← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 103

Sashe 45

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar wata  lahadi ni kaɗai na fito, tun da motar yara saboda ina amfani da ita ya sa tun ranar Jumma'a in Salisu ya ɗauko su daga makaranta sai ya ba ni key sai kuma Monday zai dawo ya karɓa. To in dai Yallaɓai ba gidana yake ba kafin ya ƙariso in na gama ayyuka gida zan ɗauko Yumna mu fita a motar ina ɗan zagaya anguwa daga can sama zuwa kasa saboda dai hannuna ya ƙarawa faɗawa. To ranar ma ni kaɗai na fita kuma a gida na bar wayata sai da ina kan hanyar dawowa na haɗu da Yallaɓai a kasa yana tahowa lokaci ɗaya yana waya sai magana yake yi yana ɗaga hannu bai ma ganni ba ni ce na hango shi yana sanye da jallabiya da dogon baƙin wando. Jallabiyan mai kalan ruwan kasa ne har da wata hula ya saka rabin kai na rasa a ina Yallaɓai ya samo wannan hulan tun kwanakin nan na ga yana saka ta lokaci bayan lokaci.

Daga nesa na ke kallon shi, tun da na É—an rage gudu. Yumna na kalla daga kwance a kan kujeran mai zaman banza. Sai na yi mirmishi kafin na ce" Yunma ga baban ki can"
Na faɗa ina mai ƙara kallon shi ta cikin gilashin mota tumbin da ya fara tarawa yake shafawa ya na faman magana a waya lura da yi bai ganni ba, kuma ni ya fito nema tun da ya je gidan ba na nan ya san na fito ne.

Hon na yi masa lokacin da na kawo kusa da shi, sai da ya juyo sannan na É—aga masa hannu ina dariya. Sai ya rike baki yana kallona kafin ya yanke wayar. Tsaya wa na yi lokaci É—aya ina sauke gilashin gefen da Yumna ke kwance.

"Hy É—an saurayi ji mana "

Na faɗa ina kashe masa ido ɗaya. Sanye na ke da wando baki plazo da riga ƙarama amma na saka after dress a saman kayana na saka brieziya hijab na Baby ne ma na maƙalashi da zan fito. Yumna ma ta sha gayu abin ta sai tashin ƙamshi take yi.

"Eye Yan matana irin wannan cakarewa haka?

Ya faÉ—a yana yi mini mirmishi, lokaci É—aya yana rike hannuwan Yumna itama ta rike shi gam ganin shi ya sa har ta fara wuntsila kafa tana masa gaurancin su na yara. Wai ita nan ta san me yi mata wasa haka take yi musu ita da Baby ta riga ta gane su in dai wajen yi mata wasa ne.

"Ya son ranka ÆŠan saurayi."

"Raina fesa. Da kyau Hajiya ta."

Ya faÉ—a yana nuna mini babban yatsa alamun jinjina.

"Shigo na rage maka hanya."

Na faÉ—a ina masa dariya shima yana ta ya ni, buÉ—e masa motar na yi shi kuma ya shigo bayan ya É—auki Yunma a saman jikinsa sai da muka fara tafiya na ji yana yi ma Yunma cakulckuli tana ta dariyan su na ihu irin na yara sannan na kalle shi ina faÉ—in" Yunma har ta gane ka kai da Baby in dai wajen wasa ne, in ba kwa kusa ta yi mini zillo tana son wasa ni ko na ce ba zan iya ba yarinya ki ji babanki ya zo."

Yana dariya ya ce" Me ya sa ba za ki yi mata wasa ba?

"Ban iya ba"

"Kin iya. Ke dai ba ki san yi mata ne, Yumna Umman ki ta iya wasa ba ta son yi miki ne kawai saboda haka kisan zaman da za ki yi da ita yauwa."

Kamar ta na jin sa ta yi zuru tana kallon shi, ni da shi muka kwashe da dariya ganin yadda ta wani yi nakwa nakwa da fuska kamar za ta yi kuka.

"Kar ka haÉ—a ni da uwata."

"To ki riƙa yi mata wasa. Irin wannan"

Ya faɗa yana shilla ta sama ya kuma caɓeta sai ga ta, tana bangala masa dariya.

"Aikin kenan daman shi ya sa in ta ganka ta yi ta zillo duk ka koya mata mugun wasa Yallaɓai."

"Dai dai kenan ma"

Muna tafe muna taɓa hira, ta kofar gida muka wuce mun kai farkon layi na sake kwana muka dawo sai a lokacin na lura ban ga motarsa ba.

"Ka shiga da motar ka cikin gida ne?

"A'a ba da ita na zo ba. Tun jiya tana gareji bakin mai ke zuba sai na kai ta aduba mini. Adaidaita na hayo."

Sai na gyaÉ—a kaina ban yi magana ba muna tafe sai ya kalleni kafin ya ce" Ehe Madam hannu fa ya faÉ—a."

Ina masa fari da ido na ce" To ya ka gani?
"Lafiya lau. Yanzu kam ba in da ba za iya tukamu ba."

"To Alhamdulillah saura motar kaina in sha Allahu."

"Akwai kuÉ—in siyan motan ne har yanzu?

Ya faɗa yana yi mini dariya ban ba shi amsa ba sai da muka isa gindin wata bishiya na yi parking na kashe motar sannan na kalle shi ina faɗin" Babu kam. Duk na ruguza jarina. Ina tunanin na riƙe wannan ko kai yara makaranta ne sai na rika kai su ina zuwa ina dawowa da su, tun da ina gida ba abin da na ke yi."

