← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 103

Sashe 42

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tabbas. Yallaɓai mun rufe ƙofa. Gimbiya ce a madadin biyu nima a madadin biyu shike nan mun cike maka ƙofa."

Na ƙarishe faɗa ina dariya.

"Shi kenan ko."

Ta faÉ—a cikin jadadadawa.

"To ba ku isa ba."

Ya faÉ—a yana wani haÉ—e rai irin da gaske nake yi É—in.

"Mun isa har ma mun yi yawa."

"Haka kuka ce?

"E haka muka ce."

Ta mayar masa da martanin cikin nuna da gaske take yi.

"Ok we shall see."

"See me?ba abin da za mu gani sai alheri wallahi ko É—auko auro ka yi ni da Madam sai mun ruguza shi. Mu ai ka gama auro wata mace kuma a duniya tun da ka aure mu."

A yadda take magana kaɗai ya isa a fahimci da gaske take yi. Har suka sauke mu a gida ina jinjina zafin kishin Gimbiya. Wato wata rana in har Yallaɓai ya ɗauko auro akwai yaƙin duniya na uku ita da Yallaɓai kanbu! Da abin na kwana a zuciyata gari na wayewa na kira Munnira na tsegunta mata yadda muka kwashe da Gimbiya jiya. Matar nan da ta laulayo ashar sai da na ce.

" Ke Munnira ki ji tsoron Allah wannan ashar É—in fa?"

Na faɗa ina dariya saboda na ga ta  ma fini kambama lamarin.

"To ba dole na  danno ashar ba. Ba a aure ita aka auro ta! Ba a yin kishiya ke kika bari aka yo miki da ita? Ba na son iskancin banza."

Ina ƙyatata dariya na ce" Ita ai za ta zo a matsayin kishiyar wata amma ita ba za ta bari a kawo mata wata a matsayin kishiya ba."

Munnira ta ce" TaÉ—ijam! Tana da aiki ni tun da har aka yi miki da ita fata na yanzu itama ayo mata ta ji in da daÉ—i."

Ina dariya na ce" To waya sanin ko zai ƙara."
"To ke ba ki ga alamu ba?
"Ban gani ba amma in dai ana maganar za ki gan shi cikin nishaɗi ba ya ƙoran maganar gaskiya."
"An gama magana. Tafida in ya ga wata yar shila zai yi tunanin ƙara aure."
"Zai iya yuyuwa tun da ya iya yi mini kishiya itama ba abin mamaki ba ne don ya yo mata."

"Namijin kenen. Uhm Maza mutanen mu."
Muna ta dariya ni da ita, har ina tsokanarta in Nasir ya gano wata yar jan fata haka.
"Ta zo ai ba a kaina za ta zauna ba."
Na yi mamaki jin haka Munnira ta yi sanyi.
"Ke kuma yau? Kin saduda ne yanzu ta shigo."
"To na ga ko ka yi haukan ma in suka yi niyya sai sun yi."
Na kwashe da dariya ina faɗin" In dai ji maza kawai matar nan bana son sadudan ƙarya"

Itama dariyan take yi mun daɗe muna mgana kafin mu yi sallama. Da Yallaɓai ya dawo gidana sai da na yi masa taɗin da cewa" Kai Gimbiyar taka ba ta son kishiya. Sai ka shirya in dai za ka ƙara aure za ta yi maka daru."

"Za ma ta yi ta gama ne. Tun da har na iya yi miki kishiya ita nata mai sauƙi ne."
Amsar da ya ba ni kenan, sai na kalle shi kawai ina dariya. Ban sani ba amma haka kurun na ke ji a jikina watan wata rana Yallaɓai zai iya ƙara aure ko bai cike gurbin ba. Wata ƙila kuma ya yi gadon marigayi mahaifin su. Tun da jajirtattace ne, sannan yanzu ya samu buɗin da riƙe mata sama da biyu ba zai zama wahala a gare shi ba.

Maganar lunching ɗin kamfanin Yallaɓai ya ta so. Ya ce ya na so a yi komai a gama kafin azumi. Shi ya sa ya ke ta shirin sa muma muna taya shi. Sanin rana ce babba a gare shi, ya yi katin gayyata kuma ya gayyaci mutane sosai abokan karatun shi, abokan harkokin shi, ƴan uwan shi na nesa da na kusa. Ya gayyaci yan siyasa amma ba sosai ba, Kawu Abba da Tariq sun yi gayya suma daga bangaren su. Tun da shi Tariq a matsayin shi na lauyan kamfani shima ya gayyato ƴan uwan shi lauyoyi. Kaf ƴan uwan shi maza za su hallarta hatta Ya Usman da ke nesa. A hankali yake ta shirin sa mun yi shawara da shi, akan za a yi abincin na sadaka sannan zai ba da a yi masa saukan Qur'ani acan ma'aikatan kafin a fara amfani da shi ya ce mini To. Abincin da lunching kuma Mimisco ta ce za ta ɗauki nauyin komai da komai har da ruwan da za a sha da lemu a wajen.  Kayan da ya yi oder suka iso kamar su kujerun ofishoshi da I.C, cafet da sauran su a ƙarshen watan Febuary kayan suka sauka daman kuma ranar lunching goma ga watan March ne. Ranar lahadi za a fara taron goma na safe zuwa ƙarfe ɗaya na rana.

