Sashe 30
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har Ma'u sai da ta yi dariya shi ko Yallaɓai kallona kawai ya ke yi yaa girgiza kai ganin yadda na haƙiƙance.
"To ni dai ki yi haƙuri kar mu je sulhu ki ɓata ma lamarin."
Na harari Yallaɓai ina faɗin" In dai har ina wajen sai na yi magana in kuma ba ka son hakan ta faru sai dai ka sauke ni na koma gida tun da ba ka son na faɗi gaskiya."
Na faɗa ina murguɗa masa baki ai sai ya yi shuru bai ƙara mgana ba, ko da muka isa gidan Alhajin na Ma'u bai iso ba sai da muka shiga muka jira shi.
Lokacin da ya zo har ya yi wanka ya ba za shadda na maiƙo har da babban riga a raina na ce kuɗi masu gidan rana duk su suke saka shi wani jin kai da ganin zai iya yin komai. Da ƙyar na gaishe shi saboda ina jin haushin shi a nan falon Ma'u muka zauna shi Yallaɓai ya fara ba ma dama ya maimaita magana sai kame kame yake yi, wai ta raina shi tun da ya ce zai ƙara aure taƙi kwantar da hankalinta ta sauya ta na abubuwa waɗanda ba halinta ba har ya na cewa wai haƙuri ya ke yi da ita sai jiya ta ƙure shi, shi kuma ran shi ya ɓaci har ya mare ta kuma ya furta sakin amma a jiyan bayan ta fita har bayan ta ya bi bai ganta ba kuma a jiyan ya janye sakin ya mai da ɗakin ta
Kallonsa nake yi a ƙasa ƙasa ina taɓe baki, ita ma Ma'u ta faɗi na ta a zencen gaskiya duka laifin shi ne. Duk shi ya rikita Ma'u ta koma haka a zaman nan ya ya bi Hajiya Zainab ban san sau adadin nawa ba ne, yana alfahari da cewa ita ba ruwanta ba ta ɗaga masa hankali lokacin da zai auri Ma'u ba yanzu ma ba ta ɗaga masa ba, sai yanzu ne ita za ta ɗaga masa hankali. Ya yi ta maganganu Yallaɓai ya ba ni haushi bai wani nuna masa kuskurensa ba yana wani lallaɓa sa, ni yadda ya nuna mini a gida ban ɗauka zai yi masa wannan lakwa lakwan ba. Daga ƙarshe an samu masalaha ya ba ta haƙuri itama ta bashi, kuma ya yi alƙwarin ba zai sake yin waya a gidanta ba in ma zai yi to ya kauce ma jin ta da ganinta. Ni ko ganin ba a yi maganar mari ba na gyara zama da cikina tulale a gaba na ce.
"To marin da ka yi mata fa? Tsakani ga Allah ba ka kyauta me ya sa za ka mare ta a kan wata?
Na faɗa ina kauda kaina cikin jin hauahi. Yallaɓai na yi mini abin da ba na so mutumin nan ya wani tattare wai an gama mgana ina dawo da su baya.
"To ka gama mgana ba ka yi maganar mari ba?
Na faÉ—a ina kure sa da ido, kawai ya wani bi ya tattare ni ai gwara a nuna masa bai mari banza ba.
"Ahto ka sani cewa Ma'u tana da gata duk abin da zai shiga tsakanin ku kar ka sake kai hannunka jikinta. In kuma ka sake to za mu kai mganar gaba, tun da Alhajin mu mata ya ba ka ba jaka ba"
Yadda na fiffitike ne ya sa har shi Alhaji Mustapha sai da ya yi dariya.
"Alhaji ka rabu da ita. Kasan masu ciki suna da saurin harzuƙa."
Na ma kasa mgana saboda Yallaɓai ya kai ni bango.
"Haba ba komai gaskiya ta faÉ—a na yi nadama kuma ni da ita zan rarrasheta. A yi mini afuwa Ya Sadiya."
Ya ce mini yana kallona Yallaɓai ma yana dariya dukkansu a ɗage nake kallon su a cikin zuciyata na ce ai duk kanwar ja ce.
"Yau na sake yadda da maganan nan ta hausawa da suke cewa jini jini ne. Ga shi yau Sadiya na mini faɗa saboda na taɓa mata Ma'u."
Sai da ya yi maganar sai na ji kunya na tashi ina mirmishi na ja Ma'u muka shiga ciki muka bar su nan a falo.
A ciki ba shawaran da ban ba ma Ma'u ba, ganin tana cikin damuwa ya sa na ce ta je ko Kura wajen Baaba ta bar Kano za ta samu natsuwa na kwana biyu sai ta dawo.
"Ina zan je Sadiya? Baaba fa cikin kishiyoyi take ba na so na je na bar mata abin faÉ—e"
"Ai ba dawo mata kika yi ba. Zuwa za ki yi da niyar za ki yi sati É—aya daga nan in kika huta zuciyarki ta yi sanyi sai ki dawo ba tare da ita ko ita Baaban ta san wani abu ya faru ba."
