Sashe 66
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tsume na kalle shi kafin na ce" ai ka gama nuna mini isata tun da jiya ka ce na bar maka gida.'
Sai kawai ya riƙo hannuna duka buyin cikin na shi ya matse yan faɗin" Na rantse da wanda raina ke hannun shi. Lokacin da kika ce in na ce ki tafi za ki tafi na faɗa ne domin na ga zaki iya tafiya ki bar ni Sadiya? Sai na ga wai kin tafi? Lokacin da kika fita wallahi ji na yi kaina ya yi wani girimgirim Sadiya na shiga tashin hankali. Me ya sa za ki yi mini irin wannan gatsen fisabillahi"?
"Gatsen me? Kai ka ce na tafi ba za ka hana ni ba."
"Na gwada ne, na gwada ki na É—auka kema a wasa kika faÉ—a "
Kallon sa na yi ina wata dariya kafin na ce" Wasa? Ni ka ga wasa a magana ne."
"Wallahi ban gani ba. Kin ba ni tabbaci jiya. Ni dai kar ki ƙara yi mini irin haka bana so. Sai ki saka ai zuciyata ta buga."
Na buɗe baki zan yi magana ya haɗe bakin mu waje ɗaya yana tallafo kaina na yi masa tsaye ƙiƙam shi ya sa sumbatar ba ta yi armashi ba.
"Ki tallafe ni ma Sadiya ta."
Ya faÉ—a cikin karyewan sauti a yanayin shi kaÉ—ai da na kalla na san tallafan yake so.
"Me zan maka? Yara na falo fa?
Ƙamƙameni ya yi yana faɗin" Na kulle ɗakin ba za su shigo ba "
Ganin ina kallon shi ya sa kamar zai yi kuka ya marairaice mini yana faÉ—in" Don Allah I need you sosai."
Sai na kasa musa massa ya ja na ya yi zuwa kan gado yana mai ƙamkame hannuwana. Duk yadda na so na basar da shi na kasa Yusuf ne fa? Yusuf ɗin da na sani tun yana matashin sa. Sai kawai nima na tallabe shi, na saki jiki na ba shi abin da yake so.
Bayam mun natsa tun kafin mu kai ga wanka ina saman ƙirjinsa ya rumgumeni yana faɗin" Ki yi haƙurin kin ji ko? Ke mai hakuri ce ki ƙara akan na baya. Mimisco ta kira ni , Suwaiba ma duk sun sake yi mini bayani na gamsu. Itama Daughter zan yi mata faɗa kowa ya yi hakuri domin a zauna lafiya kin ji"
Na yi kamar ban ji ba sai da ya ƙara faɗn" Kin ji ko?
"Na ji."
"Ba ki yafe mini ba ko?
"Uhm"
Sai ya sumbaci goshina kafin ya ce.
" Ina kaunar ki."
"Ina sonka Yusuf É—ina."
Na faɗa ina sake rumgumoshi kamar na saka shi a aljanma haka ya ƙamƙameni yana faɗin
"Na gode Abar ƙaunata Ubangiji ya bar mu tare har mutuwa. Mutuwan ma ta ɗauke mu rana ɗaya"
Ina mirmishi na amsa da Amin.
Mun so mu shagala sai muka ji kukan Yumna a kofar É—aki tana kiran sunana.
Uma
"Uma.
Ni da Yallaɓai muka kalli juna muka kwashe da dariyan nishaɗi.
*Janafty**TKGB3016*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX
Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732
Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰
Shike nan faɗan mu ya ƙare ni da Yallaɓai amma lokaci bayan lokacin in muna zaune da ya yi magana zan kalle shi na ce" Ni ai Yallaɓai ka ga ƙarar mini da ruwan kaina. Ni da ka kalla ido cikin ido ka ce mini ina da mugun nufi akan matarka. Wallahi na kasa mantawa da wannan maganar"
In na faÉ—i haka sai ya marairaice yana lallashina shi a dole sai na manta duk kalaman da ya yi amfani da su a kaina.
"Me ya sa ba ki mantuwa ne Sadiya? Maganganun da na faɗa cikin fushi kema kin san ba a son raina ba ne. In ma na ce kina da mugun nufi ai kaina na yi mawa. Tun da tsawon shekarun da muke tare da ke ban amfana da komai ba sai alheri. Ki yi haƙuri don Allah ki daina dawo da maganar da ta wuce."
In ya faÉ—i haka sai na tura masa baki na ce" Uhm, ai ka san da haka ka manta ka yi ta manganganu."
"Ki yi mini afuwa ki yafe mini. Halin É—an adam ne na ajizanci."
 Haka ya kan faɗi in na ta da maganar kuma ba wai ban yafe ba ne na yafe amma na kasa mantawa in na ga yana yi mini rawam ƙafa sai na kalle shi na tuna masa maganar. Tun yana lallashi da sake ban hakuri watarana ma shuru yake yi mini amma ya kan ce Allah na sama yana gani kuskure ne ya yi kuma ba wanda ya wuce ya yi kuskure.
Har cewa ya yi sharrin sheÉ—an ne ranar ina ta tsintsira dariya shi kuma sai ya yi fuska yana hararata.
