← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 103

Sashe 40

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya amsa mini har yana wani haɗe rai sai na kalle shi kafin na ce" To ai sai dai ka yi haƙuri zuwa anjuma ka ga na riga na yi wanka."
Amma Yallaɓai ya ce bai san wannan ba sai ma jikina da ya matso da ƙarfi ya ta da ni tsaye ya rumgumeni yana faɗin.
"Ke ce kin ƙara sugar. Wato ta bakin ki haihuwan Yumna na dabam ne."
Ya faɗa ya na shafa cikina, hannunsa na bige sai ya kai shi saman ƙirjina yana matsawa da ɗan ƙarfi har sai da na yi yar ƙara yadda na haɗe rai ne ya sa ya fara mini dariya yana faɗin" Ki gama shan kunun ki sai na ƙara horan ki kenan. Me ya sa kika yi wanka ni ban ba ki izini ba?

Kasa magana na yi, kuma abin da ya faɗa sai da ya cika shi. Lalata mini wanka ya yi kuma bayan mun gama ina shirin sauka daga gadon ya riƙo ni wai bai ba ni izini tashi ba haka nan na koma na kwanta ya cigaba da jagwalgwala ni son ran shi sai da ya nishaɗi don kansa ya ce mu je mu yi wanka sai tura mishi baki na ke yi amma ko a jikinsa. Ban samu lafiya ba sai da ya fita sallar azahar ma ta suɓuce masa sai dai ya yi ta a gidaa bayan mun karya a lokacin sannan ya yi mini sallama ya fita.

Yana fita nima bayan na yi sallar na koma barci. Daman Yumna tun da ta ji ruwan zafi take barci. Ba mu muka tashi ba sai gab da la'asar shima É—in kukan Yumna ne ya tashe ni. Sai da na ba ta Nono sannan na tashi na É—auro alwala na yi salla sanin Yumna ba za ta kwanta ita kaÉ—ai a É—aki ba ya sa na goyata sannan na shiga kitchen domin neman abin da zan dafa ma su Jidda kafin su dawo daga makaranta.
Da yake Yallaɓai ya yo mana cefane cikin satin nan sai kawai na yi mana cous-cous mai kayan lambu. Da yake ba shi da wahala nan da nan na kamalla shi. Ko da suka dawo ina falon su ina cin nawa Yunma na hannuna tana ƙiriniyar su na yara. Suna dawowa Baby ta fara damuƙarta daman in dai tana gida ba ni da haufin yar reno tun tana kuka in ta ɗauke ta har ta saba in ma ta ganta ta dinga kallonta alamun tana nuna mata sani. Sai da na karɓe ta sannan Baby ta samu daman cin abinci. Bayan sun gama na goya mata ita, Jidda kuma ta je ɗaureye musu kayan makaranta.

Ranar da wuri Yallaɓai ya dawo gidan ko kafin tara mun shige ciki ni da shi da Yumna Baby ta yi barci Jidda ce ke karatu tun da mun shiga sabuwar shekaran 2021 akawai jarabawowi a gabanta. Ni dai kwana biyun da Yallaɓai ya yi a gidana da wayyo Allah na ƙarishe shi duk cinyoyina ciwo suke yi da gaɓɓaina saboda bai sarara mini ba, in na yi ƙorafi sai ya ce wai ai ya yi ƙoƙari wajen kwana hamsin sai na ce ba yana da wata matar ba sai ya harare ni ya ce ita sunanta Saudatu ke kuma Sadiya kin ga kowacce na da nata tarim bambamcin da ya bambamta ta da ƴa'ruwata tun da na ji haka ban ƙara yi masa magana ba.

Da ba ya gidana barci na yi ta sha ina hutawa ina zan iya. Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya. Shekaran 2021 ta zo ma da Yallaɓai da babban buɗi na alheri domin ya dace da samun wani babban kwangilan gina jami'ar kuɗi a nan garin Abuja. Yadda Yallaɓai ke murna ne ya sa na san cewa ba ƙaramin alheri zai samu ba abin farincikin ma sun bashi 70% na kuɗin aikin shi satin kaf yini ya yi cikin farinciki shi ya sa ba tare da sanya ba ya saka Khalipa a makarantar su Jidda. Amma shi Gimbiya ke kai shi da kanta su Jidda kuma Salisu ne.
Samuwar kuɗin hannun shi ya sa ya tsayar da lokacin buɗe kamfanin shi ƙarshen watan Feb. Tun da ya ce yana tunanin kayan da ya yi oder su sauka a tsakiyar wata mai kamawa.

A cikin haka ne aka fara shagalin bikin mijin Ma'u. Mu ne gaba gaba masu dannen ƙirji, na ba ma Ma'u gudummuwa sosai a wajen auren nan, a ka yi taro lafiya aka tashi lafiya ba tare da na bari an ga gazawarta ba. Ta ji daɗi ta kirani tana ta yi mini godiya har shi Alhajin ya yi ma Yallaɓai maaganar daidaitarwar mu ba ƙaramin canji yake gani a tattare da Ma'u. Ni daman haƙuri na ce ta yi gashi da ta yi haƙurin har an yi auren komai ya wuce. Har Baaba da ke adawa da ni yanzu ta ɗan sakar mini,nima sama sama tunda daman can ni da ita jininmu bai haɗu ba.