Sai ta kalleni kafin ta jinjina kai ni kuma sai na ƙara da cewa" Saboda zuciyarki ta yi sanyi. Kuma Baaba uwa ce in kina ganinta hankalin ki zai kwanta ga su Zainab za ki samu yar natsuwa. In ma za ki dawo sai ku dawo tare saboda ta ɗebe miki kewa. Yara kuma kar ki yi mgana lokacin da ya ga dama ya dawo da su duk ɗaya ne da can da nan ɗin. Kar ki sake ki sake yi masa mgana kin ji ko?
Sai ta gyaɗa min kai alamun ta ji, hannuna ta riƙe tana faɗin" Na gode Sadiya. Allah ya bar ki da Yallaɓai har abada ya ba ku zaman lafiya."
Na amsa da amin amin nima ina mata ƙwatanƙwacin addu'ar da ta yi mini.
Ba mu baro gidan ba sai da muka sulhuta komai sai gashi tare suka rakomu har haraban gida muna fita bayan mun ɗau hanya Yallaɓai ya kalleni yana faɗin.
"Kin ga ni ko? Shi ya sa na ce miki kar ki zaƙe mata da miji sai Allah."
"Uhm"
Kawai na ce ina kallon Yallaɓai da na so kar na yi magana amma na ga dai ba zan iya haƙuri ba.
"Yallaɓai ni dai ka daina mini irin haka. Kawai ina so na ƙwatar ma y'ar uwata yancin ta kana dakatar da ni"
Ya kalleni ya sake kallona kafin ya ce" Me na yi kuma? Daga mgana. To ai na bar miki kin karɓan mata Umma Sadiya"
Ya faɗa yana mini dariya na yi kamar na kai masa duka saboda haushi amma ban yi ba saboda dai ya wuce duka in dai a wajena ne. Yallaɓai ai sha kumdum ne maƙura ne.
Muna hanya wayar sa na tsakiyar mu Gimbiya na ta kiran shi ya É—auka ban ji dai me ta ce ba amma na ji shi ya na ce mata gashi nan zuwa. Ina zaune a gefe ko kala ban ce ba, ita wai nan ya fita da safe ranar girkinta shi ne take ta jaraban kiran shi.
Kafin mu isa gida na sake masa maganar koyon mota kawai sai Yallaɓai ya ce" Ke da wannan abin a gaban ki ne za ki je koyon mota? Kya bari dai ki haihu."
"Za ka koya mini in na haihun! In ba za ka koya mini ba na nemo ko Adnan ko Musbahu"
Sai ya fara dariya kafin ya ce" Ba za a yi haka ba Uwargida sarautar mata. Ke ce Alhaji Alhaji ya zama ke. Dole na ijiye duka harkokina na cika umarnnin ki."
Ko gatse dai ya yi na biye mishi na ce ƙwarai kuwa.
Yana kawo ni gida ko shiga bai yi ba Amarya na ta kira kai Gimbiya ba ta da haƙuri a rayuwarta ni dai na sauka na shige gida shi kuma ya wuce ban san yadda suka ƙare ba domin ni ban sake ganin shi ba sai washegari da yamma da zai dawo gidana.
Labarin abin da ya faru da Ma'u da mijinta daga ni sai Yallaɓai ko su Ya Aina ban taɓa faɗa mata ba duk ko yadda muke da ita. Na aminta da wani abu ɗaya ka riƙe sirrin wanda ya aminta dakai. Ba daɗi ta ji wannan mganar a bakin su sai ta ji ta raina ni, yadda nima ban faɗa ba itama kuma ba ta fidda mganar ba. Haba ai ba abin faɗe ba ne tun da ba abin daɗi ba ne muka rufe maganar a tsakanin mu tun da dai an samu sulhu. Kuma ko sati ba a yi ba mun haɗu a gida mun je duba Gwaggo da take zazzaɓi har ƙarin ruwa a ka yi mata a gida. Ta ga har mun zo mun taru gabaɗaya mun kuma rabu ba ta ji na yi maganar ba tana komawa gida sai da ta kira ni tana mini godiya har tana cewa na nuna mata na fita. Da ita ne ko domin a yi mini dariya za ta faɗa amma ni na nuna mata na yi ma zumumci kara kamar Yadda Alhajinmu ya roƙe ni.
"Ai ba mganar daÉ—i ba ne Ma'u. Sirrin ki kuma ai sirrina ne in na je na faÉ—a to ni za a yi ma dariya."
Ko Ya Aina sai da ta yi mini mgana. Ta ga ni da Ma'u gwanin sha'awa har Rahila ma sai da ta yi magana na yi dariya kawai na ce duniyar ma nawa take? Ya Aina ta ce haka ne kuma na burgeta. Rahila kuma har tana mini shaƙiyancin da cewa ko na kusa mutuwa ne na zama saliha, na ce mata ai ba yanzu zan mutu sai ta rigani mutuwa muna ta dariya ni da ita. Ba su san irin masifan da Yallaɓai da su Jidda ke karɓa ba, sun ga masifa da cikin nan kala kala.