Ya ɗauki Nene da su Maman Farko ya kai su wajen sun gani sun yi murna da addu'o'i. Alhajinmu da Gwaggo da na je na faɗa musu sun kira shi sun yi masa fatan alheri yana ta jin daɗi. Shi dai ya ce walimarsa ta maza ne amma in za mu yi gayya a gida ƴan uwa a zo a yi murna bai hana ba, shi ya sa duk na faɗa ma yan gidanmu. Sai su Munnira sauran tawagan gidan su Yallaɓai yan bangaren Gimbiya ne. Ni Jamila da Suwaiba ne daman na sa ka ran in ma za su fito ranar kenan. Da bakin shi ya ke faɗa mini Gimbiya kayan snaks ta yi mishi har da ƙananun kofunan mug da sunan kamfani, ni kuma lokacin ba ni da kuɗi. Duk na ci ubansu da sunan Yumna hijaban ma tun da na haihu sau ɗaya aka kawo mini. Ba domin Gimbiya ta yi ba a'a sai domin nima matarsa ce kuma ya kamata nima na nuna nawa bajintar. Da na yi tunanin memo amma sai Adnan ya faɗa mini su Anty Bahijja sun yi masa Memo, sai na ce tun da har an yi memo da mug ni bari na yi jaka wacce za a saka gift ɗin a ciki ba ni da kuɗi amma haka na yi ƙarma ƙarma sai da Ya Auwal ya cika mini wajen 30k sannan na ba da a ka yi masa guda hamsin ta hannun Adnan.

Jakar ta kwali ce an saka sunan kamfanin ne.
Congratulaton Md Yusuf Muhammad Inuwa on your opening ceremoney of your company. Hm Tafida and son's Limited.
Cut ceey. "Miss Sadiya Yusuf Muhammad, Hauwa'u Yusuf Muhammad, Maimunatu Yusuf Muhammad and Rukyyatu Yusuf Muhammad.
Bai sani ba, kuma na ce kar Adnan ya faɗa masa sai ranar kawai sai dai ya gani. Bangaren abincin sadaka ni ya bar ma ragama buhun shinkafa za a dafa da wake, sai na raba biyu rabi na ba ma Maman Saude aikin rabin kuma sai na ba ma Maman Naana mai yi mana kitso. Na ce in sun yi su raba shi ga almajirai sadaka ce. Bangaren kayan da zai saka kuma ranar ya zo ya na cw mini da ya saka suit ko manyan kaya wanne ya fi? Ni kuma na ce ya saka manyan kaya zai fi ƙwarjini. Sai ya ce shima haka ya ce amma Gimbiya ta ce suit zai saka har ta siya masa ma ni kuma jin haka ya sa na ce duk wanda ya yi masa ya saka zai yi kyau tun da da man shi ɗin mai kyau ne. Sai ya ce kawai shi dai zai saka manyan kaya. Ya nuna min wata dakakkiyar gezner fara da ya siya ya ba da ɗinki har da babban riga. Sannan ya siya cover shoe baki mai kyau da hula dara sai agogon fata mai tsada. Ranar dai Yallaɓai sai wanda ya gan shi kawai amma kyau ne zai yi har sai ya gaji da kyau.

Tuni status ya ɗauka yan gidan su kaf sun ɗora katin gayyatan suna ta ya shi murna. Nima na dora har Samira ta yi min magana ko mata na zuwa na ce mata e amma mata gida ne, nan take ta ce mini za ta yi ma Hauwa magana wata ƙila su shigo fatan alheri. Su Ya Hamza  duk na tura musu sai aka ci sa'a a satin zai shigo Kano ya ba ni tabbacin zai je Ya Auwal dai a waya ya kira Yallaɓai ya yi masa murna. Amma Ya Muntari da Ya Abubakar da Datti duk sun ce za su je. Sai jin daɗi nake yi domin ni kaɗai na san dararen da Yallaɓai ya ɓata bai samu barci ba saboda zuwan wannan ranar mai ɗimɓin tarihi.

****.
.
RANAR TARO.
10 March. 2021.
Lahadi.

Ko da ba a gidana Yallaɓai ya kwana ba amma ya biyo ta gidana ya yi mini sallama ni da yara muka rumgume shi domin ta ya shi murna a wannan rana mai matukar muhimmamci a gare shi.
Kun ga Yallaɓai? Cancaɗi ni kaina sai da na saki baki da hanci ina kallon shi. Domin ya dawo min wani ɗan saurayi ɗan shekara talatin. Da man ya na son fararen kaya ko don ya san suna yi masa kyau ne oho? Har da wani farin gilashi su Yallaɓai manya an fito sharr. Tare da Kawu Abba shima ya sha Babban riga. Ya kuma kyauta domin da Marwa ya taho mini duk da tana ta fama da laulayin ciki. Tariq na hanya bai riga ya iso ba. Hadda su Khalipa su kan yan kanti suka saka da su za a je ni kam ni da ƴa'ƴana ko ba mu je ba mun cakare a gida har ko da Yumna na mata gayu kuma itama sai da Yallaɓai ya ɗauke ta na ce murna ta ke taya shi tun da tana jin muryansa ta fara harba ƙafafu.
Chapter 42 · 0% Book details