 Kwana biyu kamar na manta da maganar kawai ranar yana gidana da daddare muna falon muna kallo, Yumna ta yi barci tana ɗakin su Baby, sai za mu kwanta zan je na ɗaukota.
Wani American film muke kallo daman sune fina finan Yallaɓai ni kwata kwata ba sa burgeni sabo da shi ne ma na ke kallo, in ya ga na yi shuru sai ya yi ta mini bayani iyakata Umh da Hmm to ni bai san ba na son wannan bayanin ba, da zai ƙyale ni da na ji daɗi amma ba zai gane ba ni kuma ba na son na kushe ƙokarinsa. Yana cikin ba ni labarin film din ne ya gangaro kan karatu shi ne ma yake faɗa mini ya nemi gurbin PHD a Universty of Ibadan har ya samu.
Baki na buɗe kafin na kalle shi ina faɗin" Lalle Yallaɓai can Ibadan ɗin za ka koma?
"A'a ai online ne karatun sai in za a yi jarabawa zan je."
"Allah ya ba da sa'a."
Ya amsa da Amin Amin.
"Saura ni Yallaɓai maganar komawata master"
"Ina za ki je da Yumna? Ki bari ki yayeta sai ki koma."
Na kalli Yallabai shima ya kalleni, ai yadda ya ga ina kallon shi ne ya sa ya yi dariya kafin ya ce" Wallahi da gaske na ke yi. Zan hana ki komawa makaranta ne? Ko Daughter na faÉ—a mata in har za ta koma ni ba ni da damuwa."
Shuru kawai na yi masa na ma kasa mgana ina zencen makarantana yana kawo mini zencen wata matar shi, tsaki na so na yi sai na fasa kar ya ce na raina shi yana magana ina yi masa tsaki.
"Kina yayeta in sha Allahu sai ki koma. In kuma lokacin na sake yin ajiya shike nan sai ki jira ki sake haihu ki yaye sai ki koma."
Ai ban san na kai ma kafaÉ—an Yallabai duka ba ya kauce yana dariya.
"Me na faÉ—a? Ba ki son haihuwan ne yanzu?
"Ban sani ba."
Na faÉ—a ina tsumewa,
Rumgumoni ya yi yana faÉ—in"Sorry tsokanarki fa nake yi, ke ba ki san wasa ba?
"Ni ka ƙyale ni, ni ai na gama haihuwa da kai, ni da ka ce ina da mugun nufi a raina game da kai da matarka."
Na faÉ—a ina kallon shi, da sauri ya sake ni, ni na faÉ—a ne a wasa amma sai na ga ya wani daure fuska.
"Yi haÆ™.."
"Sadiya."
Ya katse ni da kiran sunana a fusace kafin na amsa ya nuna mini yatsa yana faɗin" Ba na ce ki bar tado da wannan mganar ba? Me ya sa ba kya jin magana ne, ko so kike yi ki ɓata mini rai hankalin ki ya kwanta ko? To shike nan kin ɓata mini rai kin ji daɗi."
Ya faÉ—a yana ture hannuna da na É—ora a kan cinyarsa. Ya mike na yi saurin kama hannun shi guda É—aya.
"Sorry"
Na faɗa ina leƙen fuskarsa, tun da ya kauda kai ne ya ki dariya sai na jawo shi ya faɗo gefena na sumbaci ƙuncinsa ina ƙara faɗin" Am sorry Yallaɓai na."
Lumshe ido ya yi ya buÉ—e kafin ya kalleni har muryan shi ta sauya."
"Me ya sa kike haka ne Sadiya?
"Ba zan ƙara ba"
"Shike nan ni ba zan yi kuskure kuma na zo na gyara daga baya ba? Na ba ki hakuri kin ce kin hakura to dawo da maganar kuma duk na mene ne? Ni fa mijinki ne, ke matata ce da soyayya ce ta kawo mu a wannan karnin, kina yi mini laufuka, kafin ma ki roƙe ni nake yafe miki saboda ba na son mala'iku su yi fushi da ke. Amma ke me ya sa in saɓani ya shiga tsakaninmu magana kaɗan bisa kuskure sai ki ma yar da shi makami a kaina? Ko don kin ga ina lalacewa a kanki da ban baki shi ya sa kike yi mini yanga?
Sai na kasa mgana saboda maganganun shi sun sanyaya mini jiki.
"Ka yi haƙuri wasa nake yi."
"Wannan maganar ba abar wasa ba ce. Ki bari kar ki ƙara ta yar da ita raina ba ya so. In kika ƙara zan kai karan ki wajen Alhajinmu."
Da sauri na kalle shi gira ya É—aga mini kafin ya ce" Da gaske na ke yi. Kin fara kular da ni da mganganun ki."
"Yi haƙuri ni dai. So kake yi ka sa Alhajinmu ya daina misali da mu.?
"Tun yaushe? Ai kin gama karya mini wannan record ɗin a gaban Alhaji. Fisabillahi abin da kika yi ba ki kyauta mini ba."
Na tura baki kafin na ce" To ba kai ka ja ba. Cewa ka yi na fita ba za ka hana ni ba."
"Kuma kika juya kika tafin ko kunya?