
"Ni da gidana duk hukuncin da zan yamke sai kin ce ba haka ba? Ki fita daga idona Sadiya Tam"

"In na fita idon wa zan shiga Yallaɓain?

Na faÉ—a ina masa wani kallo.

"Uhm za ki yi bayani ne."

"Sorry Oga."

Na faɗa ina dariya ganin yana mirmishi sai da ns saka shi ko dariya ƙarshenta ma bangarena muka koma tare ya je wajem yara ya daɗe a tare da su sannan ya zo ya na challagin ɗina wai me ya sa yaran shi ba su je makaranta ba?

Ina hararan shi na ce" Tun asuna ka fara mana yaƙi a gida ne za ka zo kana tuhumata."

Sai ya fara dariya wanka  ya yi bangarena ya shirya. Ya ce zai sauke Rabi'atu a makaramta zai wuce office tun ɗazu Musbsbu ke kiran shi akwai waɗanda ke jiran shi na yi masa fatan dawowa lafiya.
Bayan fitan su na rana na leƙa Gimbiya ta sha dai kuka amma dai an warware kaya. Ni dai na sake jadadda mata ta yi haƙuri  in tana so ta zauna lafiya. Ranar girki ma duk Baby ta yi mana itama nan shashena ta ci abinci muna tare da ita har dare sannan ta kwashi yaran ta suka koma bangarenta.
A ranar Yallaɓai ys ƙarishe kwanan shi a ɗakin Rabi'atu washegari ya dawo ɗakina ya yi kwana biyu sannan ya koma na Gimbiya. Ni ban san halin da suke ciki ba na ɗauka komai ya daidaita ashe ba haka ba ne, Yallaɓai dai na kwana a bangaren Gimbiya in ranar girkinta ya zagayo shima a falo kuma baya jin abincinta baya mgana da ita daga gaisuwa sai gaisuwa. Ni ban sani ba sai da ta zo tana kuka tana faɗa mini na ce ta sake bashi haƙuri amma duk da haka bayan kwana biyu ta dawo ta ce mini ba abin da ya sauya.

Jin haka da zuciya daya na ce zan yi masa mgana amma in ɗauko magamar yadda ya fara yi mini ihu a saman kaina ne na san cewa Gimbiya ta gama ɓata ma Yallaɓai rai ya gama jin haushinta shi ya sa kallonta kawai yake yi.

"To tun da ta baka hakuri ka haƙura mana? Shi kenan ita ba za ta yi kuskure ka ba ta da mar gyarawa ba?

Kawai sai Yallaɓai ya ce tun da ni ce Nene na yi masa faɗa saboda na ce abin da yake yi bai kyauta ba Allah zai kama shi.

"Ki bari Ubangijin nawa ya kamani amma ba ke ba."

Zan sake magana ya É—aga mini hannu.

"In kika sake tare ni da mganar da ta shafi Gimbiya wallahi zan kai ƙaran ki wajen Allah. Haba kin dame ni? Kin fi sanin abin da ya kamata ne? Ko sai na ce Allah ya isa ne sannan za ki ƙyaleni da wannan mganar ne?

"Allah ya ba ka haƙuri. In sha Allahu ba zan ƙara mgana bam"

"Better for you."

Tun da ya yi mini haka na koma gefe itama Gimbiyar na faɗa mata tun da ta bashi hakuri ya ƙi haƙura ta fita batun shi in ya gaji zai seuko da kansa na faɗa mata nima irin tijaran da ya yi mini daga faɗan gaskiya. Gaskiya ne yanzu Yallaɓai ya zama masifaffe abu kaɗan sai ya fara faɗa yana yi ma mutane ihu. Maganar gaskiya Gimbiya ta ba ni tausayi duk ta rame ta saka ma kanta damuwa kuma Mimisco washegarin ranar da ta zo ta saka aka zo aka tafi da mota aka aka gyaro ta dawo kamar sabuwa. Kamar ma wani abu bai same ta ba Yallaɓai da kan shi yake sake koya ma Rabi'atu mota duk da iya amma hannunta bai faɗa ba, sannan abin da na ɗan fahimta Rabi'atu ta fara raina Gimbiya ba ta jin kunyar kallonta cikin ido kuma ba ta jin kunyarta kamar farko domin akwai rana tana shashena Gimbiyar ta shigo wallahi ba ta gaisheta ba sai da na yi mata mgana. Da man abin da na kr gudu kenan yarinyar nan ta zo ta fara raina ta, ba ta da yadda ta iya.

Ban san ta in da mganar abin da ya faru ya zaga dangin su Yallaɓai ba. Amma na fi tunanin Gimbiyar ce ba ta dandara ba ta fidda mganar. Sai ga Munnira ta kirani tana ba ni labarin jiya ta je Gwamnaja Anty Bahijja tana ta masifan wai Gimbiya mahaukaciya ce za ta jama Tafida asara ita sun lura kishinta na hauka ne da man shima ina ta jiye ma Gimbiya kar ta kai wannan lokacin sai ga shi da kanta ta zo har falona tana kuka tana faɗa mini Anty Bahijja ta je ta same ta a shago sai abin ta manta ba ta faɗa mata. Wai har tana cewa in haukan ta ya tashi ya tsaya a kanta kar ta sake gigin taɓa kayan Tafida tun da ita ba ta da hankali.

