← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 103

Sashe 28

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai sai na yi jagale ina kallon Yallaɓai har wani dariyan nishaɗi yake yi.

"Yaushe ne bikin?

"Ban sani ba."

Na faɗa ina tsumewa, sai ya sake kallona yana mini dariya. Haɗe rai na yi ina kauda kai kafin na ce" Yallaɓai ko kai ma kana shirin yo ta ukun ne?
Sai ya kalleni kafin ya ce" To in Allah ya kaddara min zan ce ba na so ne?
Har sai da na buɗe baki saboda mamakin sa. Ni fa daman tuni na sha jinin jikina Yallaɓai zai iya ƙara aure in ma bai cike ƙofa ba.

"Kishi kike yi? Ba ki so na ƙara aure?

Tsaki na so na ja amma sai na yi shi a ƙasan raina.

"Ai ni ka gama mini kishiya Yallaɓai. Duk wacce za ta zo daga baya ba za ta ɗaga mini hankali ba."

"Ki ce wallahi."

Ya faÉ—a ya na mini dariya sai na ga ya mai da ni kamar wata shashasha. Hararan sa na yi, ban sake mgana ba.

"Ki rantse in yanzu na ce zan ƙara aure ba za ki ji komai a ranki ba?

"Ba zan ji ba. Ba kuma sai na rantse ba."

Kawai sai Yallaɓai ya ta so ya zo gabana ya durƙusa.

"Ki ce wallahi ba za ki yi kishi ba."

Sai kawai na kalle shi, lura na yi maganar ma nishaÉ—i take saka shi.

"Ba sai na rantse ba."

"To ƙarya ne. Ke ɗin ce ba za ki ki kishi ba?

Ya faÉ—a har ya na jan mini kumatu, na ture hannunshi kafin na ce" Me ya sa zan yi kishi! Na faÉ—a maka ni ka ga mini kishiya. Yanzu ai tsakanin ka da Gimbiyar ka ne."

"Saboda kina sona Sadiya. Shi ya sa za ki ji kishi na."

Kamar zan yi mgana sai na fasa ganin ko na tanka ba zai bar maganar ba zai ta tsokana ne yana mini dariya sai kawai na kauda kaina ban yi magana ba. Cikina ya shafa kafin ya ce.

"Bomboy fito ka ga mamanka sarkin kishi."

Da dai ya ga ban kula shi ba sai ya koma wajen zaman shi daman aiki ya ke yi a cikin system ɗin shi ya baro ya zo jin ta baki ganin kuma na ɗaure fuska ya sa dole ya ƙyaleni a cewar s na zama jagwam magana ma masifa ce da faɗa a wajena. Saboda ma yadda ya yi ban samu faɗa masa matsalan Ma'u ba na kama kaina sanin ina ma faɗa masa sai ya ce laifinta ne tun da Namiji ne, ba zai ga laifin ɗan'uwansa ba.

Mun yi waya da Ma'u kwana biyu ranar wata laraba Yallaɓai ma ba gidana yake ba, misalin tara na dare sai ga Ma'u a gidana afujajan cikin kuka sai da na ji gabaɗaya hankalina ya ɗaga, Yallaɓai ya fita kenan ya zo yi mana sallama ina tunanin ko gida bai kai ba lokacin da ta zo. Ɗaki na ja ta cikin tashin hankalin ina tambayan ta ko lafiya na girgiza da take faɗa mini Alhaji Mustapha ne ya ce ta bar masa gidansa ya sake ta saki ɗaya. Sannan lamarin bai tsaya a nan ba sai da ya haɗa mata da mari gabaɗaya farar fuskarta gefen hagu ya ta sa da shatin hannunsa.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un har da mari?

Na faÉ—a ina cikin matsanancin tashin hankali.
Ma'u ko kuka kawai take yi ta ma kasa mgana gabaɗaya sai na ji ƙafafuwana sun yi sanyi. Cikin jikina sai da na ji ya cire waje ɗaya ya motsa saboda tashin hankali.

"Me kika yi masa da zafi haka Ma'u?

Na faɗa ina mai dafa kafaɗanta cikin yanayina na damuwa. Da ƙyar na samu ta tsaigata da kukan nata ta yi mini bayani da cewa yau a gidanta ya ke yi jiya ma haka to a cewarta jiya sai wajen sha ɗaya ya shigo gidan kuma ya yi shigewarsa ɗakin sa ko da ta shiga yana ta waya haushi ya sa ta fita ta bar masa ɗakin shi ne yau da ya dawo ya shiga ɗakinta a kan gadon ta yana waya da budurwansa ita kuma ranta ya ɓaci ta fizge wayar ta haɗa da bango ta fashe shi ne ya kifa mata mari, ita kuma ranta ya ɓaci ta yi ta faɗin mganganu shima yana faɗa daga ƙarshe ya ce ta bar masa gida ya saketa saki ɗaya.

"Innalillahi Ma'u me ya aike ki? Me ya sa kika biye masa?