Jidda ta sake sabunta rigister ɗin ta na Jamb. Da ƙyar da saka bakin Kawu Abba Yallaɓai ya bari ta cike ABU zaria a first chioce ɗin ta. Shi dai wai baya so ta yi nesa da gida ni kuma na ce ai duk in da take addu'armu na tare da ita kuma ai zaria gida ce. Hmm kawai ya ce shi fa daman ya amince ne domin an fi ƙarfin shi ba domin yana ra'ayin haka ba. Ita dai Jidda tun da ya amince sai murna ta ke yi sai bayan salla za su yi jamb ɗin da sun zana ta, za su fara rubuta jarabawar fita babban sakandiri. Shi ya sa ba ta zama yanzu ita ce jamb class da lesson har asabar da lahadi yanzu ba ta zama Jidda na ci gare ta kamar mahaifinta in suka saka kansu a abu agaba sai sun ga sun cin ma nasara.

Ranar kawai Yallaɓai  ya ce mu shirya da ni da yara gabaɗaya har da Gimbiya mu je mu ga ma'aikata sannan mu ƙarisa mu ga filin da ya siya tuntuni wanda zai gina ma gida da zai haɗe mu gabaɗaya. Ranar lahadi ne kuma ba a gidana yake ba yana gidan Gimbiya ne. Jidda ma ya hana ta zuwa lesson ɗin ta da ake yi musu a makaranta saboda fitan da za mu yi, mun cakaree gabaɗayan mu har Yumna na yi mata gayu, shi muka rika jira tun da yana can gidan ne sai ya kwaso su sai ya zo mu wuce ta gidana.

Sai da suka ɓata mana lokaci sannan suka zo. Gimbiya an ci gayu abaya ta saka ta yane mayafin a saman kanta ta saka wani takalmi mai rufi har da uban gilashi su Khalipa ma sun ci gayu cikin riga da wando yan kanti. Ni daman doguwar rigar atamfa na saka ɗinkin kaftan na saka mayafi kalan kayan sai na saka takalmina baki mai saukakken tudu. Jidda ma haka ita dai Baby pakistan ne riga da wando a jikinta da breziya Hijab. Tana kuma riƙe da Yumna ni ce ke ɗauke da jaka da na sako mata ruwa da ƙyallen goge tumbulunta tun da tumbuli take yi shi ya sa take yi kiba kamar ana hurata.

Mun gaisa sama sama da ta so ta shige gidan gaba ne sai kuma ta fasa ta shiga baya da yara. Ni ko ba ta san mota ba ta dame ni ba, mijin ma gabaɗaya na raba shi ballantana wata motar banza. Muna tafe ni da shi muna hira shi ne ma yake sako ta a cikin maganarmu shima ɗin a daƙune take amsa mishi ban san me aka yi mata ba, ko Yumna ba ta ɗauka ba nima ban tura mata ba. Na fahimci bata kaunar fita ta haɗamu ni da mijina ta aure mini shi, ni ban yi kishi ba sai ita? Mamaki
take ba ni in dai fita ta haɗamu gabaɗaya ta riƙa cin mgani kenan. Ni ba na ta ita in muka gaisa ban ƙara jan ta da magana sai dai in har ita ce ta sake yi minI magana. Ina da aji ba zan zauna ina bin kishiya ba. Har muka isa hira muke yi da Yallaɓai yana faɗa mini yanzu ƙasa za su fara amfani da shi sama sai zuwa gaba. Wancan kuma wajen tun da ya siye shi tuntuni yanzu yana matsayin mallakin shi ne. Zai ba da hayan saman ƙasan kuma yana tunanin abin da zai saka a wajen.

"Yallaɓai to ka buɗe shagon sai da kayan gine gine mana "

Yana tuki ne amma sai da ya juyo yana kallona.

"E mana. Na ga kai ma in ka buÉ—e amfaninka ne tun da in kwangila ta samu suma kayan ginin siyansu kake yi."

Sai ya jinjina kai alamun gamsuwa kafin ya É—an waiwaya baya yana faÉ—in" Ke fa Daughter ba ki ce komai ba?
"Me zan ce?
"Ke ma ki ba ni shawara. Kin ga Sadiya ta. Kusan komai da zan yi in na nemi shawaranta tana kawo mini shawarwari masu kyau kuma in na yi amfani da su ina ganin alfanu sosai."

"To ba gashi ta baka ba"

Ta faÉ—a har a muryanta haushin ta bai boyu ba.

"Duk da haka kema ina son jin na ki shawaran"

Shuru ta yi kamar ba za ta yi magana ba sai da ya sake yi mata magana sannan ta ce" Ni a ganina me zai hana ka buÉ—e shagon provision tun da wajen a bakin titi ne."
Jinjina kai ya yi kafin ya ce" Good. Ke ma kin kawo point amma na Sadiya ya fi muhummanci. Bari mu fara da na ta, daga baya in komai ya tafi daidai sai a buÉ—e shagon provision É—in"

"Ka san shawaran ta za ka É—auka me ya sa ka na ce sai na yi magana?

Ta faÉ—a a zafafe.

"Saboda kema kina da haƙƙi a kan haka."

"Uhm"
Chapter 40 · 0% Book details