Bai yi magana ba amma dai ya kalleni, sai kuma ya ma yar da hankalin shi kan yi ma Yumna wasa.

"Ko Yallaɓai? Kafin na samu kudin siyan motar ko?

"A'a ba zai a yi haka ba"

"Me ya sa to?

Na tare shi ina mai kallon shi, sai ya dawo da hankalin shi kaina lokaci ɗaya yana faɗin" Saboda tuntuni motar nan tana hannun Salisu kuma kin ga ya tambayi izini tun a shekarun baya ya na ɗan haya da ita nan ƙauyakun kusa damu yana ɗan samun na cefane kawai sai rana tsaka na ce zan karɓa motata kin ga hakan ya dace?

Sai na yi shuru ina kallon shi ban yi magana ba amma dai gaskiya ya faɗa bai kyautu a karɓa ba.

"Shi ya sa ba zan karɓa ba. Kuma kin ga ya daɗe yana aiki tare da ni tun mashin ɗin sa har ya zo ya rasa mashin ɗin bayan na sauya mota sai na bar mishi wannan a hannun shi ba saboda kai su Jidda makaranta ba ne, saboda shima ya taimaki kan shi ne kin ga ne?

Sai na gyaÉ—a masa kai kafin na ce" Haka ne."

"To kin gani. Ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu abubuwa suna ƙara warware mini zan siya miki mota in sha Allahu."

Kallon sa na ke yi domin ni na san alƙwarin Yallaɓai haka ya yi mini na buɗe shago har yau bai iya cika alƙawarin da ya ɗaukar mini ba.

"Kin yi shuru?

Sai na sauke ajiyar zuciya kafin na ce" Uhm Allah Ya sa."

"Amin ko ba ki yarda da abin da na ce ba ne? Wallahi zan siya miki ba ni na ce ba."

Ƙureni da ido ya yi ganin ina kallon shi ban ce komai ba.

"Ki yi mini magana mana ba na son wannan shurun fa"

"Yallaɓai ni dai ka daina yi mini alƙwari in dai ka san ba za ka iya cika mini ba"

Sai ya zura mini ido kawai bai yi magana ba.

"Ka daina lasa mini zuma a baki kuma ka tafi da sauran zumarka ban ƙara ganin ta."

"Wani alƙawari na yi miki ban cika ba Sadiya?

Ya faɗa a muryansa a natse ba maaganar wasa nima ko na gyara zama ina faɗin" Suna da yawa amma babban ciki ne na buɗe mini shagon Saloon. Ka samu damarmar maki da yawa a baya Yallaɓai amma ba ka cika mini alƙawarin da ka yi mini ba, duk da ba kyauta za ka buɗe mini ba da kuɗaɗena a hannunka amma abu ya gagara ko da yaushe sai dai ka ce kai ka yi alƙawari za ka  buɗe mini amma shuru. Duba fa ka gani Gimbiya a bayana ta zo gashi yanzu har ta buɗe shago business ɗin ta na ta bunƙasa amma ni sai dai ka yi ta lasa mini zuma a baki. Ba domin na ɗan kama ma businness ɗin hijaban nan ba da har yau ina nan ina zaman jiran warrabuka."

Na gama faɗa a tsume, ban so na yi magana ba amma yau ne ya kai ni bango. Na gaji sai ya zauna ya yi ta cewa zai yi mini kaza zai yi mini kaza amma ya kusa cika alƙwari ko ɗaya da ya yi mini sai maganaa a fatar baki.
Shuru ya yi ya kasa mgana har yana dukar dakai.

"Ka yi haƙuri ban so na yi maganar nan ba. Ta kama ne."

"Kallon maƙaryaci ashe kike yi mini Sadiya ban sani ba?

Ya faÉ—a yana mai kallona.

"Ni dai ban ce ba."

"Haka ne mana. Kina mini kallon makaryaci sannan mara adalci ke ban buÉ—e miki shago ba amma na je na buÉ—e ma Daughter ko?

"Ni fa ba haka na ke nufi ba."

"Haka ne mana. Ga shi kin faɗa mini da ba ki fara ma sana'ar sai da hibajai ba da har yanzu kina nan kina zaman jiran warrabuka ko?
Ko ba haka kika ce ba?

Shuru kawai na yi ganin yana neman sauya mini mgana ta.

"Muje gida sai mu yi maganar a can"

Na faÉ—a ina kokarin ta da motar tsawa ya daka mini sai da Yumna ta firgirta ta fashe da kuka.

"Ba in da za mu je, anan kika fara ta kuma anan za mu ƙarƙare ta."

Ya faɗa da karfi har ya na buga kujeran mota ni gani na yi ma yana neman sakar mini da yarinya da ya sa da sauri na saka hannu na karɓeta ina rumgumeta ganin ta firgita tana ta kuka.
Rigata na É—aga ina zaro mata Mama saboda in ba shi na ba ta ba, ba za ta daina kuka ba.

Ina ba ta Nono Yallaɓai ya ta sani a cikin motar nan yana ta yi mini masifa saboda ba ya son gaskiya. Eh mana rashin gaskiya in ba haka ba ai bai cika alƙawarin ba. Kawai yana kunfar baki ba shi da abin faɗa ko da zai kare kan shi da shi.
Chapter 45 · 0% Book details