← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 103

Sashe 53

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni ai ban ce komai ba na dai ce Jidda ƙoƙarina ta ɗauko. Shi ya sa duk abin da ta yi ma himma take samun nasara da taimakon Ubangiji."

Ya faÉ—a yana Æ´'ar dariya.

"Allah Ya ba mu sa'a."

Na faɗa kawai saboda ba na so maganar ta yi tsayi amma Yallaɓai bai so haka ba kawai sai ya kalleni yana sake faɗin" Amma kin ga Baby ina jin kanki ta ɗauko sam ba ta kai Jidda ƙoƙari"

"Au ni daƙikiya ce kake so ka ce ko Yallaɓai?

Na faɗa ina masa wani kallo sai ya fara dariya yana faɗin" Ni yaushe na ce miki daƙiƙiya?
Ban bari ya cigaba da magana ba na yi wucewata ina faɗin" Sai kuma ka yi. Na gode da cin mutumci Yallaɓai. Ka ji na ce Na gode."
Jin yadda na yi maganar ya san na yi fushi sai ya biyo ni ciki yana rage mini murya, da ƙyar na haƙura sai da ya yi mini rantsuwa da cewa da wasa yake yi sannan na aminta da shi har na saki fuska muka cigaba da hira. Daman da daddare ne ya zo yi mana sallama tun da gidan Gimbiya zai kwana yau da gobe.

Ranar jumma'a Jidda ta dawo, gidan Khaleesat na saka aka aika mini da saƙon hijabai ta taho mini da shi, ta dawo a jigace ta sha wuya motarsu ta yi ta lalacewa a hanya sai mangariba ta iso. Yallaɓai ya kirani ya fi sau biyar yana yi mini masifan ya zan haɗa yarinya da kaya na san ba ta taɓa tafiya waje mai nisa ba, ko da za ta tafin ma da kyar ya bari da ace baya da wani abin da zai yi shi zai kaita. Amma sai da ya kaita  tasha yana jadadda mata ta kula da kanta, kafin ta kai ko ban san sau nawa ya kira ta a waya ba, to yau ma za ta dawo ya yi ta kiranta daga baya sai ya daina samun ta a waya shi ne zai sauke faɗan shi a kaina, tun ballatana da Jiddan ba ta taso da wuri ba saboda jiran sakona. Ai ni sai shuru da ba da haƙuri tun da dai ba ni da gaskiya. Sai da ta shigo gidan nan na samu sauke numfashin salama na kira Yallaɓai na faɗa masa duk da haka bai fasa faɗin abin da ke ran shi ba.

"Sai yanzu ta iso? Sadiya ba ki kyauta mini ba, kawai ki haÉ—a yarinya da kaya ki wahalar da ita fisabillahi kin kyauta kenan?

"Na ce ka yi haƙuri Yallaɓai ganin za ta dawo ne ya sa na ce ta karɓa ta taho mini da shi."

"Ni dai ba na so. Kar ƙi kara yin haka. Ba ta fa taɓa tafiya ta yi ita kaɗai ba"

Mamakinsa ya kama ni, Jidda kamar wata ƙaramar yarinya ni dai shuru na yi har ya gama bambamin sa ya kashe wayar ban ƙara ce masa komai ba, tun da tun ɗazu nake ba shi haƙuri amma kamar ya haƙura sai kuma da ya ji ba ta dawo ba sai ya fara mini masifan wai ni na ja. Ni fa daman na sani Jidda a wajen Yallaɓai ta musamman ce, in dai lamarin da ya shafe ta ba ya zaune ba ya tsaye, ya yi ta wani kafa kafa da ita kamar wata ƙaramar yarinya. Ai ban ma ga kafa kafa ba sai da ya dawo gidan haka ya zaunar da ita yana tambayanta ta sha wahala? Ta gaji ne ba dai ta samu wata matsala ba ko?

Tana dariya tana faɗa masa ita lafiyanta ƙalau, ba ta samu wata matsala ba kawai lalacewar motar ne, har yana tattaɓa wuyanta, ya ji ko tana da zazzaɓi, ni dai ina gefe ina kallon ikon Allah na kasa mgana. Na ɗauka Yallaɓai ya gama faɗan shi amma ina yana ganin hilimin saƙon da Jidda ta taho da shi faɗan shi ya dawo farko wai da gangan na yi kamar Jidda ne zan saka ta ɗauko uban kaya haka? Wai har Yallaɓai na faɗin an ya ina da tausayi kuwa?

Baki na saki kafin na rufe ina faɗin" To wai duk wannan faɗan na mene kuma Yallaɓai? Ina ce ba ga Jiddan ta dawo ba? Kuma ita Jiddan yarinya ce kar ka manta she is 19yrs kuma jami'a za ta shiga so Jidda ba yarinya ba ce, ka ma daina jijiyan wuya ko Baby ta wuce yarinya ballantana Jidda."

Na faɗa cikin jin haushin sa, to ya dame ni magana ta ƙi ta ƙare kamar cin kwan makauniya, maimakon ya yi shuru sai ya ma ya harzuƙa ya fara faɗin duk haƙurin da na ba shi na ƙarya ne tun da ban yi nadaman abin da na yi ba ina cewa wai Jidda ba yarinya ba ce.

"Za ki haÉ—a da kanki ne? Kin ga ko har yanzu yarinya ce."