"Allah ya kyauta amma ni na san irin wannan ranar za ta zo"

Haƙuri na yi ta bata tun da ni kam ba ni da yadda zan yi da su Anty Bahijja nima ai haƙuri na ke yi da su. Na ji daɗi dai Gimbiya ta fahimci duk da tana na su akwai wani wajen da za su iya nuna mata Tafida ne ya fi kusa da su kuma tun ba a je ko'ina ba ta fara ganin haka har kuma lokacin Yallaɓai bai sauko ba ni na ba ta shawara ta kira Baba Tafida ta faɗa masa komai shi ya tako har gidanmu ya hada su ya yi musu sulhi mu ma ya tara mu ya yi mana faɗa. Dalilin zuwam Baba Tafida ys sa Yallaɓai ya sauko ya dawo yana sauraran Gimbiya amma ta ɓarar da alfarmanta mai yawa a wajen Yallaɓai
motar da ta gama faÉ—a a kanta tana ji tana gani Rabi'atu ke hawa motarta tana zuwa makaranta, tana kuma shiga gari da abin ta amma ita miji ke jin haushi har Rabi'atu tana É—aukan Gimbiya a mai yi mata hassada tun da na san za ta faÉ—a ma dangin ta kuma kowa da maganar da zai kawo mata
Balle na ga tana da ƙawaye suna biyo ta gidan ni dai ba ruwana nawa ido ne tun da mijinta bai hanata tarkacen ƙawaye ni a wa? Iyaka dai in sun zo za ta kawo su har bangarena su gaisheni abinci ma ni nake ba su wani lokacin tun da in dai tana makaranta ni ke dafa abinci da ita ba kuma wanda ya sakani ni na saka kaina ganin wata rana sai yamma take dawowa ta gaji ba za iya wani girki ba shi ys sa nake yi dafa abincin da ita.
Mota kuma Yallaɓai ya ce bai siya ba in Gimbiya ta isa faɗan ya sa ya siya. Na ce ta yi shuru ta ƙyale shi, sai yanzu ne Gimbiya ke son dawowa jikina ta makara amma duk da haks ban gwasale ta ba. Ina ba ta shawara kamar yadda zan ba ma kaina kums ni daga ita har Rabi'atu daya na ɗauke su.

*****

Mun yi azumin watan Ramadana mun yi salla. Jidda ta dawo gida salla amma ana fice sallata koma saboda za su fara jarabawa. A bayan salla muka muka yi auran Anti yar wajen Ya Murja Kaduna muka kai ta muna gama nata muka faÉ—a ma Firdausin Ya Balki. Ita kuma Funtua muka kaita auran gida babanta ya yi mata. Duk fa mun zama iyaye girms ya kams mu tun da mun aurar mun kai ga jikoki ma.
An saka ma zainab ƙanwar Ma'u rana itama dangin  mahaifinta a can kura ne za su aurar da ita ga ɗan katsina.
Lokacin da muka yi sha'anin Rabi'atu ba ta nan ta tafi Maiduguri ganin gida, Gimbiya ce kawai ta zo mini biki da ƙannenta har da Maryama da muka taba samun matsala. Yanzu sai gaisuwar mutumci ina anfanin to rigima? Har su Munnira duk na ce su saki tun da itama ta saki a cewar Munnira wai da ta ga uwar bari ba, domin abin mamako har su Anty Bahijja yanzu Rabi'atu na zuwa gidajensu lafiya lau kamar ba su ne masu taya Gimbiya a dawa ba.

Da ta dawo daga maiduguri tazo da tsaraba ba wamda ba ta ba shi ba, ni kaina turaren wuta har ina kyautar shi.Yarinyar an yi mata huɗuban kyauta yadda za ta siye kowa to haka take yi ko Gwammaja za mu je ba za ta zuwa hannu rabbana sai ta riƙe ma su Nene wani abun. Cikin lokaci kaɗan Rabi'atu ta yi farimjini a dangin Yallaɓai wai har Anty Bahijja wata rana a ɗakin Nene mun je gaisheta ni da Gimbiya da yara ta zauna tana yabon Rabi'atu tana faɗin yarinyar akwai hankali sai daga baya ta yi ma Tafida uziri shi ya ga abin da ya gani. Har Nene yabon ta take yi in ta zo gida nan ta yi wannan ta yi wannan har kunshin su na yan maiduguri take zuwa na musamman ta ƙun sa ma Nene a kafa da hannuwana duk wani abinci da ta san Nene na so in za mu je za ts yi ta je mata da shi, wani abun ma ni ke faɗa mata. Mimisco da man ba ruwanta ko ita tafaɗa ta ce Yarinyar nan tana da wayau ta san dubarun zaman duniya.
Kuma ita ba ta ware kowa ba, kowa na ta ne, har su Suwaiba haka take girmama su shi ys sa cikin lokaci kalilan kowa ya san Rabi'atu har mazan fa in suka zo gidan haka za ta yi ta musu rawan jiki. Yallaɓai ko sai jin daɗi yake yi yana fahari Gimbiya ko sai kuka da nadama ba ta da yadda za ta yi ƙaramar yarinya ta zo ta sha gabanta.
Chapter 90 · 0% Book details