"Haba Sadiya a kan gadona na sunna zai kwanta yama yi mini waya da budurwa na yi magana yana ce mini ai ba budurwa ba ce matarsa ce tun da saura wata ɗaya auren su. Ni kuma raina ya ɓaci na fasa wayar shi ne ya mare ni. Sadiya bai ishe shi ba har sai da ya ce ya sake ni, ni fa wai Alhaji ya saka ni fa Ma'u"

Ta faɗa cikin gunjin kuka gabaɗaya sai na ji kaina ya sara. Ba ni a ka saka ba amma na ji sakin nan a raina. A raina ina tunanin yadda Alhaji Mustapa ke son Ma'u ya na ririta yau ita ce ya sake ta saboda wata mace. Macen ma da bai aure ta ba. Lalle duniya juyi juyi na gaba ya koma baya. Lallashinta nake yi amma ni kaina na rasa kalaman bakina, lamarin ya dake ni, na ji abun a cikin raina na rasa yadda zan yi da Ma'u kuka kawai take lamarin akwai cin rai da baƙin ciki namiji ya sake ka saboda wata mace macen ma ba ta ma shigo gidan ba, to in ta shigo kenan sai abin da ya yi gaba.

Ni kaina kamar in yi kuka idanuwana har sun kaɗa hawaye sun tarun mini a ƙwarmin idanuwana, abin da Alhaji Mustapha ya yi zalinci ne kuma rashin adalci ne a kan gadon aurenta? Tsakani ga Allah ya kyauta kenan, sai na fahimci so kawai yake yi daman ya ga yadda Ma'un za ta yi ne. Duk yadda na ke cewa ta yi hakuri sai na ji hakan da ta yi ta ni a wajena dai-dai ta yi ta kuma san mutumcinta amma marin ne da ta bari a ka yi shi ne kuskurenta sannan me ya sa ta fasa ma sa waya? Da da ta yi masa magana bai ji ba sai ta bar masa ɗakin duk tsiya dai ba kwana zai yi ai ya na wayar ba. Kai gabaɗaya na girgiza da lamarin nan jikina ya yi sanyi matuƙa har na gaza wajen lallashin Ma'u.

Na bar Ma'u a ciki na fito falo Baby ta yi barci Jidda ce kaɗai ba ta yi barci ba. Amma na kora ta ɗaki daman tana falon su tana karatu ne. Jidda fa ba ta yarda ta yi zaman gida a banza ba ko da yaushe cikin duba littafanta na makaranta take yi. Na zauna na rasa mafita wa zan kira a daran nan? Har na yi tunanin kiran Ya Aina sai na fasa in na yi tunanin Ɗorayi sai na ji gwiwata ta yi sanyi. Duk wanda zan kira yanzu wataƙila ma sun kai ga kwanciya kar na ɗaga musu hankali, Yallaɓai na ji shawaran na kira shi ya kwanta mini a zuciyata har na ciro wayar a chaji zan kira shi sai na fasa tuna yana gidan Gimbiya bai da ce na kira shi ba, ko ba domin komai ba akwai sirrin da ba na so ta ji, shawaran na tsayar ni da zuciyata a kan da safe sai na kira shi, da haka na koma ciki na samu Ma'u har lokacin na dirjan kuka nan fa na zauna ina ta ba ta haƙuri na san lamarin akwai ciwo amma ta yi hakuri zuwa da safe sai mu ga yadda za mu yi ta koma gidan mijinta.

"Ba zan koma ba Sadiya. Allah na gama zama da shi tun da har ni zai wulaƙanta a kan wata macen da bai aura ba."

"A'a Ma'u ba za a yi haka ba. Za ki koma gidan ki. In ba ki koma ba ta vi riba kenan kin bari wata macen da ba ta ma shigo ba ta kore ki daga gidan mijin ki da Æ´aÆ´anki."
Na gama faÉ—a ina bubbuga bayanta alamun lallashi.

"Duk ma abin da ya faru ai shi ya so haka Sadiya. Tun da ya ɗauko maganar auren nan ba irin cin kashin da Alhaji bai yi mini ina ta kauda kai ba saboda kin ce na yi haƙuri amma yau ya kureni har da mari fa? Sannan ya ce mini ya sake ni na bar masa gida. Ni Ma'u ni ce wai namiji ya sake ni kuma ya yi mini koran wulaƙanci?

Sai ta sake fashewa da kuka tabbas an yi mata tozarci duk da dai shima ina tunanin cikin ɓacin rai ya yi saki amma dai abin da ya yi bai kyautu ba, a yadda na ke jin zuciyata in ni ce ka yi ma wannan tozarci wallahi ba ma zan tsaya a kusa ba tafiya zan yi in da sai ka fara kuka kafin na dawo. Ni a tunanina ko na ce a hange na saki shi ne ƙarshen tozarcin da namiji zai yi ma mace saboda zai ƙara aure.

Amma ba zan ce Ma'u kar ta koma gidan ta ba, sulhu a ke nema, gidan ta daban nawa gidan dabam haka zalika, zuciyarmu ba iri ɗaya ba ne amma ni kam ba zan zauna ka mare ni ka mari banza ba, duk da haka tun da ta zo wajena da kukanta sai na tabbatar da an ƙwatar mata yancin ta. Tuni Alhajin ya zube min a idona ina ganinsa da ɗan kima a baya amma a daran na ji gabaɗaya na daina mutumtata shi.
Chapter 28 · 0% Book details