"Jaririya ce Nono take sha Yallaɓai"

Sai ya yi shuru bai ƙara mgana ba ni kuma a lokacin na hau sama na miƙe ina faɗin" Kayan fa ba akanta ta ɗauko su ba. Yadda kake wanman faɗan ko dakon su ta yi daga Zaria zuwa nan sai haka"
Ina gama faÉ—in haka na É—auki Yunma muka bar musu falon haba ba ta yuyuwa kamar wata Jiddan gwal ne, ai ganin yadda na yi cuÉ—uncuÉ—un da fuska na haÉ—e rai ya san halina shi ya sa sai ya bar maganar amma da ban yi masa haka ba abin mamaki ba har ya gama kwana biyun shi kullum sai ya ta da maganar ina dalili.

Waɗanan Hijabai ai ban siyar da su cikin daɗin rai ba domin na tuna da bambamin faɗan da Yallaɓai ya yi ta mini raina sai ya sosu, in ta yi ƙyafci ni kaɗai saboda takaici. Zan ga yadda zai yi in ta samu admission za ta tafi makaranta sai na ga ƙarewar so da ƙauna. Kuma ba daɗewa suka ba ta Admission, da kuma Course ɗin da ta zaba wato Phamarcy, nan da Yallaɓai ya fara yi mata shirin makaranta privision kamar za a buɗe shago komai Jidda ta ce tana so ya siya mata har da ma wanda ba ta ce ba, tare suka je kasuwan shi da Jiddan da Baby ni ina gida ko gayyata ta bai yi ba kuma na so ya ba ni ragama ni na samu riba a ciki amma Yallaɓai ya yi fuska ni kuma ban yi masa mgana ba saboda kar ya ranfo ni, na zura masa ido kawai ina ganin ikon Allah wajen uban da yar gabaɗaya.

Da yake sai January  sabuwar shekara za ta yi rigistration ta koma sannan su fara karatu. Shi ya sa shekaran na kamawa na 2022 ana buɗe portal ɗin biyan kuɗin makaranta ya ɗauke ta suka tafi. Ranar cikin ikon Allah zai je Kaduna sai ya biya ya sauke ta a cikin makaranta da in ta gama abin da za ta yi ta wuce gidan Uncle Hamza. To kwanan ta biyu tun da har hostel sai da ta tsaya ta yi clicking ta samu Queen Amina Room of 12 ta ce su huɗu ne a ɗakin ta samu loka da gadon ƙasa, a gida daman Babanta ya siya mata katifa mai kyau, ranar da Yallaɓai zai dawo ya biya ya ɗauko ta suka dawo tare bakin shi ya huta nima kunnuwana suka huta.
Washegari kuma ya saka Adnan ya rakata firstbank ta buÉ—e, banki saboda makaranta.

Jidda duk ta zagaya gidajen yan'uwan Babanta ta yi musu sallama. Mimisco ta ce na ba ta hijabai guda biyar za ta biya kuɗin. Su Anty Bahijja kuɗi duk suka ba ta, har Gwammaja ta je da Ɗorayi ta yi musu sallama su Ya Aina a waya na faɗa musu suka yi fatan Allah ya sa a fara cikin nasara. Ta je har gidan Gimbiya ta yi mata sallama sai ta ba ta takalmi cover shoe guda biyu sai abaya guda ɗaya da kayan kwalliya. Kawu kuma ya aiko mata da dankalin turawa da kwai da yawa, dankalin ma kaɗan na ɗibar mata kwan kuma Yallaɓai ya ce sai ta je can ta siya saboda zai jigata a hanya kafin su kai. Ranar lahadi 28january Jidda za ta tafi makaranta za ta bar mu da kewa.

Duk da Yallaɓai bai ce da ni za a je ba amma na yi shiri ni da Baby da Yumna na ce zamu raka Jidda har makaranta itama na ta murna ashe Yallabai ya shirya da wacce zai je, sai ana gobe tafiya ranar asabar kenan ya ga ina ta shiri, na yi mata dambun nama ita kuma ta yi ma kanta su Snacks cokes, donut, cincin cake kaɗan ta yi saboda lalacewa sai miya da ta yi mai naman rago, sai ƙuli da na siya mata mai yawa yaji kuma Munnira ta dako mata mai daɗi ya ji tafarnuwa, Hauwa ta aiko mata da garin rogo mai kyau, da kansu suka zo suka kawo mata tare da yi mata yan nasihohin ta yi abin da ya kaita ba ruwanta da rayuwar makaranta ta tuna da tarbiyan da iyayenta suka ba ta.

Sai bayan tafiyar su na zaunar da ita na yi mata nawa. Karatun Qur'ani salla da azkar kar ta yi wasa da su ta dake da karatu ban da shagala da ƙawayen banza duk abin da ya shige miki duhu ga gidan Uncle ɗin ki ne, in kina jin kewan gida ki je ki yi musu Weekend na yi mata fada sosai tana kuka ta ce in sha Allahu ba za ta saɓa magana ta ba. Ni daman ba na jin ta Jidda ba ta da rawan kai, da man dai Baby ce uwar rawan kai. Ina cikin yi mata nasihan sai ga Yallaɓai ya shigo jiya da yau duk a gidan Gimbiya yake. Ganin mu zaune a falo ga su Jidda duk a ƙasan cafet sun natsu ya sa ya ƙariso yana faɗin.

"Me ake tattaunawa na ga har Yumna ta yi ladabi"
Chapter 53 · 0% Book details